← Book details A Jininsa Yake Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 28

Sashe 9

A Jininsa Yake Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba? Ga shi ta aje butar a waje. Ta juya ta fito tana kwala mata kira, yayin da dukkansu suka aje cokula suka fito. Kamar wasa, babu Zarah acikin gidan. Mamaki ya ishi Inna. Ta kama baki, tana kallon igiya babu hijabin da ta shanya. Sageer ya ce,"Wai ita Zarah da gaske take yi? Inna tayi shiru abin ya girmi shekarun ta. Naseer ya numfasa ya ce,"Inna ki gaya mata, idan ta ji ina asibiti kar ta sake ta zo guna. Zo mu je Sageer. Ya yi waje. Sageer ya ce,"Inna ki ce Allah ya bata hakuri. Sai anjima." Da kyar ta iya amsawa,"Allah ya ba mu alkhairi." Shi ma ya wuce. Inna ta ja kujera ta zauna, yau na ga zamani ni A'isha. Kiri- kiri yarinya ta ban kunya? Suna tafe a mota Sageer, ya ce,"Yanzu ina muka nufa? Ya ce,"Gidan za ni, duk ayi ta ta kare, idan ma yankana ni za su yi, su yanka. Ba shi kenan ba? Idan kowa yayi min, ai bai kamata Zarah ta yi min ba. Duk saboda wa na shiga wannan halin? Ba saboda sonta ba ne? Duk ba ta ga hakan ba." Ya furta. Sageer yayi shiru domin ya lura abokin sa ya zare gaba daya, kar ya tofa wani abu, ya kara masa zafi. Ya ci uban birki a kofar gidan, ya fito yayi cikib gida, bai ko saurari Sageer ba. Sai dai yana shigowa ciki ya tsinkayi Ameer na ta tsala kuka. Nan da nan ya yi turus, guiwa sa ta kwa6e, a salu6e yai sallama falon. Umma na kokarin goya Ameer a lkcn Abba kuwa na zaune gefe iya wuya yake. Kuma yana ji da kowa, duk wanda ya kuskura yi masa wata magana akan Naseer. Yana shigowa. Abba ya mike ya debi takalman sa ya bar gidan. Naseer ya bi shi da kallo, ya kasa cewa da shi komai, har Umma ta gama goyon, ta sa hannu ta dauke gwangwanin (Prisso-cream) din da ta siyo ta dora bisa firij, ta dauki fidar ta yi waje. Ita ma ya bi ta da kallo, sannan ya bi bayanta. Tana famfo tana wanke fidar da soso da omo. Ya bi ta, ya tsaya a gefen ta ya sanyaya murya,"Umma!Ji ta yi tamkar ya watsa mata wuta. Ranta ya ci gaba da k'una kamar ta rufe shi da dukan fitar hankali. Ya durk'usa ya mika hannayen sa gaba gare ta. Idanuwansa dauke da kwalla. "Umma, ki yi wa girman Allah ki amsa min. Umma ki dube ni ki saurari rokona. Na yi laifi Umma, amma tuni na gane kuskure na, ku ba ni dama ta karshe Umma. Da yardar Allah ba zan sake saba maku ba, Umma ki taimake ni." Ta gama dauraye fida, ta yarfe ruwan, ta juya ta koma daki tana daddaure su yadda suke. Naseer ya nemi wuri nan ya zanau dirshan! Sageer ya matso zai masa magana, yayi sauri ya riga shi." Je ka gidan abin ka Sageer. Na gode." Ya yi dan jim, yana kallon sa,"Ka ta fi na ce, babu komai, sai mun hadu." Ya numfasa ya ce,"Shi kenan, Allah shi kyauta." Ya juya ya fice, ba tare da Naseer ya sake cewa wani abu ba. Nan yayi ta zama har ya tuno, bai yi sallah ba. Yayi alwala a nan