← Book details Abokin Aikina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 68

Sashe 23

Abokin Aikina Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Nufo ni ya yi gadan-gadan yana ƙoƙarin haɗa jikin shi da nawa, cikin zafin nama na tura shi ya yi baya. Sannan na nuna shi da hannu cikin ƙololuwar ɓacin ran da ya ziyarce ni.
"Kada ka yi gangancin zo mini da wani sabon sanabe, don sanin kanka ne babu wata alaƙa da ta yi saura tsakanina da kai yanzu. Sawunka a likkafa ka fice mini daga ɗaki tun muna shaida juna, idan kuma ka fi so ka tunzura ni na yi maka aika-aika to ka sake zuwa kusa da ni."
Kallo na ya tsaya yi na ɗan lokaci, kafin ya sake nufo ni yana dariya kamar bai ji kashedin da na yi masa ba. Janyo ni ya yi da ƙarfi na zille, nan take muka fara kokawa ni da shi, cike da ƙarfin zuciya nake ta hana shi abin da yake ƙoƙarin aikata mini.
Ganin da gaske ba zai samu haɗin kaina ba, ya dawo magana cikin haki yana faɗin, "Wallahi duk abin da ya biyo baya kada ki ga laifina. Ba dai kin hana ni haƙƙina ba? To ke kuma ki jira me zai faru cikin kwanan..."
"Kai har kana da bakin faɗar wani haƙƙinka da ke kaina yanzu? Kenan ka manta tsawon lokacin da ka ɗauka ba tare da ka neme ni ba? Ko an faɗa maka kai kaɗai ne mai haƙƙi ni ko oho? To ka je ka ɗauki matakin kada ka yi sanya, idan kuma ka fasa wallahi ban gode maka ba. Mitsssss! Aikin banza tura agwagwa cikin ruwa."
Na ƙare maganar a fusace saboda furutan shi sun sa na ji ya kai ni bango Ya jingine.
"Za ki gani!"
Zancen da ya yi kenan ya ja rigar shi ya fice fuu tare da bugo ƙofar ɗakin da ƙarfi. Ƙofar na bi da harara tamkar idona zai faɗo ƙasa, sannan na je na saka makulli na rufe na dawo na zauna ina haki. Mamaki na shiga yi a kan rashin adalci irin na Mukhtar, saboda rabon da ya nemi ni a matsayin matar shi ta sunnah sama da shekara uku. Kuma duk na yi haƙuri na jure amma sai yanzu zai zo mini da guntun rainin hankali.
Wanda na sani idan da zan kai shi kotun musulunci take yanke za a raba aurena da shi, saboda iya cutarwar duniya ya yi mini kuma ya tauye ni da baƙar igiyar da yake tinƙaho da ita.
Daren ranar ma sai da na gamsar da kaina sannan na samu damar yin bacci cikin nishaɗi, saboda ya tayar mini da tsohuwar jarabar da kullum nake ƙoƙarin kawar da kaina kanta, tare da addu'ar samun sauƙinta a wurin Allah.

Da safe ma tun da ya fita bai dawo gidan ba, sai dare bayan mun shige bacci sannan na ji yana rufe gida, ban wani damu ba don daman can bai ɗaɗa ni a ƙasa ba. Haka ma ranar Lahadi bai zauna ba, don ko yaran bai bi ta kansu ba a lokacin. Saboda ba wannan ne karon farko da fara yi musu hakan ba, domin ya sha shafa musu laifina a duk lokacin da na samu saɓani da shi, don a baya ma ko abu ya siyo ba zai bai wa kowa ba ko da yaran sun gani. Haka zai cinye abin shi muna kallo ba tare da ya ba mu ba, tun yaran suna jin haushin abin har suka daina zuwa kusa da shi idan sun gan shi da leda. Saboda a can baya ma idan ta yi masa daɗi, miƙa wa ɗiyan 'yan'uwan shi yake yi Ummu Salma tana kallo ya hana ta. A tunanin shi ni yake yi wa baƙinciki don na ji haushi.

