← Book details Abokin Aikina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 68

Sashe 57

Abokin Aikina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zancen Inna Kulu kenan a lokacin da muke ƙoƙarin shigewa gida,
"Ai duk mutumin da kika gani tare da Mukhtar, ba mutumin arziƙi ba ne. Shi ya sa idonsa ba su yi mini girma ba, balle na fasa sauke musu duk abin da ya fito bakina. Ai dai duniya ce, su yi duk abin da suke so Allah yana jiran su a madakata, domin su karɓi sakamakon abin da duk suka shuka."

Ummu ta ƙare maganar tare da cire hijabinta ta ja buta zuwa bayi. Na ja kujera 'yar tsugunno na zauna, sannan na sauke ajiyar zuciya na ce,
"Ni na rasa da me zan fassara wannan lamari. Duk da idan ɓera da sata daddawa ma da warinta. Maman Taufiƙ tana da zafin kishi sosai har na fitar hankali. Shi kuma mijinta yana da idon kallon mata ya ji sun burge shi. Idan ya yi laifi a kan ɓoye matan da ya yi, to laifinsa kaɗan ne nata ya fi yawa. Saboda ya fi kowa sanin zafin kishinta, yana gudun ya faɗa mata hakan ya janyo masa tashin hankali. Amma kuma da ya faɗa mata gaskiya sai ta fi jin sauƙin abin, da a ce ta ji labari kwatsam! Bayan aikin gama ya gama."

"Maza! Maza!"

Zancen Inna Kulu kenan tare da jinjina kai, kafin maganar Kawu Sale ta shigo dodon kunnuwanmu tun kafin mu gan shi.

"Me mazan suka yi?"

Murmushi na yi mai sauti ban ce komai ba, Inna Kulu ce ta yi ƙarfin halin faɗin,
"Tsohuwar bazawararka aka ce yaushe za ta kawo sadaki a É—aura muku aure?"
"Ki rantse da Allah gaske kike yin maganar nan, ni kuma cikin satin nan a É—aura na dinga zuwa gidanta dangana sanda."
"Idan da rabon sandar ta jingine ka gidan da ƙarar kwana ai sai ka je ga fili ga mai doki."

Zancen Inna Kulu kenan da Kawu Sale, tsam na miƙe ina dariya na yi ɗakin Umma. Kwance na yi, bayan na mayar da ruwa da kunun ayar da Maman Taufiƙ ta ƙi sha a furji. Ina ta juya abubuwan da suka faru a kwanyata bi-da-bi, har tunanin Sajida ya faɗo mini a rai zumbur na miƙe na fito waje. Inna Kulu na iske ɗakinta ina faɗin,

"Wai Inna ya aka yi da kuka kai Sajida gidansu?"

Inna Kulu fuskata babu yabo babu fallasa ta ce da ni,
"Lafiya lau na fito gidan, duk da Uwarta ta yi ta jifa ta da maganganu marasa daÉ—i. Bayan na ce ga 'yarta nan mun kawo mata kada ta tsine mata. Tun kafin na gama fitowa na ji tana faÉ—in, yau gidan mijinta za ta kwana ta gama kwana gidan har abada."

"Allah Sarki Sajida!"

Haka kawai na tsinci hawaye suna kwaranya a kan fuskata, saboda duk abin da aka yi mata sanadina ne. Domin a huce haushi na da ake ji a kanta, saboda ta nuna tana ƙaunata a fili fiye da kawunta.

"Akwai Allah! Kuma in Sha Allah sai abin ya zame mata alheri."

Zancen Umma kenan, wadda ke riƙe da labulen ƙofar ɗakin Inna Kulu. Kafin ta ɗora da faɗin, "Ke kuma Kulu idan ba ki daina zancen Bazawarar Sale ba, sai 'yan Amin su amsa ya tare can tun da ba za ki bar shi ya huta da magana ɗaya ba."

"Ai da yana iyawa da ya yi tun lokacin da take rawar ƙafa kansa. Idan kuma kun isa a yi auren cikin satin nan kamar yadda ya ce."
"To ba mu so, kuma Allah ya raba mu. Ke ma da kike zancen saboda kishi Allah ya ba ki ikon dainawa. Mace saboda jin daÉ—in aure da tsufanki ma sai kin yi kishin Salenmu! Amma duk kika motsa sai kin cika baki kamar gaske."

"Kyale ta Habi! So take yi na ɓanɓaro sabuwar budurwa ɗanya shataf!"

Zancen Kawu Sale ya sa na yi murmushi ban shirya ba, haka suka dinga wasar su kamar yadda suka saba na baro É—akin. Zuciyata cike da tunanin. 'Kenan dai mace komai tsufanta idan ta ji daÉ—in aure tana kishin mijinta. Balle masu rangwamen shekaru waÉ—anda suke tsaka da cin ganiyar lokacinsu.'

****

Daren ranar bacci rabi da rabi na yi, saboda na yi ta kiran wayar Sajida domin na ji halin da take ciki. Amma duk kiran da na yi babu wanda na samu wayar kashe ake cewa.
Jiki babu kuzari muka shirya ni da yara kamar koyaushe, Najib ya kwashe mu ya ajiye su ni ma ya kai ni wurin aiki.
Ban yi wani aikin kirki ba ranar saboda ban da natsuwar zuciya, a ƙarshe ma tattara komai na yi na tura drowar teburina. Saboda ƙwaƙwalwata ta toshe ba na gane komai face tunanin Sajida da Maman Taufiƙ. Sai tashin hankalin da zai biyo baya ita da Amininta idan ta ji labarin yankan bayan da ya yi mata.