famfon, ya wucce sasan su, yayi Sallah a falo ya ci gaba da zama nan bisa sallaya. Babu abinda zuciyarsa bata saka masa ba. Zarah kuwa bata dowa ba, sai bayan sallar la'asar, ba shakkar komai. Ta yi sallama ta shigi ta wuce Inna a tsakar gida ta shigo daki. Inna ta tafa hannu ta ce,"Da izinin wa ki ka bar gidan nan? Ina kuma ki ka je? Kai tsaye ta amsa,"Inna ai na gaya maku ba zan koma ba. Kin zaci wasa na ke yi ko? Ta ce,"To ba kuwa zama a gidan nan ba, bari baban na ki ya shigo. Na lura so ki ke ki kawowa mutane raini. Ta juya ya bar dakin. Zarah ta matsa inda kulolin abinci ke aje, ta buda ta zuba ta hau ci. Karfe 5 M.Umar ya shigo gida, Inna ta feshe shi. Ya jinjina kai ya ce,"Wai Zarah da na sani ki ke fadi? Ta ce,"Ka na wasi-wasi kenan? Shiga tana nan a daki." Tunda ya baro dakinsa yake balbala masifa har cikin dakin."Ki hada kayan ki, ki koma inda ki ka fito! Ta ki motsi, M.Umar har da barazara duka, amma ko alama Zarah bata motsa ba, sai sharar kwalla take yi. M.Umar ya cika da al'ajabi, yana haki, ya koma dakin sa. Inna ta yi zuru tana kallon sabon salo. Fadi take cikin ranta,"Zarah ta kangare." Haka kowa ya kwana a wannan dare. Babu barcin kirki.

Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

Washe gari bayan sallar asuba. Nusaiba ke zaune bisa gado, tunani bisa tunani. Tun jiya take cikin wannan yanayin. Musamman da ga Abbanta ba shi cikin sukuni kuma tun isowarsu gida, babu inda ya sake fita. Tashin hankalinta ya k'ara tsananta, tun daga lkcn da ta ga nononta ya cika, har ya fara tsiyayewa a banza. Bakin takaicin dake cinta kenan, a halin yanzu bisa gado, ta rasa inda za ta tsoma ran ta, ta ji sanyi sbd tunanin dan kyakkyawan dan ta. Ta tabbata yana can yana kukan neman nono, ga shi nan yana zubewa a iska. Farkewa ta yi da kuka, sbd tausayin rayuwar da Naseer ya je fasu ita fa dan ta,. Ji ta yi an riko ta. Muryar Umminta ke fadin,"Nusaiba! Daina kuka, ki yi hkr. Ta fado jikin Ummi ta rungume ta. Ummi ta shafa kanta ta ce,"Ki yi shiru na ce. Allah ne ya kaddaro miki wannan al'amari. Yanzu dago fuskar ki ki ji. Ta dago, Ummi ta sa hannu ta share mata hawaye, kafin ta ce,"Abinda na ke so da ke Nusaiba, ki yi hakuri mu je a dauko yaron nan.Bawan Allah ne shi, bai da laifin komai. Sannan shayar da shi da za ki yi, shine yake sanya shakuwar uwa da danta, soyayya tare da jin kai.Ki sani Nusaiba Ubangiji ne kadai ya san dubun ladan da uwa take samu tun daga daukan ciki, haihuwa, raino tare da bada tarbiya, ga 'ya'yan da Allah ya bata,kar ki bari wannan gara6asar ta wuce ki Nusaiba. Ki dauko dan ki ya shaku da ke, ya san cewa ke ce mahaifiyar sa.
Ta yadda zai ji kan ki, a cikin zuciyar sa, idan Allah ya raya shi. Na yiwa Abban ki magana, na rarrashe shi, na kuma yi nasara, ya amince, yanzu yardar ki na zo nema, domin ya ce shi ba zai matsa miki ba, duk abinda ki ka za6a shi za'ayi.
