← Book details Abokin Aikina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 68

Sashe 18

Abokin Aikina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Me da me ne a cikin jakar?"
"Credentials É—ina ne da wasu 'yan kayana, sai wayata da ATM tare da sauran wasu tarkace."
Na ba shi amsa jikina yana rawa, kai-tsaye ya nufi hanyar fita É—akin tare da faÉ—in,
"Jira ni yanzu zan dawo."
Zumbur na miƙe tare da rawar jiki da ta murya ina haɗiyar yawun tsoro masu wucewa muƙut a wahalce. Kuka na dawo yi masa ina faɗin, "Don Allah ka bar kayan nan kada ka koma ba sai an ɗauko ba, idan ma za ka je mu je tare dukanmu daga can ka ajiye ni wani wuri na jira asuba."
"Babu inda zan je da ke! Ki jira ni a nan yanzu zan dawo."
Yana ƙare faɗar hakan ya fice tare da rufe ni ta baya, dole na durƙushe jikin ƙofar ina wani irin kuka mai kama da na mutuwa. Saboda abubuwa sun cakuɗe mini a kwanya na rasa me zan kama na ji sanyi.

Na daÉ—e a cikin halin kafin na fara jiyo sautin kukan yaro wanda ya sa hantata kaÉ—awa, domin hakan ya tabbatar mini da dole ne matar shi ta farka duk nauyin baccin da take yi. Kuma faruwar hakan tamkar fallasa asirin rufin É—akin da aka yi da ni ne, wanda alamu ya nuna mini kafin ya dawo ta yi watanda da naman a cikin gidan.

Safa da marwa na fara yi da a tsakiyar falon, hannuna a ka ina tsiyayar ruwan hawaye mara sauti. Kukan yaron na ji ya yi yawa, da muryar shi gwanin tausayi. Na nufi ƙofar ɗakin na kara kaina jikin ƙofar domin na ji ko akwai wani motsi bayan na shi.
Amma har ya ci kukan ya bari don kan shi ban ji muryar kowa ba balle wani motsi. Ƙarfe biyu da rabi na dare da mininti shidda, na ji alamun takun tafiya yana kusanto ɗakin da nake, gabana ya ƙire ya faɗi dum-dum! A lokacin da na ji ana murɗa ƙofar ɗakin da nake ciki.

Shin wane ne? MD ne ko matar shi?😹

D. AUTA CE✍🏼

*ABOKIN AIKINA*

*@HADIZA D. AUTA*

*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*

*LAMBA SHA BIYAR.*

Ƙoƙarin buɗe ɗakin da na ji ana yi, hakan ya ƙara ƙarfin dakan luguden uku-uku da zuciyata ke yi. A ɗari na bazama da gudu na faɗa wata ƙofar da na gani, babu jinkiri na saka key tare da shan jinin jikina na lafe a jikin bango. Addu'a na dinga yi a zuciyata bayan na toshe bakina da nake gudun ya tona mini asiri.
Takun tafiya na ji ana nufo bakin ƙofar toilet ɗin da na ɓuya, hankalina bai ƙara tashi ba har sai da na ji an sake taɓa handle ɗin ƙofar an murɗa. Babu shiri na darje daga tsayen da nake, saboda sulɓin tyles ɗin da ya ja ni zuwa ƙasa na yi zaman 'yan bori.
Ƙuguna na dafe ina yarfa hannu saboda sosai na ji zafin faɗuwar. Shiru ban san sake jin motsin komai ba bayan takun tafiyar da na ji kamar an bar bakin ƙofar. Mintuna a tsakani na fara jin kukan yaron a cikin ɗakin.

"Shiii!" Na ji ana faɗa wa yaron da muryar da nake da tabbacin ta MD ce, amma fargaba da tashin hankalin da nake ciki ya sa na ƙaryata hakan a zuciyata. Saboda ina gudun na fito ya zamana matar shi ce take kama da muryar shi, ko kuma a ce suna tare tsautsayi ya sa ta gan ni na janyo masa rigima daga taimako.

Tsawon minti goma ina zaune inda nake ban motsa ba, har zuwa lokacin da na ji an fara ƙwanƙwasa ƙofar toilet ɗin. Sannan na tsinkayo muryar shi yana faɗin,
"Wannan shirun na lafiya ne kike yi a cikin toilet kuwa?"
Dafa ƙirjina na yi sannan na sauke ajiyar zuciya tare da haɗiyar yawun da suka tsaya mini a maƙoshi. A daddafe na dafa bangon na miƙe ina jan ƙafafuwana da suka yi mini nauyi. Na buɗe ƙofar cikin sauri na kawar da kaina gefe, saboda kallon da yake aiko mini fuskar shi a haɗe mai kama da tuhuma.
Wucewa ya yi na biyo bayan shi caraf idanuwana suka sauka a kan jakar kayana, cikin sauri na nufi jakar ina faÉ—in, "Yanzu sai da ka je É—auko..."
Kuka ya suɓuce mini wanda ya hana ni ƙarasa maganar da na yi niyya. Shiru na minti biyu sannan ya yi gyaran murya ya ce da ni,
"Wannan jakar kaɗai na gani, amma ban ga ƙaramar ba. Ko a can gidan da kika shiga kika jefar da ƙaramar jajar ba ki sani ba?"

