← Book details Abokin Aikina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 68

Sashe 11

Abokin Aikina Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Na amsa cike da jin daɗin kulawar da yarana suke ba ni, ledar da MD ya ba mu na buɗe cikin sauri na fito da robar takeaway ɗin da ke ciki guda biyu. Na buɗe nan take ƙamshin jallof ɗin da ke ciki ya gauraye falon, sannan na buɗe ɗayar robar sai ga peppe chicken a shaƙe ya sha jar suya.
Murmushi na shimfiɗa a kan fuskata, cike da jin daɗin wannan kyauta ta musamman. Tire na sa Ummu Salma ta miƙo na juye jallof ɗin da naman duka, sannan na ɗebo taliyar na zuba. Na ce duk su zauna mu ci tare, murna ɗauke a kan fuskokinsu muka fara cin abincin.
Muna tsaka da ci Mukhtar ya shigo ya yi mana tsaye a kai yana ƙallon mu. Ni dai ƙanzil ban ce da shi ba ina ta cin abincina, saboda ban san ina jin yunwa ba har sai da na fara kai loma. Haidar ne ya kula shi ta hanyar faɗin "Abba ka zo mu ci..."
"Rufa mini asiri kada a fasa mini kai Haidar. Wannan abincin ai na manyan ma'aikata ne ba irinmu ba".
Sarai na fahimci bugun gorar da yake yi mini, amma kallo ma bai ishe ni balle na tanka shi. Yana tsaye na gama ci na miƙe na wanko hannuna, sannan na sha ruwa tare da jan jakata na yi ɗaƙina. A jikina nake jin kallon da ya bi ni da shi, hakan ya tabbatar mini da kallon tuhuma ko zargi yake yi mini.

Har zan shiga toilet na fito domin na tunatar da yaran zuwa islamiya. Karaf na ji maganar Haidar yana faÉ—in "Abba mai masarar ta tafi ko? Har na so na je ta canza mini tawa na fasa, saboda tsoron ka yi mini faÉ—a tun da ka ce kada mu sake fitowa sai ta tafi..."

"Kai Haidar! Tashi ka je ku yi shirin makaranta lokaci yana ƙurewa". Ina ƙare faɗar hakan na juya zuciyata cike da ƙuna, domin zancen shi ya hasko mini korar da ya yi musu domin ya ji daɗin hira da mai masarar.

Har na gama sallah ban daina jin zafin abin a raina ba, waton shi bai hangen bayan shi kullum gaba kawai yake kallo. Ba ya gudun abin kunyar da zai janyo wa 'ya'yan shi gori musamman yanzu da suka fara girma.

"Allah wadaran naka ya lalace!"

Abin da na faɗa kenan bayan na sauke ƙatuwar ajiyar zuciya. Ina nan zaune kan sallaya suka shigo suna yi mini sallama za su je makaranta. Na yi musu fatan dawowa lafiya tare da addu'ar tsarin da na saba yi musu idan za su fita. Ficewarsu ya sa na goge ƙwallar da ta zubo mini a gefen ido, sannan na miƙe na yi sallar Asr, saboda an fara kiran sallah a masallatan da ke cikin unguwar.

Wanka na yi sannan na dawo falo na zauna ina aikin takardun da MD ya ba ni, zuciyata a cunkushe da damuwar rashin sanin ciwon kai irin na Mukhtar.
Tunanin yi wa MD godiya ya faɗo mini a rai, na ajiye biron da ke hannuna na ɗauki wayata da ke kusa da ni. Data na buɗe na saƙuna suka gama shigowa, sannan na nemo shi aka yi dace yana online. Na tura masa saƙo kamar haka,
"Baba Maigadi ya ba mu saƙonka, mun gode sosai Allah ya ƙara rufa asiri ya saka da alheri."

Sai da saƙon ya tafi sannan na fara dudduba sauran saƙonnin mutane ina bayar da amsa. Karaf na ji muryar Mukhtar a tsakiyar kaina.
"Na san za ki yi zargin wani abu dangane da abin da kika ji Haidar ya faÉ—a. To wallahi ni babu komai tsakanina da mai masara. Amma fa idan kin yarda don na san halinki da mugun zargin tsiya, mutum bai isa ya yi abu ba sai kin saka mai ido".

Ban kula shi ba balle na tanka, dannar wayata kawai nake yi ba tare da na ɗago kai ba, saboda hankalina yana kan wayar don na hango MD yana typing. Saƙon ya shigo kenan ina ƙoƙarin buɗewa, babu zato na ji Mukhtar ya fisge wayar daga hannuna.

Zumbur na miƙe cikin zafin nama na yi kan shi a fusace, saboda ƙoƙarin duba wayar da yake yi...

