← Book details A Jininsa Yake Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 28

Sashe 8

A Jininsa Yake Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba za ka dan ci komai ba? Ya kada kai, bari dai in je in dawo. Ya fice, tana fadin a dawo lafiya. Ya kwankwasa kofar shagon, ya zo ya bude, suka koma ciki tare. Daga kallon Naseer kawai. Sageer ya gane yayi nadama, gaba daya ya jeme ya fita hayya cin sa. Ya dube shi a sanyaye ya ce,"Ka ga irin abubuwan da na ke gaya maka ko? Yanzu ina ribar wannan abu? Kullum ina gaya maka yi wa iyaye biyayya ibada ce, duk kuma mai yin sa ba zai ta6a ganin 6acin rai ba. Amma Naseer na ka ji, ni ban san abinda ke damun ka ba. Dan yaro jariri an ajiye maka shi, ina amfanin sa? Iyayen ka na ta kuka saboda kai, wacce irin masifa ce wannan? Ka farka daga bacci Naseer, kai ba yaro ba ne."Ya dube shi kwalla suka zubo ya ce,"Ban san abinda zan ce ba Sageer, domin ni kaina na san mai laifi ne, saboda haka duk hukuncin da aka yanke min, yayi dai-dai. Sai dai babu wanda ya san cewa na dade da yin nadama, sannan in na ce ba son Nusaiba yanzu, na yiwa raina karya. Shi ya sa na dage ba dare ba rana wajen kula da ita tare da rokon Allah ya bata lafiya, don in samu in nemi gafarar ta, na kuma nuna mata iya so da kaunar da na ke mata yanzu. Allah da ikonsa sai ta sami sauki, hankalinta ya dawo jikin ta, a lokacin da iyayen ta ke wajen, sannan bata 6ata lokaci ba, ta zayyane masu komai. Ka yarda da ni Sageer? Ka taimake ni, domin ni yanzu ban san yadda zan yi ba." Sageer yayi shiru, yana kada kai

Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

Tabbas ya yarda da maganganun Naseer, saboda yana daya cikin masu mmkin yadda Naseer ya rinka kula tare da ririta Nusaiba, sai dai a lokacin ya dauka saboda halin da ta shiga ne, kuma bata son kowa ya kusance ta, sai shi. Ya nisa kafin ya ce,"Yanzu tinkarar Abban, tashin hankali ne ba karami ba, kuma dole ne aje a same shi, tunda shine jigon komai. Abin yi shine, ka taso mu je wajen sa, ayi ta ta kare ko kashe mu zai yi." Ya kada kai,"Gaskiya Sageer ba zan iya ba.ka je kai kadai tukuna, ni na fi kowa sanin halin Abba." Ya ce,"Shi ke nan. Za ka jira ni a anan din ne? Je ka dawo ina jira. Ungo key din mota don ka yi sauri. Ya kar6a ya fito a sukwane, ya fada mota, yayi gidan su Naseer. Yayi sallama falon Abba, a lokacin Umma tana goya Ameer ta fito ta siyo masa madarar jarirai, bayan ta nemi Zarah ta rasa a cikin gidan, don bar mata ajiyar yaron kafin ta dawo. Shi yasa zuciyan Abba ke kara tafarfasa, ya sani babu makawa ita ma tafiyar ta ta yi. Da kyar ya amsa sallamar Sageer. Ya shigo a darare, ya nemi gefe ya makure, ya ce,"Sannu Abba." Ya ce,"Me aka yi Sageer? Ya ce,"Abba Naseer ne................Ya dakatar da shi da hannun sa kafin ya ce,"Tashi ka tafi! Sannan idan ka je, ka gaya masa ita ma wacce yake son ta tafi abinta, saboda haka ya zo ya kwashe kayan sa, ta bar min gidana in huta." Ya tashi ya durk'usa Abba................Ya runtse idanuwansa,"Sageer ina ganin mutuncinka, don Allah, don son Annabi ka tashi ka tafi. In dai akan maganar abokinka ne, na riga na datse magana, na yi rantsuwa Naseer ba zai sake sani kaffara ba. Saboda haka ka je ka gaya masa, shi 'yantacce ne, kar ya dami kan sa. Tashi, kanzil ban ka kara fadi ba, idan har ni ina isa in gaya maka. Idan kuma ban isa ba, to kacigaba da zama. Sageer ya shiga 3, Abba ya daddaure shi, ga magana bakin sa babu damar fadi, yana ji, yana gani, ya tashi ya fice. Yayi tsaye jikin mota ya rasa tudun dafawa. Ga wata sabuwa, kuma ita ma Zarah ta yi gaba. Duk da dai yana ganin na ta mai sauke ni, amma ba dadi ace ita ma tana gidan su.Ya fi minti 5r a tsaye, sannan ya bude mota zai shiga. Ya hango Umma tafe. Ya tar6e yana mata sannu da Zuwa. Ta amsa za ta wuce cikin gida, ya ce,"Umma ku taimaki ni Naseer na cikin wani hali, komai za iya faruwa da shi. Ta ce,"Shine me? Sai aka ce karshen Umma ya zo? Ya ce,"Ba haka ba ne Umma. Wallahi Naseer yayi nadama, tun ranar da ta sami kan ta cikin wannan yanayin, kuma ba shi da wani buri daya wuce idan ta ji sauki, ya bata hkr akan abinda yayi mata. Sai kuma aka sami akasi, komai ya yamutse. Ta yi dan murmushin takaici ta ce,"Yaro man kaza. To yanzu da ka zo nan ka na ta dogon bayani, akwai Nusaiba a nan ne? Tana fa Kaduna, a gaban Ka Babanta ya dauke ta. Ba sai ya je can ba, ya roke ta. Menene abin zafi? Ya durk'usa bisa guiwa, ya ce,"Ku yi wa girman Allah Umma ku yafe masa, ke ma kin san duk abinda ki ka fadi, ba zai yuwa ba. Sai da goyon bayan ku." Yana sa aya Abba na tsayawa kofar zauran, bai ce wa Umma komai ba, ta wuce cikin gida. Shi ma ya bi bayan ta. Sageer ya sauke numfashi, ya tashi ya fito ya tafi.

Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

Yana shiga shagon zama kawai yayi, ganin haka Naseer din ma yayi shiru, ya san babu nasara. Sun dau minti goma a haka, kafin Sageer ya ce,"Wai Zara ma ta tafi gidan su."Ya dube shi da sauri." Me na yimata ita kuma? Kashe ni suke so su yi ko? Shi kenan." Ya goge kwalla. Wayar sa ta hau bugawa, da kyar ya dauka. Yakubu ne ke kiran sa. Ya rasa ta yadda zai yi ya dauka. Ya dubi Sageer, ya ce,"Zo mu je gidan Yakubu." Ya tashi suka tafi. Ya maida masa bayanin komai. Yakubu yayi masa fada kamar zai ari baki, shi kansa ba karamar kunya ya ji ba lokacin da Alhj ya kira wayarsa, yana gaya masa Naseer ya ci amanarsa. Duk da haka yayi masa alkawarin shiga maganar, sai inda karfin sa ya kare. Shi kuwa Naseer B ana maganar, yana kallon kowa a dage, zuciyar sa gwanin haske, har yana addu'ar kada Allah yasa su shirya. Amma bisa fuskar sa, ya fi kowa nuna damuwa kamar yayi kuka. Daga gidan Yakubu, wajen Zarah suka iso, misalin karfe 1 na rana. Sun shigo gidan. Inna na kwashe abinci cikin kula. Ta daga ido ta dube su, tana amsa sallamar su. Gaban ta ya yanke ya fadi, ganin yadda Naseer yayi wanu duhu lokaci guda. Ta ce,"Dan Inna! An gaishe ka da aiki. Ku shiga gani nan zuwa." Ya wuce simi-simi. Sageer ya bi bayan sa, suna zaune. Inna ta gama abinda take yi a kicin, ta bi su dakin. Zarah ta leko daga bayi ta ga Inna, ta shige sai ta sadado ta aje buta, ta suri hijabin Inna dake shanye bisa igiya ta yi waje ta bar unguwar. "Sannu dan Inna, ka sha aiki Wallahi, ya gajiya? , Ya sunkuyar da kai Sageer ya ce,"Inna kuskure ne, kin kuma san ajizanci irin na Dan-adam. Amma a yau ya gane, har ya tuba........ Ta katse shi, tuban mazuru? Sau nawa Naseer ke cewa ya tuba a gidan na ma kawai, wanda na sani? Ai ba zan iya fadi ba. Yanzu wa gari ya waya? Babu abinda ba mu gaya maka ba D'an Inna, tun kafin ayi auran nan. Bayan anyi kuma, ba mu fasa ba, sai dai in kafar ka bata shigo da kai gidan nan ba, amma ba ka ji. A fuska lafiya lau ka ke, halin ne kawai ka kasa gyara shi, su yi dai-dai da fuskar ka. Me yasa? A yanzu wa ka ke ganin zai iya tunkar Alhj? Babu abinda za mu iya gaya masa, ya yarda, saboda ka riga ka rushe ginin tun ranar zane. Naseer ya ce,"To Inna shi kenan, haka za'a sa ido, auran ya kare kenan? Ta ce, "Eh mana, ta riga ta gayawa Babanta ba ka son ta, wa ka ke zaton zai je ya ce, karya ne? Ya ce,"Gaskiya Inna ban yarda ba, na san ana zuwa biko Inna. Sai dai in ba za ki je min ba ne kawai
Ta yi dan murmushin dole ta ce,"Dan Inna manya, ga laifi, ga saurin tuba. To shi kenan, ka bari Baban na ku ya dawo, za mu san yadda za'a yi." Ya numfasa ya ce,"Wai ita ma Zarah don ta kara min hawan jini shine ta bar gida ko? Ina take, sai ta ci dan banzan duka yau, in ni sa'an ta ne, za ta gaya min." Dariya suke da Inna da Sageer, kafin Inna ta ce,"Yanzu ta shiga bayi, za ta yi alwala ta yi sallah." "Ina nan ina jiran ta ta fito,." Inna ta mike,"Bari in kawo maku abinci Sageer. To Inna. Sageer ya amsa. Ta fice,"Sageer ya ce, "Na ciro maka wayar Rediyon can ne?, Me zan yi da ita? Dukan mana harka mance? Tsaki yayi ya dauke kai. Inna ta shigo da abinci ta ce,"Ka fa ci. Sageer ka matsa ma sa ya ci. Ya ce,"Ai zai ci Inna." Ta yi waje ta koma daki. Shiru- shiru Zarah ta ki fitowa daga bayi. Inna ta fito da wannan mamakin, tana tambayar kanta,"Ita wannan zaman me take yi a bayi?" Tana sa aya, ta aje ido bisa buta a gefe. Ta leko dakin ta ce,"An gama dukan?" To ai ban ji kuka ba, bata daku ba kenan." Suna dariya ya ce,"Ai bata shigo ba Inna.." Ta gintse fara'a ya ce,"Ban gane
Chapter 8 · 0% Book details