Shi kuma Naseer din muna nan muna jiran sa, ya kawo miki takardar ki.
Yanzu me ki ka ce?
Ta goge kwallan da suka dararo mata, ta ce,"Ki je ki dauko shi Ummi, babu komai."
Ta tallafo fuskarta ta ce,"Yayi kyau. Allah yayi miki albarka.
Amma ki tashi ki shirya Direba zai kai mu, don ki kintso kayan ku a natsa.
Tashi ki daina kuka, ba na son ki na damuwa, kin kuma san Abbanki hankalin sa ba zai kwanta ba.
Ta goge hawayenta sarai,. Umma ta kama ta ta riko, ta raka ta hanyar bayi, sannan ta fice ita ma, don shiryawa.
Abban ke kwance a falon sama bisa kujera, shi kadai yake kallon silin yana lissafon halayyar Dan- adam mai abin mamaki.
Nusaiba ta shigo cikin shirin tafiya.
Kamar mai ciwo yake kwance, bai motsa ba har ta zo gun sa, yana kallon ta.
Ta tsugunna ta kwanto kanta jikinsa, ta yi shiru.
Ya daka kanta ya ce,"Bebina, ki je ki dauko dan ki, ki shayar da shi.
Allah zai ba ki lada, kin ji?Ta amsa da kai. Ya ce,"Mike ku tafi, na ga Ummin ki ta gama shiryawa.
Allah ya kiyaye hanya." Ta ce,"Amin Abba na." Ta mike ta wuce ya bi ta da kalllo, ta kai kofa, ta waigo suka hada ido, yayi dan murmushi yana mata (bye-bye) da hannu.
Ita ma ta yi masa, sannan ta sauka, lkcn karfe 7:30am. Ummi ta matsa mata ta dan ci kayan karin safe.
Karfe 8 Direba ya dauko su, suka damk'i hanya.
Karfe 8 din dai-dai. Naseer ya shigo falon, Umma, don gaishe su ko ba za su amsa masa ba.
Umman kadai ke falon,
tana ta faman gyangyadi.
Da alama Ameer ya sami barci, domin cikin dare yana ta jin kukan sa.
Bata kalle shi ba, ya durk'usa gaban ta, ya ce,"Umma ina kwana?
Kamar za ta kyale shi, sai wata zuciya ta ce, amsa.
Bata kalle shi ba ta ce, lafiya.
Farin ciki ya lullube shi, ya ce,"Na gode Umma.."
Ta kyale shi.
Yayi dan jim yana kallonta, kafin ya ce,"Umma ina Abba?
A fusace ta dube shi, ta yi masa tsawa,"Ga shi nan a baya na a goye!
Tabatacce maras kunya.
Ka sake zuwa ka tambaye ni, ina Abba ya ke, sai na ci mutuncin ka!
Yasa hannu ya dafa guiwoyinta ya ce,"Yi hakuRi Ummana, ba zan sake ba.Dama Zarah ce ta ce ba za ta dawo ba, sai Nusaiba ta dawo, shine nace ko za ki sa baki ta yi hkr ta dawo kafin a shawo kan Alhj?
Kai tsaye ta dube shi, tsakar ido ta ce,"Ban zuwa." Kar mu yi haka dake Ummana. Wallahi na yi nadamar abinda ya faru, ku sa ke ba ni dama ku gani zan rike Nusaiba iya rayuwata.
Ta dube shi a dage ta ce,"Bakin alkami ya riga ya bushe maka Naseer, domin jiya da daddare su M.Umar da M.Lawar sun zo. Amma Abbanka ka ya rantse, ya masu, babu ruwan sa a cikin maganar ka.
Haka ni ma bai lamunce min ba.
Saboda haka ka makara, dabara kuma ta rage wa mai shiga rijiya. Ina fatan ka gamsu.
Chapter 9 · 0% Book details