Sashe 28
A Jininsa Yake Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko Zarah ta gyara gidan su dai-dai gwargwado tare da taimakon Naseer. A cikin su da iyayen su babu wanda bai keta hazo ba, ya sauke faralinsa. Komai maka Allah shekaruna mikawa hada da tarindaukaka. Naseer ke zaune shi kadai bisa kujeran alfarma a farfajiyar bayan gidansa. Yayi shiru ya zunduma taunan baya, har ya zo kan rayuwar da yake cikin ta a halin yanzu. Ya dubi tafkeken gidan sa a birnin Potugal, mallakar sa wanda ya zuba makudan daloli ya siya. Babu abinda ke ransa, sai dumbin godiya ga Ubangiji da yayi masa baiwar da ba kowa ke samun irin ta ba. Sannan ya mallaka masa ingantattun mata na nunuwa a fadin duniya.Zarah idan ya tuna irin baiwar da Allah yayi mata na kaifin hankali da sanin yakamata, ya tuna ita ta fara gaya masa rayuwa shirin Allah ce, bai kamata Dan-adam yana alkawari a hurumin da ba nasa ba, sai ya ji son ta ya shafe ko'ina a jikin sa, yana neman zautar da shi. Nusaiba matar da yake wa yak'inin sa'a ce a gare shi, Allah ne yayi masa arziki daga gare ta, 'ya'ya da dukiya tare da fice a duniya. In dai ana maganar wasan Polo, duk masoya wasan sun san da Naseer Jah-Jah. Shi yasa idan ya dube ta, haka kawai ya kan ji hawaye sun cika idanuwansa, sbd tsabar tausayin kan sa, da ace ya rasa ta akan wautar banza. Son ta ruwa ne, ya aje wa ransa, don ko ya fadi, shi kansa yana ganin karya yake yi. Yayi mika, take nan kewar su ta kama shi, domin babu ko dayan su a tare da shi. Zarah na jarabawar karshe ta kamala B-ed din ta. Nusaiba kuwa ta na watan haihuwa ta 6. Ita kadayaushe ta fi son haihuwa a gida. Gaba daya hankalin sa ya koma gun sun, daren nan ya kasa barci. Kamar wasa zuciyar sa ta rasa sukuni, ba shiri ya nemi hutun shekara. Bai hada sati ba, ya baro Potugal, sai ganin sa suka yi kwatsam! ----------------------------------------------------------------------------------------------- Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ 'Ya'yan sa suka baibaye shi, tun isowar sa har la'asar yana tare da su. Direba yayi kiran su lkcn Islamiyya, kowanne ya fito cikin shiri, ya shiga mota. Direba ya wuce da su. Zarah ta idar da Sallah, ta fito babban falo ta iske Nusaiba zaune tana kallo. Kusa da ita ta zauna tana fadin,"Ki na nan ki na kallon fadace-fadacen nan da ya ki ci ya kicinyewa." Ta ce,"Ke dai bari, ai ni wannan fadan na k'asashen larabawan nan tsoro yake ba ni." Zarah ta ce, ke me kika fahimta daga gare shi? Ta ce,"Karshen duniya mana. Dama ance idan zamani ya zo karshe, alamun har da 6arkewar rikicin k'asashen gabas ta tsakiya. Yanzu dubi k'asashe nawa ke rigima, ana kashe su, kamar ana kashe kiyashi, tsakanin mu a musulmi kenan." Zarah ta tallafe kunci ta ce,"Wannan rayuwa tana firgita ni, me mu2m ya kamata yayi, banda ya kadaita Allah, yayi masa ibada, sannan idan ya ci, ya bada sadaka, don neman karshe mai kyau? Ta ce,"Wallahi kuwa Antina, musamman na mu mata da aka ce mun fi yawa a gidan wuta. Biyayyar aure ce matsalar mu komai muka yi gidan miji lada ne. Amma sai ki ga abin ya gagara. Kar ma ace miki akwai abokiyar zama, abin ya fi kazanta. Sai ki ga mace ta mance cewar akwai hikimomi da yawa cikin auren mace fiya da daya shi yasa Ubangiji ya halasta shi. Haka kawai ta dauki bakin kishi ta dorawa kanta, daga nan ne za ta fadawa hallaka. Allah ya kiyashe mu. Zarah ta kamo hannun ta, suka runtse,"Kin yi gaskiya amarya, shi yasa na ke wa Allah godiya da yasa ke ce abokiyar zama na." Ta yi murmushi,"Ni din Antina? Na fi kowa farin cikin samunki. Allah ya k'ara hada kan mu, ta yadda yayanmu zai ci gaba da samun kwanciyar hankali. ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Tafi suka ji ana yi ta bayan su. Duk suka waigo,yayan na su ne a tsaye yana jin su. Ya zagayo suna dariya ya tsaya gaban su, ya ce,"To a matsa min in zauna." Suka ware ya zauna tsakiyar su." Allah ya kamaku, ashe zama ku ke kuna gumalta ko? Zarah ta kama baki, "Lah! Allah mai halitta, jaba ta dubi bakin mijinta. Gulmar me kuma a mu ka yi ta ka? Ya kamo kunneta. Nusaiba na kwasar dariya, ya ce,"Ita jabar 6ata dubin ta ba ne? Ta ce,"Oho." Ya k'ara murdawa, ta yi k'ara. Nusaiba ta kamo na shi ta ce,"Allah sakar min Antina, ko ni ma in cire na ka. "Ya saki ya dube ta,"I see, kun hada kai ko? O.k, yayi kyau, ke ba zan ta6a ba, kin zama yangwam! Amma ke, za mu hadu." Duk suka yi dariya. Ya rungumo kafadansu ya sake fadin,"Allah ya yi maku albarka, kun zama abin alfahari na, kun zama jigon rayuwa ta. Na kuma gane rayuwa shirin Ubangiji ce, mutane da yawa suna samun dama, amma sai su ki amafi da da damar har ta wuce su, daga baya su zo suna cizon yatsa. Allah ya ba mu ikon amafin da damar mu." Suka nisa suka amsa da Amin. Kowacce ta dora kanta bisa kafadar gefen sa. Suka yi shiru na 'yan dakikai. Cikin shirun ne suka ji kamar suatin T.V, a wani sashi na gidan. Naseer ya ce ,"Wai ba duka yaran nan sun taifi makaranta ba?. Eh mana." ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Ya mike yana fadin,"Ga sautin (Game) can ina j? Duk suka mike suka bi shi sashin yara. Ameer ne ya kuke yana buga Game na tseren Polo, sautin T.V ya rage can k'asa, yi yake kamar zai tashi sama, sbd kwaikwayon yadda dawakan ke gudu. Naseer ya lalla6o ya cafke kunnansa, a tsorace ya waigo manyan idanuwan nan na sa. Suka kara yo waje tamkar Naseer a zamanin da yake shagalinsa a filin sukuwa. Bai tanka masa ba, yai ta jan kunnan sa har falo, sai su Zarah ke ta faman salati suna fadin,"Amma dai Ameer Allah ya shirye ka! Ya tsaya ya k'are masa kallo, kafin ya ce,"Kai ne babba, amma babban kwabo? Kullum da kai ake complain! To zan kwashe Game din tunda shi ke hana ka zuwa makaranta! Yayi sukuiti yana kumbura. Nusaiba ta zungure shi, "Maras kunya, sai anyi magana, ya rink'a cika yana hura hanci, wa ka fi zuciya? Come on wuce ka dau ko jaka Lado ya kai ka! Zarah ta kamo shi,"Wuce mu je, ka dauko jakar, kai ba ka ganin kannin ka sun tafi? Ta raka shi ya dauko jaka. Nusaiba na ta fada, ta fita ta kira Lado Direba, yasa shi a mota zai wuce da shi." Nusaiba ta zauna kusa da Naseer ta ce,"Ameer sai addu, ace yaro baya maida hankali a karatu. Sai game din tsiya? Shi yasa ban so ka kawo masu wannan sabin Game din ba." Ya ce,"Zai bari ne." Zarah ta dawo ta zauna inda ta tashi,"Ameer kenan an dai tafi ana ta kunci,"Nusaiba ta ce,"Ai kin ji Babansa ya ce zai bari ne, amma complain din Ameer yayi yawa, ko makarantar kuka suke da rashin maida hankalinsa, ga masifa, ni na rasa irin sa." Ya ce,"Ni kuwa in na kalle shi, dariya yake ba ni." Kin ji ko Antina? Ta ce,"Ya dai kamata ka sa baki, ka yi masa fada sosai, kafin ka bar garin nan, kila ya fi jin na ka. Ameer yan aikin gidan nan bai kyale ba, haka 'yan kanninsa. Aliyu kadai bakin sa ke ceton sa da yake duk gautan ja ne. Baba na da Alhaji kuwa, sai dai su yi kuka su share hawaye, balle kuma 'yan matan." Ya kama kai, ya ce,"Wayyo Abba na, duk wannan laifin shi kadai? Wai ba yarinta bace? Nusaiba ta ce,Yarinta? Me yasa............ Ya katseta,"Ya isa! A yimin shut up nace! Rashin jin nan fa kowa yayi shi, ke kin yi, ke ma kin yi. Ni ma na yi." Nusaiba ta ce,"Oho, ashe abin gado ne, ta 6angaranka, amma mu ba muyi rashin jin kin zuwa makaranta ba." Yayi 'yar dariya ya ce,"Yan rainin wayau, kun cika ni da , kamar ban san sirrin kowacce ba." ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Zarah ta gyara zama ta ce,"Ai sai ka fadi"Yalla6ai, mu na ji." Ya dube ta, ya ce,"Ke fa kullum ki na like bayan taga, ki na zuba ihu, hawaye sharaf-sharaf, majina har baki. Da an tambaye ki menene? Sai ki ce kudin (Break) dina ne suka 6ace." Ya fadi yana kwaikwayon muryart har da shashshekar kuka. Ya juya kan Nusaiba,"Ke kuma ai Abba ya gaya min da zarar Direba ya fito da mota, zai kai ki makaranta, sai ki ce kashi ki ke ji." Ni din? Zarah ta ce,"Ke ma ki ka tsaya tambayar sa. Ta figo filon kujera. Nusaiba ma ta dauko na ta, suka rufe shi da duka. Me zai yi ba dariya ba, yana fadin,"Mugaye, k'arya na yi.........? Na kwashe 'yan biro na da takarduna na bar gidan, don ba zan iya ceton Naseer ba. Tsokanar fada A JININ SA YAKE!!! , saboda haka ALHAMDU-LILLAH, na gaji da shari"a. Idan kuma akwai ma iyawa, to Bismillah! Jah-Jah na can yana dakuwa a hannun zaratan matan sa.." ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ afuwan bakujini da wuriba sakamakon wayata tadan samu matsala, daga bayakuma nadanyi rashim lafiya, your prayer is needed pls
Zaharaddeen Shomar
Whatspp 08168575100
Zaharaddeen Shomar
Whatspp 08168575100