← Book details Abokin Aikina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 68

Sashe 19

Abokin Aikina Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"A fito mana da su duka idan har sun ƙi bayar da jakar da kayan cikinta a yi musu duk abin da ya dace."
Abin da MD ya faɗa kenan fuskarsa a haɗe tare da rungume hannun shi a ƙirji yana feso iska a bakin shi. Ɗaya ɗan sandan ya fara yi musu sallama kamar yadda MD ya yi a farko. Mintuna a tsakani sai ga maza da mata suna fitowa daga cikin gidan fuskokinsu ɗauke da tsoro.
Sai da 'yansandan suka ƙare musu kallo sannan ɗaya ya ce da su, "Ina jakar wannan yarinyar da kuka ƙwace a cikin gidanku?" Kallon juna suka fara yi kamar ba su san komai ba.
"A gaskiya ranku ya daÉ—e ba mu san komai dangane da batun jaka ba."
Zancen wata koɗaɗɗiya kenan wadda fuskarta ta gama ƙonewa da bilicin. Maganar MD na ji a fusace cikin ɗaga murya ya ce, "A cikinsu wace ce ta zare miki hajabi?" Idona a kan Ummita na nuna ta da hannu tare da ƙarin bayani kamar haka,
"Ita ce ta cire mini hijabi, wurin kiciniyar cire mini riga jakar ta faÉ—i a wurin, lokacin da zan fito kuma na bar ta a can, saboda gudun tsira na manta shaf ban bi ta kan jakar ba."
"Minti biyar aka ba ki ki fito da jakar nan yanzun nan."
Wani daga cikin 'yan sandan ya yi maganar tare da nuna Ummita da bakin bindigar da ke hannun shi. Ummita ta fara zarar ido tana nuna kanta cikin wayancewa da ƙoƙarin zare kai ta ce,
"Ni ban É—auki jakarta ba, sai dai idan a cikinsu wani ya É—auka ban sani..."
Bahagon marin da wani É—an sanda ya kwaÉ—a mata, babu shi ta fasa ihu tare da komawa cikin gidan da gudu tamkar wata zararriya. Tara-tara 'yansandan suka yi da sauran maza da matan gidan suka jefa su motar shiga-ba-biya, sannan wata 'yar sandar da ke cikinsu ta faÉ—a gidan a sukwane.

Minti biyar kacal ta fito riƙe da ƙugun Ummita da ke riƙe da jakata tare da wani matashi hannun shi da ya ɗaga hannun shi sama alamun miƙa wuya. Motar aka watsa su duka sannan aka ba ni jakata bayan na buɗe ta gaban kowa, kuma na tabbatar musu da komai yana ciki yadda na saka.
Motar 'yansandan ta fara barin ƙofar gidan tare da mutanen gidan da suka kwasa, kafin ta MD ta bar wurin tare da ni da ke baya na hakimce ina hurar hanci. Amma duk da hakan nan take gumi ya jiƙa mini fuska, zuciyata ta hau bugawa da sauri tamkar za ta fasa ƙirjina ta fito waje.
Saboda hango Mukhtar dumu-dumu a cikin 'yan kallon da suka zagaye mu suna rabon idon ganin ƙwam. Wanda shi ma nake da tabbacin ya gan ni a lokacin da zan shiga motar MD, na yi mamaki matuƙa da ganin shi wurin, tare da ko-in-kulan da ya yi wa ganina ba tare ya nuna ya san ni ba, balle ya ɗauki mataki a kaina ko a kan MD.

