← Book details Abokin Aikina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 68

Sashe 32

Abokin Aikina Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

_Gabaɗaya ya ɗaure ni da jijiyoyin jikina, na shiga tunanin maganganun shi tare da yadda zan fuskanci lamarin a tsanake. Domin na kare shi ba tare da an gano shi ne ya yi sanadin rasa mini kayan ba, amma na san duk abin da zan faɗa ba zan fita daga wannan laifin ba. Matuƙar ba gaskiyar zancen na tona ba domin na wanke kaina. Haƙiƙa zuciyata ta yi amanna da tsayuwa kai-da-fata, domin na yi masa garkuwar da za a kasa hango laifinsa, balle a jefe shi da wata maganar da ransa zai ɓaci."_
_Da wannan tunanin na kwana cikin raina, shi ko lallaɓa ni kawai yake yi tamkar wata sabon ƙwai har baccin ya ɗauke ni. Tun da safe ya fice gidan ko kayan cefane aiko mini ya yi a lokacin da rana ta take, domin na fahimci ko ido ba ya son mu haɗa kafin ya fita. Hakan ya sa jikina ya yi sanyi na tabbatar da cewa dole ce ta sa shi ya yi mini hakan, duba da yadda yake jin nauyina kuma yake jin kunya ta a kan abin da ya aikata mini._
_Ban san ya aka yi ba, mahaifiyar shi ta shigo ɗakin fuskarta a haɗe, tare da yin tagumi tana ƙare wa ɗakin kallo. Kafin ta yi magana cikin sanyin murya tamkar ta yi kuka._

"Don Allah ki yi haƙuri Zaituna, wallahi ban san wainar da yake shukawa ba sai yanzu da ya shiga yana yi mini bayani. Saboda a lokacin da na ji ana ɗibar kayan ana sakawa mota, sai da na kira shi na tambaye ina za a kai miki kaya. Kai-tsaye ya ce da ni daga gidanku aka aiko ɗauka, za a canza miki sababbi kafin ki dawo. Da wannan maganar ya rufe mini baki kuma ya toshe ƙofar zargin da ya shiga kaina. Don Allah ki yi haƙuri Zaituna, kuma in Sha Allah yau-yau ɗin nan duk inda zai nemo miki wasu kayan sai ya yi ko na tsine masa albar..."
"Haba-haba! Ai abin duka bai kai can ba Innar Hanafi. Ya yi mini bayanin komai tun jiya kuma na gamsu, don haka kada ki damar da kanki a kan hakan. In sha Allah babu abin da zai faru domin ba zan bari kowa ya san yadda gaskiyar abin yake ba. Kuma ya ce zai san yadda za a yi kafin hankalin mutane ya kawo kan kayan."