Misalin ƙarfe ɗaya da rabi kiran Najib ya shigo wayata, duk da ban san me zai faɗa mini ba; sai da gabana ya buga da ƙarfi kafin na ɗaga wayar numfashina yana sama da ƙasa.
"Maman Haidar, na je makaranta tun ƙarfe ɗaya ban ga su Ummu Salma ba, gabana aka watse makarantar amma ban ga sun fito ba. Har maigadin na tambaya ya ce da ni wani ya zo ya ɗauke su da mashin. Na je Bafarawa Estate a can ma an ce ba su koma gidan ba."
Dam-dam-dum! Shi ne sautin luguden da zuciyata ke yi tamkar ta fasa ƙirjina ta fito. Ban san lokacin da na zabura na miƙe tsaye ina ta maimaita faɗin, "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!" A bakina ba.

Waya a kunnena na fito da gudu na yi bakin gate, ban ma san ya katse kiran ba har sai da wani kiran ya sake shigowa.
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! Wayyo Aunty wuta! Ki zo ki cece ni wuta! La'i'laha illallah Muhammadur Rasulullah! Shi kenan!!!! ÆŠakin duka ya kama da wu..."

Muryar Sajida kenan da na ji a cikin waya, da wata sabuwar lambar da ban san ta ba, kafin kiran ya katse. A gigice, na durfafi saman titi idona a rufe ba na gane komai da kowa a lokacin, balle na hango abin da ke gabana. Odar mota na ji 'Ɗiiiiiiiiiiiiiii!' A cikin kunnuwana tamkar za a fasa mini dodon kunne. Cak! Na tsaya sai jin na yi an ture ni na faɗi gefen titin, daga ni har wayar mun ɗaiɗaya. Yunƙurin miƙewa na fara yi na ji an riƙa ni da hannu biyu na tashi, sai sannu ake jera mini ba tare da na shaida muryoyin mutanen ba sai ta mutum ɗaya waton MD.
Ruɗu da firgici ya sa na zama tamkar wata zararriya ina faɗin, "Yarana sun ɓata! Wuta ta canye Sajida! Don Allah ku taimaka mini zan mutu idan na rasa yarana da Sajida. Zan mutu idan na rasa yarana su ne rayuwata."

Hannuna na ji an ja ban tirje ba na bi, aka saka ni cikin mota sannan aka rufe. Fisgar motar aka yi da ƙarfi idona a rufe ina ta zunduma ihu, tare da kiran sunan Sajida da yarana tamkar wata mahaukaciya sabon kamu.

Hmmmmm! Laifin daɗi ƙarewa. A nan muka kawo ƙarshen ABOKIN AIKINA littafi na ɗaya. Idan Allah ya ara mana lokaci an yi sallah lafiya za mu ɗora da wani sabon salon kafcen. A cikin littafi na biyu mai tsayawa a zuciya. Ubangiji ya albarkace mu da ganin wannan wata mai tarin falala waton Ramadan.

Fatan alheri gare ku gabaɗaya luv u all😘

D. AUTA CE✍🏼

*ABOKIN AIKINA*

*@HADIZA D. AUTA*

*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*

*AM BACK MY FANS.*

*ARBA'IN DA ÆŠAYA.*

'Ƙiiiii' Shi ne kalar birkin da MD ya ja, a daidai ƙofar gidan Kawu Sale. Saboda hanzarin fisgo ni da ya yi na faɗa jikinsa a haukace babu shiri, a dalilin bai gama tsayuwa ba na nemi ɓalle murfin motar na fice.
Kallon-kallo muka dinga yi wa juna, kafin na yunƙura kamar wata zakanya, na fisge daga riƙon da ya yi mini na fice motar aguje ina ƙwala wa su Umma kira. Gidan na faɗa a sukwane tare da faɗin,

"Umma! Umma ki zo an sace su Haidar! Wayyo Zuciyata za ta buga!"

A tsakiyar gidan na zube ina gunjin kuka cikin sauti tare da É—aga murya. Inna Kulu da Umma har rige-rigen isowa wurina suke yi tare da jero mini tambayoyi. Ban bi ta kan tambayoyinsu ba, illa ihun kiran sunayen yarana da nake yi tare da Sajida a haukace.
Ruwa na ji Umma ta watsa mini a jiki da ƙarfi, na zabura ina ƙoƙarin ficewa gidan tamkar wata zautacciya. Inna Kulu ta damƙe ni Umma ta fara girgiza ni tare da faɗin,
"Ki dawo! Hankalinki! Na ce!"

Tsawar da ta yi mini sosai ta shiga jikina, cikin sauri na faɗa jikinta ina kuka na ce, "Haidar, Ummu Salma da Iman duka sun ɓace! Ita ma Sajida wuta ta ƙone..."

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Me ke shirin faruwa da mu ne haka?"

Zancen Inna Kulu kenan, kafin Umma ta ja hannuna mu fito gidan, motar MD na hango a inda na bar ta. Hakan ya sa na tuna ashe shi ne ya kawo ni gidan, har mun yi gaba ya biyo mu yana gayar da Umma. Fuskarta a haɗe ta amsa masa sannan ta ƙara jan hannuna muka yi gaba.
Biyo mu ya yi da motar yana roƙon Umma ta shigo ya kai mu inda za mu je, amma haƙuri kawai ta ba shi sannan ta tare mana wata adaidaita muka shige. Tafiya adaidaitar take yi ina sharɓar kukana mai ɗauke gunji kala-kala.

'Wuuuuuuummmmmh!! Ummmmmm!'

High Court Juduciary na ga an rubuta, a jikin bangon allon saman bakin babbar kotun da ke Sokoto.

"Kotu kuma? Me ya kawo mu kotu?"
Chapter 57 · 0% Book details