Mu haɗu a next page😛

D. AUTA CE✍🏼

*ABOKIN AIKINA*

*@HADIZA D. AUTA*

*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*

_*Ban yarda ba! Kuma ban amince a juya mini littafi ba, ko a yi amfani da shi ta kowace fuska ba tare da izini na ba. Saɓanin hakan zan ɗauki matakin gaggawa wanda babu sani balle sabo😼*_

*LAMBA TA GOMA.*

Cikin sauri ya yi gefe wayar a hannun shi yana dubawa, haushi ya sa na bar shi da wayar na dawo na zauna ina ci gaba aikina. Sai da ya gama binciken abin da yake son gani, sannan na fara jin maganganun da suka ƙara tunzura ni daga bakin shi.
"Wai ke har yaushe za ki gano aure yana da muhimmanci? To wallahi a wannan karon zan É—auki mummunan mataki a kan wannan munafukin mutumin..."
"Kafin ka É—auki mataki a kan shi, ka fara É—auka a kanka domin abin kunya da Allah wadai ba halin shi ba ne shi. Don haka ka yi duk abin da ka ga za ka iya tun da shi kwando yana iya ce wa rariya na yoyo".

A fusace na ba shi amsa, shiru ya ratsa a tsakani ba tare da ya ce komai ba. Ban É—ago ba balle na ga yanayin shi, amma jikina ya ba ni kallo na yake.
"Yanzu don Allah ke ba za ki mutunta auren da ke kanki? Babu hujjar da za ki riƙa balle ki halasta tarayyar da kike yi da wannan ƙaton mutumin. To bari ki ji abin da ba ki sani ba, wallahi idan na lamunci komai ba zan yarda da irin wannan cin kashin ba. Don haka zan ɗauki mataki a wannan karon tun da ke ba ki san zurum ba..."
"Ka riga da ka yi sake ɗan zaki ya girma, a yanzu na riga da na ƙuna ba na tarar ƙauri. Duk abin da za ka yi wallahi a jiraye nake domin babu abin da zai razana ni..."
"Haka kika ce?"
"Haka na faÉ—a!"
Fuu! Na ji ya wuce ba tare da ya ba ni wayar ba, na yi hanzarin ajiye rubutun na sha gaban shi cikin matsanancin fushi na ce, "Ba ni wayata!"
"Ba zan bayar ba...!"
Amsar da ya ba ni kenan bai gama rufe bakin shi ba, cikin azama na fara ƙwatar wayar ta ƙarfi a hannunshi. Kokawa muka fara yi da shi ina ƙoƙarin ƙwata yana hana ni, a bisa tsautsayi ya ɗaga wayar sama na yi zillo na bugo hannun shi ta suɓuce masa. Cikin zafin nama na yi ƙoƙarin cafko ta amma ban yi dacen hana ta kai wa ƙasa ba. Kife ta faɗi na duƙa zan ɗauka ya saka ƙafa ya shura ta ta daki bango gabaɗaya ta tarwatse.
Layina na kawai na duƙa na zare daga jikin kwankwatsattiyar wayar, sannan na juya ba tare da na ce da shi komai ba. Domin a lokacin komai zan iya yi masa ɓangaren aika-aikar da zan illata shi matuƙar na biye zuciyata, gudun aikin da-na-sani a zuci na yi jarumtar faɗar 'Innalillahi wa inn ilairraji'un' Allah ya taimaka na yi controlling temper ta cikin ɗan lokaci.

Takardun na kwashe na yi saurin shigewa ɗakina na rufe. Sannan na janyo sabuwar wayar da MD ya ba ni na saka layina da memoryna. Kasancewar akwai nefa a lokacin na jona caji na kwanta ina sauke numfashi a wahale, saboda yadda nake ji tamkar zuciyata za ta ɓalle ta fito a kan matsanancin bugun da take yi.
Tsawon lokaci ina cikin mawuyacin halin kafin zuciyar ta lafa numfashina ya daidaita. Ihun yara da bugun da ake yi wa ƙofar ɗakina hakan ya tabbatar mini da yara sun dawo. Daga nan inda nake na yi musu magana cikin ɗaga murya,
"Ku je ku yi shirin sallah!"
Shirun da na ji ya gasgata sun ji abin da na ce. Ko da aka yi kiran sallar magrib ban tashi ba har sai da aka fara tayar da Sallah. Sannan na miƙa cikin rashin kuzari na yi toilet na ɗoro arwala na yi sallah, na daɗe ina jera addu'o'i a kan Ubangiji ya kawo ƙarshen zamana da Mukhtar lafiya. Domin ba na fatar zuciya ta ɗebe ni na aikata abin da zai shafi mutuncin 'ya'yana na janyo wa Ummata da 'yan'uwana gori.

Daren ranar ban fita falo ba, a nan na ƙarasa aikin takardun sai da goman dare ta buga, sannan na gama na fito domin na ga a wani hali yarana suke. Addu'a na tofe su da ita sannan rufo musu ƙofa ina goge ƙwallar tausayinsu da ta gangaro mini.

Kasancewar ba na cikin walwalar zuciya setting ɗin WhatsApp kawai na yi, sai facebook da na ɗan leƙa bayan na buɗe. Ban wani jima ba na ajiye wayar saboda komai ya gundure ni, idan aka cire MD da ke gefen zuciyata motsi kaɗan sai na tuno shi a raina.
Chapter 11 · 0% Book details