_Hawaye ta shiga sharewa da gefen mayafinta sannan ta fice gidan tamkar ta kife saboda sauri, domin fuskarta a haÉ—e take babu alamun wasa. Hakan ya tona asirin takaicin ta a kan abin da Mukhtar ya aikata mini ba tare da sanin ta ba._
_Bayan fitar ta da mintuna kaɗan ta aiko na rufo ɗakin na zo tana nema na, na yi wa Ummu Salma wanka na shirya ta tsaf tana zuba ƙamshi muka yi gidan. Haƙuri ta ƙara ba ni sannan ta roƙe ni da Allah kada na bari wani ya san da maganar, a cikin 'yan'uwana ko nasu. Saboda abin kunya ne da gori kawai hakan zai janyowa tare da faruwar abin da ba a yi tsammani ba. Don ta nuna mini muddin gidanmu aka sani rikici zai iya ɓallewa sanadin hakan, a ƙarshe ma abin ya shafi aurenmu._
_Har raina ba na fatar rabuwa da Mukhtar a lokacin, ko sakin da na nema ƙarfin hali ne kawai na yi domin na rage ƙunar da zuciyata ke yi._
_Daren ranar a gidansu Mukhtar na wuni, duk wanda ya zo a nan yake iske ni mu gaisa. Domin ko cefanen da ya aiko a nan na yi girkin ƙannen shi da Sajida ɗiyar Yayar shi suka taya ni. Domin Innar Hanafi tun da muka gama magana ta fice gidan, ba ta dawo ba har sai da duhun marece ya fara kawo jiki. Sannan ta zauna tana sauke numfashi, ina lura da fuskarta har da 'yar rama ta yi. Cike da mamakin me ya jigatar da ita take ta sauke numfashi alamun gajiya a tattare da ita._
_Abinci na kawo mata ta ci tana saka mini albarka, bayan ta gama ci ta ja ni ƙuryar ɗakinta ta ce na zauna. Cikin sanyin jiki na zauna zuciyata cike da tunanin abin da take ƙoƙarin sanar da ni, wanda ba ta so kowa ya ji daga ni sai ita sai Allah._
"Zaituna! Ina ƙara ba ki haƙuri a kan laifin da Mukhtar ya aikata miki. Kuma don Allah ki yafe masa don ko kaɗan bai yi miki adalci ba. Sannan abu na biyu da nake son sanar da ke, ki yi haƙuri a kan abin da za ki gani a ɗakinki. Na je na ƙulla da ƙyar na samo miki gado da kujeru, domin ba na farinciki mutane su taras da ke a yadda na gan ki babu komai sai faƙon ɗaki. Kuma don Allah kada ki bari hakan ya janyo muku tashin hankali ko ki ce za ki yi zuciya watarana ki sanar da Ummarki. Saboda muddin ta ji wannan magana ba za ta sake ganin girmansa idonta ba, kuma in Sha Allah sai ya biya ki kuɗin kayanki ko da arziƙi ko da tsiya-tsiya."

_Har ga Allah tausayinta ya kama ni, duba da yadda ta ɗaga hankalinta sosai a kan lamarin. Kuma kayan da ta faɗa na yi haƙuri da su, hakan ya nuna mini ita ce ta yi fafutukar nemo mini su, domin ta wanke kaso biyar a cikin goman laifin da Mukhtar ya aikata mini._
_Cike da ladabi na nuna mata babu komai kada ta damu, domin na ƙudurta komai za a yi mini a gida ba zan faɗi abin da zai sa a gano laifin Mukhtar ne ba._
_Sai da na yi sallar Isha sannan ƙannen shi suka raka ni ɗauke da Ummu Salma Sajida da kular abincin shi a hannu. Wanda na dawo takanas na ɗauki kula sabuwa na zuba masa, don Allah ya tsare bai taɓa mini kayan kitchen ba, sannan kuma na dawo da wasu sababbin da Umma ta saya mini na ƙara da waɗanda nake da su._

_Ƙwalla na shiga gogewa bayan ƙannensa sun tafi Sajida ma ta bi su sun fice. Na shiga dudduba kujerun da na gani a falona, sannan na nufi ƙuryar ɗaki na ga sabon gado da wadrobe har da madubi. Duk da ba su kai darajar nawa ba, amma har zuciyata na ji daɗin ganin su kuma na yi farinciki._
_Wanka na shiga sharp-sharp na kammala, sannan na feshe jikina da turaruka masu sanyi, na mulke jikina da wata shu'umar humra mai taken 'Yar Sakkwato. Saboda kayan matan da aka ɗirka mini da kazar ƙarin ni'imar da na ci, sun sa na ji ina kewar Mukhtar tare da zumuɗin ya kasance ni a raina. Kuma na yi alƙawarin zan faranta masa a daren ranar ko don Innar Hanafi, saboda ba ƙaramin daɗi na ji a kan kulawar da ta ba ni ba. Saɓanin baya da ba ta sake mini fuska tun bayan rikicin abincin da suka ce ina ba su kaɗan._
Chapter 32 · 0% Book details