← Book details Abokin Aikina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 68

Sashe 15

Abokin Aikina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Cikina yana wata huÉ—u ya yi bulaguro zuwa Abuja, ya bar ni daga ni sai cikina sai Mahaifiyar shi da dangin shi. WaÉ—anda suke faÉ—i-tashi a kaina domin su É—ebe mini kewar shi, kuma su faranta mini. Takanas Yayar shi ta kawo mini babbar 'yarta domin ta taya ni zama har ya dawo. Duk da wani lokaci a cikin gidansu nake wuni sai dare ya yi na dawo gidan na kwanta._
_Sai da ya shafe sati biyu har da kwanaki sannan ya dawo. Duk da ina jin haushin daɗewar da ya yi, saboda babu wani uzurin dolen da ya kai shi, amma hakan bai hana ni nuna masa farincikin dawowar shi ba. A daren ranar ya kashe ƙwalamar shi a kaina, amma ni ya janyo mini amaye-amaye a tsakiyar daren zuwa safiya. Saboda turaren jikin shi kwata-kwata bai yi mini daɗi ba, haka ma warin tabar da na ji bakin shi yana yi ya saka ni aman dole. Sai dai tun da ya yi mini sannu sau ɗaya ya juya kwanciyar shi yana ta minshari, jiki na ja na yi falo. A kan kujera na kwana a ranar ina ta tofar da yawu saboda tashin zuciyar da nake ji a duk lokacin da na tuna da warin tabar._
_A rayuwata na tsani taba, domin ko warinta na ji sai kaina ya juya. Dalilin hakan duk mutumin da na gani yana shan taba har raina nake jin ƙyamar shi, kuma ba na zuwa kusa da shi balle warin ya dame ni. Kwana na yi ina juyi da tunanin ina Mukhtar ya haɗu da taba har ya sha, saboda tun da nake da shi ban taɓa sanin yana shan taba ba balle na gani. Hakan ya sa na shiga kokwanto a kan ita ce ko dai ni ce kawai na ji kamar ita._
_A lokacin mun cinye abincin gara har mun fara aune, dalilin haka na fara shiga wata sabuwar matsala. Duba da yadda na saba dafa abinci wadatacce na kai gidansu, bayan wanda 'yan'uwan shi suke shigowa su ci ko kuma su tafi da shi. Ga shi idan ma na dafa ni ba na iya cin nawa sai na gidansu idan an ba ni. Haka zan dafa iya konon da ya kawo, idan na cire masa na shi sai na juye musu saura a kula na kai musu. Hakan ya janyo suka fara haure mini kai, tunanin su ni ce kawai na tsiro da abin don ba na son ba su._
_Saboda ba su san daga shi ne ba, idan ya shigo da konon shinkafar ya ga da mutane a gidan sai ya je Kitchen ko wani wuri ya ɓoye ta. Sai dai ya kira ni gefe ya sanar da ni ga inda ya ajiye idan na tashi dafawa._
_Sannu a hankali suka canza mini gabaɗaya, abincin da nake kai musu ma suka daina karɓa, ni ma wanda suke ba ni suka daina aiko mini. Na shiga damuwa da neman dalilin sauyin su, na samu amsar a bakin 'yar Yayar shi wadda ta yi taya ni bacci. A lokacin da ta ga na shiga damuwa, a kan na ba ta abincin ta kai musu suka dawo mini da kayana._

"Wallahi Aunty dama kin daina ba su, don na ji suna faɗar tun da ba ki yi niyyar ba su ba gara su hutar da ke. Domin wai a lokacin da kike son ba su sai kin cika kula ki kai musu, kuma duk wanda ya shigo kina ba shi saɓanin yanzu da kika daina."

"Ikon Allah!"

_Ita ce kalmar da ta fito bakina ban shirya ba, saboda mamakin zancen da kuma rashin adalcin da suke ƙoƙarin yi mini. Sai da na sauke ajiyar zuciya sannan na ce,_
"To wallahi Sajida ba daga ni ba ne. Shi yake siyo shinkafar kaɗan shi ya sa nake ba su kaɗan. Amma da a ce zai siyo wadatacciya zan ba su kamar yadda na saba, wataƙila ma a fi haka musamman yanzu da ba komai nake iya ci ba." Na ƙare maganar cikin damuwar da ta bayyana kan fuskata.

"Ki ƙyale su Aunty kowa ya yi nagari don kan shi."

_Amsar da ta ba ni kenan a ƙoƙarin ta na kwantar mini da hankali, kuma sosai ta shiga jikina. Saboda zallar gaskiyar da ke ciki tare da jin daɗin fahimtar da ta yi mini._
_Da ya dawo ban ɓoye masa komai ba na sanar da shi, saboda ya yi wa abin tufƙar hanci ta hanyar sauya awon da yake yi domin a samu zaman lafiya. Amma fitittike wa ya yi ya shafa wa idonsa kwalli, a kan cewa; konon shinkafar shi ne daidai ƙarfin shi. Na yi ta so na nuna masa illar ƙaramin awon da matsalolin da zai haifar mana a nan gaba, amma ya nuna mini ya fi ni sanin komai da tsarin rayuwa. Dole na ƙyale shi a yadda yake so don ba ni da ikon saka shi dole, musamman da na ga ya fi ni son dangin shi amma bai ji kunyar yin abin da yake so ba._

_Haka muka ci gaba da tafiya babu jituwa tsakanina da mahaifiyar shi da ƙannen shi, har zuwa lokacin da cikina ya yi wata tara haihuwa yau ko gobe. Wanda a lokacin ya karta mini wani gagarumin laifin da ya so katse igiyoyin au..._

Zuuuu! Shi ne sautin virbration kiran da ke fitowa a cikin wayata saboda tana silent. Wanda ya dawo da mu daga duniyar waiwayen bayan da muka lula daga ni har Amina, wadda ta yi luf tana sauraro na ko motsin kirki ta kasa yi.
Da hanzari na ɗauki wayar saboda ganin sunan Baba Ali ɓaro-ɓaro a jikin fuskar wayar. Gaishe shi na fara yi cikin mutuwar jiki da sanyin murya, bayan fargaban da nake ciki a kan kiran na shi. Wanda ya haifar mini da bugun zuciya da sauri da sauri, kafin na fara jin maƙasudin kiran cikin faɗa da ɗaga murya.

