← Book details Abokin Aikina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 68

Sashe 25

Abokin Aikina Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Maganar da muka ji kenan daga ni har Amina a bakin ƙofar ofis ɗina, cike da mamaki muka bi mata biyun da ke shigowa da kallon mamaki, waɗanda ke ƙoƙarin isowa inda muke cikin gadara. Kallon sama da ƙasa ɗaya ta fara yi mana sannan ta tsayar da kallonta a kaina, nuna ni ta yi da key ɗin da ke hannunta ta ce,
"Da alamu ke ce Munafukar da nake nema!"
"Ta ya za ki neme ni bayan ni ban san ki ba!" Maganar da na faɗa mata kenan cike da jin haushin rainin hankalin da take ƙoƙarin yi mini, har cikin ofishina. Bayan dakan luguden da zuciyata ta hau yi saboda tsabar kaɗuwar da na shiga"
Kallon uku kwabo ta yi mini sannan ta miƙa hannu ta baya wadda suka zo tare ta saka mata wani wallet a hannunta, sai da ta buɗe shi sannan ta wurgo mini a fusace saman ya daki ƙirjin ya yi ƙasa. Daga shi har kayan da ke cikin shi suka yi ɗaiɗaya, na yi hanzarin kai kallona a kayan da suka zuba daga wallet ɗin, cike da mamakin yadda aka yi ta yi ta same su. Kafin na duƙa na ɗauko Amina ta riga ni haɗa kansu ta ɗago, cike da zallar mamaki a kan fuskarta ta fara jujjuya kayan cikin wallet ɗin a hannunta tana faɗin,
"Wai ku bayin Allah me ya kawo ku ofinshin nan da rana tsaka haka? Sannan ina kuka haÉ—u da Id card É—in ta, da passport har da ATM?"
"Za ki samu duka amsoshin tambayoyinki dalla-dalla, kuma zan yi miki gwari-gwari yanzu ba sai na ja zaren da tsawo ba. Amma kafin nan ke ki yi mata bayanin inda kika je kwatankwaci kika baro wallet É—inki."

"Kwartanci kuma!?"

Maganar da muka haɗa baki kenan wurin faɗa ni da Amina cikin tashin hankali, babu zato na ji 'Karaf' sauti da dirar marin matar a kan fuskata. Kafin na yi wani yunƙurin ramawa ta ci kwalata a masifance tana faɗin,
"Sai na illata ki, ta yadda gobe ko da kuɗi aka ce ki sake zuwa gidana kwartanci ba za ki iya taka ƙafarki ki je ba."
Duka ta fara kai mini Amina tana riƙe hannunta cikin zafin nama, yayin da ni kuma na shiga ƙwatar kaina ta ƙarfi duk da fargaba ya hana ni kataɓus. Ƙawarta ta fara janye Amina tana faɗin,
"Ke dalla malama matsa daga gefe ba wurinki muka zo ba. Ci ubanta Fatima gobe ko kallon MD aka ce ta yi ba za ta sake ba, balle ta kai ƙafarta gidanku a matsayin ƙatuwar kwartuwar da ba ta ramin kanta sai na wasu."
Sunan MD da na ji ƙawarta ta faɗa na ji ƙirjina ya buga dam-dam! Amma a hakan bai hana ni jarumtar ƙwace riƙon da ta yi mini. Amina ta yi hanzarin shiga tsakaninmu tana tura ta baya, ita kuma sai ƙoƙarin kai mini bugu take yi ta gefen Amina.
Cikin ƙololuwar ɓacin rai na fara nuna ta da hannu ina huci na ce,
"Zan nuna miki na fi ki tashanci matuƙar kika sake taɓa ni da sunan du..."
Kafin na rufe bakina ta shammaci Amina ta kawo mini wani sabon duka, kukan kura na yi tare da ture Amina gefe. Cikin rufewar ido da na zuciya na yi cikinta da duka iya ƙarfina. Kokawa muka fara yi ni da ita Amina tana ƙoƙarin raba mu, ƙawarta kuma tana ƙara zuga ta da ihun faɗin ta ci ubana kada ta ƙyale ni.
Ta dake ni na dake ta muke yi a tsakiyar ofishin ba tare da ta yi nasarar kayar da ni ƙasa ba. Cikin sa'a na saka mata ƙafa ta faɗi na hau kanta ina ta jibga, ƙawarta ma tana kai mini duka tare da ƙoƙarin ture ni daga saman ruwan cikinta.
Ban san ya aka yi ba na tsinkayo muryar MD yana salati, amma hakan bai hana ni ci gaba da jibgar ta ba inda ta yi mini daÉ—i. Domin ko a shekaru zan iya girmar ta kaÉ—an ko mu zo tsara, duk da ta fi ni zama duma-duma amma hakan bai sa ta yi nasara kaina ba.
Amina ta janye ni daga samanta ina huci tare da ƙoƙarin ƙwacewa na koma, da nufin sake kai mata wani dukan domin na cire rainin da ke tsakaninmu. Saboda raina ya yi ƙololuwar ɓaci a kan abin da ta yi mini, haka idona ya rufe ba na ganin komai face na yagalgala ta iya son raina.