Ban dawo natsuwata ba har sai da na ga mun shiga gidajen Sama road, mamaki ya so kashe ni saboda ganin da na yi ya doshi hanyar da za ta kai mu Bafarawa Estate.
'Ina zai kai ni?'
Ita ce tambayar da na yi wa kaina a zuciya, sai ga amsa tiryan-tiryan ta bayyana kanta. Domin kuwa ƙofar gidan Kawu Sale ya ci birki, gidan da Ummata take rayuwa tun da jajayen sawu har yanzu da girma ya kamata.
"Fita ki je! Kuma ki yi mini sallama da Umma!"
Zancen MD kenan a fusace kuma cikin ɗaga murya. Haka na fito tamkar wadda aka kama ta yi wa Sarki ƙarya. Haka na fito jiki a mace na ja jakar kayana da ta hannuna na yi cikin gidan, ba tare da na waigo ba balle na damu da ce masa na gode.
Saboda har raina ban ji daÉ—in taimakon da ya yi mini ba, tun da har ya kawo ni gidan a maimakon tashar da nake so ya kai ni.
'Tukunna ma wa ya sanar da shi unguwar su Umma da gidan duka?'
Tsaki na ja sannan na faɗa gidan ko sallama babu na yi ɗakin Inna Kulu ina haɗe fuska. Ummata da Inna Kulun duk suna tsakar gidan amma babu wanda na yi wa magana. Saboda tsabar mugun haushin da MD ya cusa mini a zuciya, ji nake yi tamkar na kama da wuta na ƙone ƙurmus kowa ma ya huta.
Ina ji lokacin da wani yaro ya shigo yana sanar da Ummata ana sallama da ita waje. Ban san ya aka yi ba ni dai na ji ta shigo tana balbala faÉ—a tamkar ta ci babu.
Sai ga ta cikin ɗakin tamkar an jefota, ba ta yi ƙasa a gwiwa ba kawai ta fara kai mini duka da hannu bibbiyu tana kuka. Da ƙyar Inna Kulu ta taɓe ni a hannunta bayan ta gama jibga ta son ranta har da gwabra kaina a bango.
Ban haushin abin da ta yi mini ba, domin ba na tantama a kan ta yi hakan ne kawai saboda ta huce haushin da na ba ta a lokacin, wanda ni ko kaÉ—an ban ji dukan ba, don zafin da zuciyata ke yi ya fi dukan da take yi mini linkin.
Inna Kulu ta fitar da ita daga É—akin tana haki, tare da jifa ta da miyagun maganganun da suka tsaya mini a zuciya. WanÉ—anda suka saka ni sabon kuka tare da yi wa Mukhtar Allah ya isa ta fi dubu, saboda shi ne ya shiga tsakanina da ita, kuma sanadin shi ne ta fara kyara ta, tare da jifa ta da miyagun kalamai munana, a duk lokacin da rigima ta haÉ—a ni da shi.

'Ina mafita?'
Tambayar da na yi wa kaina kenan bayan na gama naÉ—e maganganun Umma a kwanyata. Domin babu komai a cikinsu sai muguwar fata gare ni, a kan muddin ban koma gidan Mukhtar na ci gaba da zaman 'ya'yana ba.

Hmmmm! Ana dara ga dare ya yi

*ABOKIN AIKINA*

*@HADIZA D. AUTA*

*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*

*LAMBA SHA SHIDA.*

Daga nan ɗakin da nake ina jiyo sautinsu ita da Inna Kulu tar-tar a cikin kunnuwana. "Haba Kulu! Shi kenan kullum abu ɗaya za a dinga yi? Har yaushe Zaituna za ta gano abin da nake lurar da ita? To ni kam a wannan karon, wallahi zan fitar da wuyan hannuna a cikin duk abin da ya shafe ta. Ta je ta yi duk abin da take so tun da ta isa da kanta da rayuwarta, amma wallahi ba zan zauna da ita cikin gidan nan ina ganin wulgawar ta ba. Don duk lokacin da na tuna ta kashe aurenta ta bar 'ya'yanta a wulaƙance sai na ji baƙinciki."
"Ki yi haƙuri Habi, tun da dai hannunka ba ya ruɓewa ka yanke shi ka jefar." Zancen Inna Kulu kenan cikin tausasa murya a ƙoƙarin ta na tausar Ummata, daga mugun fushin da ta shiga tana ta feso hayaƙin maganganu masu nuni da zallar ɓacin ran da ta shiga, sannan kuma masu kama da yi mini baki a fakaice.
"To ke Kulu sau nawa mutum ya sa aka cire masa hannun aka jefar? Ai sai dai idan ba ta kama ba. Don haka ta tashi ta koma gidan mijinta yanzu tun muna shaida juna. Idan kuma zaman gidan take so ni zan bar mata gidan ta zauna, amma ba za mu jeru ni da ita ba"
Chapter 19 · 0% Book details