"Mijinki ya kawo ƙarar ki wurina, a kan abubuwan da kike yi a wurin aiki. Waɗanda bai kamata gare ki ba, a matsayinki na matar au..."
"Wallahi Baba ƙazafin da ya saba ne kawai babu gaskiya a ciki. Burin shi kawai na daina aikin nan bayan kuma shi ma yana rufa masa asi..."
Amsar da na ba shi kenan cikin muryar kuka saboda tsabar jin haushin abin da Mukhtar yake yi mini. Shi ma ya tare hanzarina yana faÉ—in,
"Ko ma dai mene ne ki ji tsoron Allah a matsayinki na matar aure. Don kin san hukuncin matar da ke cin amanar aure, don haka ki kiyaye. Allah ya ƙara miki haƙurin zama da shi tun da Habi ta zaɓar miki zaman. A tunaninta irin wannan zaman ya fi alheri da zaman ki bazawara."

Hawaye na goge a kan fuskata sannan na ce, "Don Allah Baba ka yi haƙuri. Wallahi ba na ƙaunar Mukhtar a rayuwata kuma na tsane shi."
"Ki yi haƙuri Allah yana tare da ke."
Daga wannan maganar da ya katse kiran, sauke wayar na yi daga kunnena ina zuƙar majinar kuka. Kayana kawai na haɗa a jaka na miƙe na fice daga offis ɗin, ba tare da na yi wa Amina sallama ba saboda ƙunar da zuciyata ke yi.

Hmmmm! ABOKIN AIKINA fa rikici ne daddale a cikin shi yasin😅

D. AUTA CE✍🏼

*ABOKIN AIKINA*

*@HADIZA D. AUTA*

*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*

_*Littafina free ne ban yarda a sayar da shi ba, ko a juya shi ta wani ɓangare ba tare da izina na ba😒*_

*LAMBA SHA UKU.*

Karaf na ci karo da mutum ba tare da na tantance wane ne ba. Amma duk da hakan ban jira komai ba na yi gaba, balle na bai wa wanda muka yi karon da shi haƙuri.
Idona a rufe na fice ma'aikatar tamkar na kifa. Jefa ƙafafuwana kawai nake yi, a dalilin duhun baƙincikin da ya yi mini rumfar da ta lulluɓe mini zuciya.
Ban yi tsayuwar jiran adaidaita ba na ci gaba da jefa ƙafafuwa cikin sauri, har na yi katarin ganin wata za ta wuce babu kowa a ciki na tare. Luf na yi bayan na zauna ina sauraron waƙar da ke tashi a cikin daidaitar. Wadda nake jin ta har tsakiyar zuciyata, domin ta ƙara rura wutar tsanar Mukhtar a cikin zuciyata. Saboda duk wani baiti da ke fita a cikin waƙar, ina alaƙanta shi da ni kuma ina ji a raina tamkar ni ce nake furzo su daga bakina zuwa kunnen Mukhtar.

'Ka rusa soyayyar da zuciya ke ma.'
'Na daina ƙaunar ka zan iya rantse ma.'
'Ba wata alfarmar da za na iya yai ma.'
'Ka naÉ—e tabarmar kunya ka je Allah ya yafe ma.'

'Maƙaryaci babu ni babu shi.'
'Tuntuni mun raba hanya da shi.'
'Ko da tsautsayi ya gifta.' 'Ni ba ni so nai gamo da shi.'
Waɗannan baitukan ba ƙaramin tasiri suka yi wa zuciyata ba, domin sun ƙara tunzura ni na kai maƙura a kan abin da na kitsa wa zuciyata.
Wanda na gama amanna da cewa shi ne abin da zai kawo ƙarshen zaman yaƙin da nake yi da Mukhtar. Har aka kai ni ƙofar gidan mai adaidaitan bai canza waƙar ZO MU SASANTA ba tamkar da gayya.

Jikina yana rawa na biya shi kuɗin shi na nufi ƙofar gidan, ganin shi a buɗe ya tabbatar mini da su Ummu Salma suna nan. Afujajan na faɗa falon da ƙudurin na aiwatar da nufina, sai ga shi na yi turus babu shiri saboda Ummata na gani zaune a falon cikin yarana.
Har a raina ban ji daɗin ganin ta ba, ƙarin takaicin kuma ƙofar ɗakin Mukhtar a rufe alamun bai dawo daga aiki ba. Gani na ya sa su Ummu Salma suka yo kaina suna ihun murna tare da faɗin,
"Oyoyo Mama!"
Fuskata a haÉ—e na isa tsakiyar falon na zauna babu yabo babu fallasa na gayar da ita.
Ba ta amsa mini ba, sai kallon da na ga tana yi mini ta gefen idona, Domin na kasa haɗa ido da ita. Don ba na so ta katse mini hanzari dangane da abin da na kitsa wa zuciyata, ko da tsiya-tsiys ko ta halin ƙaƙa.
Chapter 15 · 0% Book details