"Yanzu miye fa'idar wannan abin da kuka aikata? Tukunna ma ke me ya kawo ki wurin nan har cikin ofishinta?"
MD ya yi magana cikin sanyin murya mai ɗauke da tsananin ɓacin rai, na ƙwace daga riƙon da Amina ta yi mini na koma kujerata ina gyara zaman mayafina, wanda ya saɓule a jikina yayin damben ba tare da na sani ba.

"Ai dole ka ga laifina yanzu, bayan ka gama kai ta har gidana a matsayin kwartuwarka kun ci amanata. Shi ne ka matsa mini a kan na je jinyar Ammi don ka ji daɗin sheƙe ayarka son ranka da ita. To Allah ya toni asirinku daga kai har ita, saboda ta bar mini shaidar da zan gane ta zo gidan, domin ta nuna mini ta fi ni matsayi a wurinka. Wallahi sai Allah ya saka mini a kan tozarcin da ka yi mini Aliyu, kuma daga kai har ita ba zan taɓa yafe muku cin amanar da kuka yi wa aurena ba."
Tana ƙare faɗar maganganun ta juya fuu za ta fice daga ofishin, kamar zautacciya ta ƙara dawowa tana nuna ni da hannu ta ce,
"Sai na nuna miki na fi ki iya karuwanci wallahi. Don sai kin raina kanki a kan wannan abin da kika aikata mini."
Tana ƙare faɗar hakan ta fice tana ci gaba da masifa cikin ɗaga murya, ƙawarta ta rufa mata baya sum-sum cikin takun munafukai. Ajiyar zuciya MD ya yi sannan cikin sanyin murya ya ce da ni,
"Ki yi haƙuri don Allah! Wani lokaci tana yin wasu abubuwa tamkar akwai wani abu saman kanta. Ban san za ta zo ba da ban bari ta fito daga gida ba wallahi, don haka duk da ban san dalilin da ya sa ta yi miki hakan ba, ina ƙara ba ki haƙuri don Allah ki yafe mata."
Kallo ma bai ishe ni ba balle na tanka masa, Amina ce kawai ta ce da shi,
"Muna zaune kawai muka ga sun shigo ita da ƙawarta suna ci mata zarafi. Mamakina ma yadda aka yi ta haɗu da wallet ɗin Zaituna, wanda kusan shi ne musabbin duk wannan jidalin."

"Ranar Alhamis ta manta shi a nan, Baba masinja ya kawo mini shi na karɓa da zummar na ajiye mata har yau na ba ta. Shi ne fa na manta shi a gida ban fito da shi ba, wataƙila dalilin da ya sa ta zargi wani abu kenan ta zo wurinta da wannan sifar. Ki ƙara ba ta haƙuri in sha Allah hakan ba za ta sake faruwa ba matuƙar da gaske ni ne mijinta."
Chapter 25 · 0% Book details