"I, a can na zubar da ita, don ko da na shiga gidan tana maƙale a kafaɗata."
"Za ki iya gane gidan idan mun je unguwar?"

"Zan gane"
"Ok! Tom da safe za mu koma ki karɓo jakar."

"Ba sai mun koma ba na yafe musu." Na yi hanzarin faÉ—in maganar don ba na son su yi masa rashin mutunci, domin na fahimci tsagerun mutane ne. Kuma 'yan iska ne ajin farko.
"Za mu koma! Idan ma sun kawo mana rashin kunya sai na haÉ—a su da jami'an tsaro."

Shiru kawai na yi masa don a ɗan zaman da na yi da shi, na gano mutum ne mai magana ɗaya. Kuma duk abin da ya furta ta tabbata babu sauyi ko da bai yi wa mutum daɗi ba. Jikin jakata na rakuɓe tare da yin tagumi har zuwa lokacin da yaron ya sake motsawa yana kuka.
Wanda ban lura da shi a kan gado ba har sai da kukan shi ya shiga dodon kunnena. Na yi hanzarin miƙewa na riga MD ɗaukar shi, jijjiga shi na fara yi tare da bubbuga bayan shi har ya sake komawa bacci.
MD ya ce na kawo shi ya kai wa mai aikinsu na ce ya bar shi wurina, daga haka ya fice ɗakin bai musa ba. Na lallaɓa na ajiye shi a kan gadon, sannan na zauna ƙasa na ɗora kaina saman katifar gadon. Hannuna riƙe da hannun yaron na shiga nazarin tafiyar da zan yi idan safiya ta waye. A gefe ɗaya kuma zuciyata cike take da fargabar abin da zai faru, idan matar MD ta yi ido biyu da ni a cikin gidanta.
Ban san lokacin da bacci ya yi awon gaba da ni ba, sai bayan na farka idona ya kai kan agogon da ke manne cikin ɗakin. Wanda nake tantama a kan gaske ne abin da na gani ko kuma daman can ba ya aiki. Domin kuwa ƙarfe bakwai saura na gani. Abin da ya ƙara ba ni mamaki kuma; yaron da nake riƙe da hannun shi ba ya kan gadon, wanda alamu ya nuna an ɗauke shi ba tare da na san an shigo ɗakin ba.
Zumbur na miƙe na faɗa toilet na yi wanka agurguje saboda fitsarin da ke jikina har lokacin. Na yi arwala na fito na ƙargame ɗakin da makulli, sannan na yi sallah a gaggauce cike da tsoron kada ina sallah na ji saukar duka.
Na shirya cikin doguwar rigar shaddar da ke cikin kayana, sannan na saka mayafi mahaɗin shaddar ba tare da na shafa ko da mai ba. Jakata na ɗauka na fito daga ɗakin babu shiri na ja baya na rakuɓe, saboda ganin wata dattijuwar mata ta nufo ni da tire a hannunta, wanda nake da tabbacin abinci ne za ta kawo mini.
Kallon mamaki na bi ta da shi har ta shige ɗakin, saboda ganin ta gaishe ni cikin mutunci da sakin fuska tamkar ta san ni. Yaƙe kawai na yi mata a lokacin da ta ce da ni,
"Hajiya ki koma ki karya kafin ki tafi. Yar laɓai ya ce idan kin gama ki same shi waje."
Bayan ta wuce na ja jakata ba tare da na bi ta kan abincin ba. Sauka na yi ƙasa da sauri har da sassarfa cike da burin na fita gidan ko da hankalina zai kwanta, domin na huta da fargaban da nake ciki.

Cikin motar na same shi yana sauraron ƙira'ar sudes daga cikin ayoyin ƙarshe na suratul Rahman. Ban jira ya ba ni umurni ba na buɗe motar na shige ina zarar ido rungume da jakar kayana. Kai-tsaye ya fice gidan ba tare da ya ce da ni komai ba ya cilla motar a kan titi. Sai da muka yi doguwar tafiya muna gaf da shiga unguwar da na baro jakar, sannan ya ce da ni,
"Idan mun kai gidan ki sanar da ni."
Daga haka ya ja bakin shi ya tsuke ni ma ban ce komai ba sai kai da na ɗaga alamu 'To'. Tun daga nesa na nuna masa gidan ya ci birki a daidai ƙofar gidan, sannan dukanmu muka fito ya ce na jira shi a nan. Cikin gidan ya ɗan tura kai tare da ɗaga murya ya fara rafka musu sallama, sannan na ga ya dawo ya jingina bayan shi jikin motar shi yana dannar waya.
"Ku ƙaraso za ku hango motata."

Maganar da na ji ya faɗa kenan a cikin wayar sannan ya mayar da ita aljihu, a daidai lokacin da wani ya fito daga cikin gidan yana ƙare mana kallon sama da ƙasa.
Yana ƙoƙarin yin magana muka jiyo jiniyar motar 'yansanda, a ruɗe na kai kallona ga fuskar MD, cike da mamakin abin da ya sa shi kiran su tun kafin a yi musu zancen jakar.
Ko da na dawo da kallona a kan ƙofar gidan wayam na gani babu mutumin da ya fito gidan balle alamun shi. Yansandan suka ƙaraso wurin suka bai wa juna hannu da MD suk gaisa, sannan wani daga cikinsu ya ce da shi,
"Ya kuka yi da su?"
Chapter 18 · 0% Book details