← Book details Abokin Aikina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 68

Sashe 3

Abokin Aikina Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Shiru na yi kawai ina ci gaba da tsiyayar ruwan hawayen da suka kasa tsaya mini tamkar burgaggen famfo. Na sani ita mai tausayin halin da nake ciki ce, amma wani lokaci ina jin haushin yadda take ganin ban iya zaman aure ba ne, shi ya sa Mukhtar yake shuka mini tsiyar da ya ga dama. Duk da ina jin takaicin kallon da take yi mini, ina yi mata uzuri saboda ba ta haɗu da rabin kwatar matsalar da nake ciki ba ne. Na san da ta shiga makamancin halin da nake ciki, wataƙila za ta fahimci yadda abin yake.

"A tara mata dubu ba za su iya haƙurin da nake yi gidan Mukhtar ba, a cikin matan dubu kuma har ke kanki Maman Taufiƙ ba za ki iya wata ɗaya da Mukhtar ba, a yadda na san halinki da tsattsauran ra'ayinki. Don haka ki bar kowa ya kalle ni a yadda ya fassara ni, ki bar kowa ya zage ni a yadda yake so. Na yafe wa duk wanda ya zage ni a cikin rashin sanin ba bisa haƙƙina ba, amma Mukhtar ba zan iya yafe masa ba ko da zan janyo wuta tana ƙona jikin shi..."
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'uun! Sau nawa zan ce ki san abin da kike faÉ—a Zaituna? Yanzu ribar me za ki ci idan kin yi wa mijinki uban 'ya'yanki Allah ya isa? Ba kya gudun wani abu ya same shi ta sanadin hakan?" Tambayoyin da ta jero mini kenan a ruÉ—e, saboda firgicin abin da ta ji a bakina, wanda inda da sabo ta saba ji amma ta kasa shanye wa kunnuwanta a duk lokacin da irin haka ta kama.

"Gaskiya ki gyara furutan da kike furzarwa ga mijinki..." "Duk abin da ta yi mini ke kika janyo. Don ke kika shigo zuga ta kina fakewa da ban haƙuri" zancen Mukhtar kenan a tsakiyar kanmu, zumbur ta miƙe tana faɗin "Allah dai shi ne masani a kan komai. Domin yadda nake fatar na zauna da mijina lafiya ita ma ina mata fatar hakan..." Idona a kanta ta fice ranta a ɓace, hakan ya sa na fara girgizar ƙafafuwana cikin matsanancin fushi na ce "Ranar da duk haƙƙin matar nan ya kama ka, wallahi ba za ka ji daɗin rayuwarka ba. Ka ji da haƙƙoƙan da ka ɗauka ka daina ƙoƙarin ɗora wa kanka wasu. Domin zargin da ke cin zuciyarka zai yi ta janyo maka musibar da ba ka san ina za ka shiga ba ranar lahira..." "Daman ai ke ba ki mini fatar na gama lafiya balle na shiga aljanna..." "Duk abin da za ka faɗa ka faɗa kanka tsaye, ni dai na sani haƙƙi bala'i ne mitsssss! Aikin kawai"
A fusace na miƙe na shige ɗakina tare da rufo ƙofa. Gado na faɗa ina rera kukan da na kasa tantance ainahin na mene ne nake yi. Shin tausayin kaina da ban yi sa'ar miji ba? Ko tausayin 'ya'yana da ban zaɓar musu uba nagari ba? Ko kuma tausayin MD da ya rufta rayuwar shi cikin bahagon auren da bai san lokacin haɗuwar shi da sanadin lalacewar shi ba? Ta ya zan fassara mafarin matsalata? Ta ya zan warware wa kaina baƙin ƙullin da ya hana ni jin daɗin aure? 'Allah kana gani ba ni da kowa sai kai. Ka kawo mini waraka daga matsalolin da ban san ya zan yi na shawo kansu ba'. Abin da na faɗa kenan a zuciyata cikin ƙanƙan da kai ga Ubangijina.

Hmmmm! Yanzu aka fara 😅

*ABOKIN AIKINA*

*@HADIZA D. AUTA*

*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*

*LAMBA TA HUÆŠU.*

Kiran sallar zuhur ya sa na miƙe jiri yana kwasa ta na ɗoro arwala. A zaune na yi sallah saboda ƙafafuwana da na jin ba za su iya ɗauka ta ba. Bayan na gama a nan kan sallaya na kwanta ina sharɓar hawaye, ban san lokacin da bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ni ba. Azababben ciwon kai ya farkar da ni babu shiri, saboda luguden da ake yi mini cikin kai ya linka yadda na saba ji, dafe kan na yi ina ta faɗin sunayen Allah a zuci da bakina. Kukan da cikina yake yi ya sa na yunƙura zan miƙe jiri ya kwashe ni na koma na zauna. Shiru na ɗan lokaci ina sauraron daddaƙar da ake yi mini cikin kan, sannan ina jin tashin ƙarar tv'nmu cikin kunnuwana daga nan inda nake, ƙarfin halin miƙewa na yi ina layi na fito daga ɗakin domin na samar wa kaina abin da zan iya ci. Ganin Mukhtar zaune a falon yana kallon waƙar Indiya, hakan ya sa na ji wani tuƙuƙin baƙinciki ya rufe mini zuciyata, don har ga Allah na tsani jin muryar shi ma balle na yi ido biyu da shi. Hakan ya sa duba ɗaya na yi masa na kawar da kai na shige kitchen, duk da raina ya ɓaci da ganin garar da yake ci shi kaɗai ba tare da ya neme ni ba. Duba da yadda ya san ban da lafiya tsawon kwanaki kuma ban ci komai ba. Sai maganin Chemist da yake siyo mini don bai yarda da zuwa asibiti ba. Ganin yake yi na cika jaye-jayen abin da zan ɗora masa wahala, ko yara ke ciwo sai an yi da ƙyar yake bari a je asibiti. Wani lokaci ma sai mun yi rigima sosai sannan yake jan yaro ya je da shi da kan shi, a ƙoƙarin shi na nuna jin haushin matsin lambar da nake yi masa. Ba zai je da ni ba ko ya ba ni damar zuwa da su ba, sai dai idan sun dawo na ga magungunan da aka siyo ban isa na ce komai ba.

A wannan karon ma tea kawai na iya haɗawa na fito. Ina ƙoƙarin shigewa ɗaki ƙamshin naman da yake ci ya cika mini hanci, amma hakan bai sa na waigo ba balle na yi masa ƙorafi. Zaune na yi bakin gadon na zuƙe shayin sannan na yi shiru ina nazarin yadda aka yi na rasa wayata. Domin hankalina duka ya dawo kanta saboda ita ce abokiyar hira ta, kuma ita ke ɗebe mini damuwa a duk lokacin da nake cikin ɓacin rai ko kaɗaici. Mintuna kaɗan da shan shayin na jiyo muryar wata tana sallama, kamar na share amma na kasa haƙuri na miƙe ina taku a hankali na fito domin, na ga wake sallamar. Firdausi ƙawata ce na gani ta nufo ni cikin fara'a tana faɗin "Ashe kina ɗaki?" "E, mu je daga ciki" Sai da ta yi gaba sannan na bi bayanta, bayan na aika wa Mukhtar mugun kallon da nake ji kamar na shaƙe masa wuya, saboda kallon da na ga yana yi muna ta gefen ido.
Chapter 3 · 0% Book details