Ranar Litinin tun da sassafe na tashi, na haÉ—a wa yarana abin kari sannan muka shirya tare da su muka fice. Ganin É—akin shi a rufe ya sa na gano ya yi wurin aiki don ban san fitar shi ba.
Bayan na ajiye su makarantarsu, na ba su kuÉ—in tara da waÉ—anda za su hau abin hawa idan aka tashi. Sannan mai adaidaitan ya ajiye ni wurin aiki bayan na nemi alfarmarsa, a kan idan lokacin tashi ya yi daga makaranta ya koma ya É—auko mini su Ummu Salm.
Saboda akwai sanayya tsakanina da shi kuma sosai yake girmama mutuncina a zahiri. Ina tafe zuciyata cike da tunanin riƙon shi a matsayin wanda zai dinga kai su Ummu Salma makaranta, kuma ya ɗauko su a duk lokacin da aka tashi. Da zummar idan an yi mana albashi na dinga biyan shi kuɗin shi gabaɗaya.
Zancen zucin da nake yi ya katse a daidai lokacin da mutanen wurin suke ta yi mini ya ƙarfin jikin ina amsawa. Turus na yi saboda babu makullin ofishin a hannuna, domin a ranar Alhamis da na bar wurin tashin hankali bai sa na tsaya rufe offishin ba. Ficewa kawai na yi saboda kwata-kwata na manta kowa da komai, face neman hanyar da zille wa auren Mukhtar a idona.
Ofishin MD na nufa raina yana suya, saboda ba na farinciki da ganin shi saboda haushin shi da nake ji. Na yi wa kaina katanga da shi kuma na kwance ƙaƙƙarfar alaƙar son da na fara ginawa a tsakanina da shi. Kaina a ƙasa ina shan ƙamshi na ƙwanƙwasa masa ƙofa,
"Yes! Come in"
Ita ce maganar da na ji ya faɗa na tura ƙofar kaina a tsaye na isa gaban shi. Ban damu da gaishe shi ba cikin haɗe fuska na ce,
"Key za a ba ni."
Ya miƙo mini yana ta rubutun shi ba tare da ya kalle ni ba, cike da haushi na fice saboda ganin ko-in-kular da ya yi mini.
Zama na yi bayan na zauna, ina nazarin abubuwa da yawa a cikin kwanyata. Sannan na fara duba files ɗin da na gani a saman teburina, na shiga aiki tuƙuru ba tare da na nemi ba'asin komai kansu ba. Saboda ina da masaniyar komai nasu, bayan lissafin da na shiga bugawa da calculator, ina ta rubuta adadin da na samu a wuraren da ya dace a jikin files ɗin.
Turo ƙofar ofishin da sallamar Amina bai sa na ɗago daga aikin da nake yi ba, na dai amsa mata sallamar saboda ba na so ta katse mini aikin har sai na gama.
Tsawon minti goma tana zaune har na kammala aikin na ture files É—in gefena. Tagumi na yi da hannuna biyu muna kallon juna muna murmushi, sannan na cire farin gilashin da nake sanye da shi ina faÉ—in,
"Sannu cika-aiki. Wannan sammako haka ba kya bari a kira ki?"
"Gara dai na zo don zuwa da kai ya fi aike."

Dariya muka saka a tare sannan na jingina bayana jikin kujera ina É—an juyawa a hankali. Murmushi É—auke a kan fuskata na ce da ita, "A ina muka tsaya da labarin? Don na san kin fi ni sanin inda za mu tashi."
Zama ta gyara sannan ta ce, "Abu mai sauƙi cire wando ta kai, mun tsaya ne a daidai inda cikinki ya kai wata tara haihuwa yau ko gobe. A lokacin da Abban su Ummu ya yi miki laifin da ya so katse igiyoyin aurenku."
"Madallah da ke, don ni haddar kaina ta daÉ—e da gogewa."
Shiru na yi ina nazarin abubuwan da suka faru a lokacin, sannan na yi murmushin da iyakacin shi leɓe tare da sauke ajiyar zuciya na ɗora daga inda na tsaya.

_EDD na yana cika na ce da shi ya bari na koma wurin Ummata, saboda koyaushe zan iya haihuwa amma ya nuna ba zan je ba har sai na haifu. Domin ita kanta Ummar ta so a mayar da ni wurinta na haifu gabanta, amma babu kunya ya nuna ya fi so sai na haifu gidansa. Ba ta ja da tsauri ba ta bar maganar saboda ya fito ƙarara ya nuna ba ya so._
_Duk da girmama al'ada irin ta Sakkwatawa haka ta haƙura, domin abu ne wanda kowa ya sani haihuwar farko a gida yarinya take yi. Wani lokaci ma da wuri ake komawa a yi ta dakon zuwan haihuwar._
Chapter 23 · 0% Book details