Sashe 15
A Jininsa Yake Part 3 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Ai shi kenan tunda baya son ta dawo!
Ya nemi waje nan ya zauna dabas, ya cire hula zufa ta keto masa.
Zara bata iya kara komai ba, ta ma tashi ta bar wajen.
Umma na jin sa, kanzil ba ta ce da shi ba.
Bayan sallar la'asar, yana kwance dakin sa ya rasa abinda ke masa dadi, kamar an kwaso son Nusaiba an kara cusa masa cikin zuciya, sannan a 'yan kwananin nan da bai ga Ameer ba, duk kewarsa ta ishe shi.Gaba daya abubuwan sun dagule masa, domin ya sani ba za su ta6a daidaitawa da Abbansa ba, muddin Nusaiba bata dawo cikin gidan nan. Ya runtse ido, ya dafe kai kamar ya kwarma ihu. Zumbur ya mike ya kwashi makullai, ya fice ko Zarah bata sani ba, ya fada mota. Ya sake yi wa Kaduna tsinke. Yana zuwa. Sakatare ya ce Alhj ya tashi.
Yana kokarin fitowa daga get. Motar Yakubu na shigowa. Suka tsaya kowa ya fito gaba dayan su, babu mai walwala a fuska. Yakubu ya fara magana,"Ko ka ji abinda ya faru?" Ya ce,"Na me ? Ya ce,"Na rufe (Dabai Riders) mana.
Alhj ya rufe kulob, yadda yake gaya min ma ya sa dawakan a kasuwa har an samu masu siya." Salati Naseer ya fara yi, kafin ya ce,"Saboda me? Ya numfasa ya ce,"Wallahi ban sani ba, amma tun faruwar wannan al'amarin na ku hankalin Alhj a tashe yake. Iyaka kokari na, akan ya sauya shawara, amma ya ce ra'ayin sa ne.."
Naseer ya k'ara tarus! Idanuwan sa suka kawo kwalla, ya ce,"Yakubu ban san yadda zan yi ba, dazun nan na zo na yi magiya gun sa, ya ce in je zai neme ni, wai ina zuwa gida. Na tarar an kwashe kayan Nusaiba kaf. Lambarta ba'a samu.
Kuma ni na san rufe kulob din nan, duk baya rasa nasaba da matsalar nan, wata kila yana ganin ta dalililin Polo ya hadu da ni.Ban san abin yi ba Yakubu? Ya ce,"Gaskiya ne. Magana kan ta gama lalacewa. Ka san komai Alhj zai iya yi saboda Nusaiba, kar ka manta ita ce 'yar sa kawai. Sannan duk abinda ya faru, kai ka jawa kanka, domin ba karamar asara ka yi ba. Sai ka yi addu'a Allah ya sa hakan shine alkhairi. Gida ka nufa?
Ya kada kai,"Ina nan sai na ga abinda ya turewa buzu nad'i. Yakubu ya ce,"To sai ka dawo,"Goodluck." Na gode." Naseer ya fice, shi kuma ya karaso wajen sakatare, ya aje abubuwan daya zo da su.
Gidan Naseer ya nufa. Alhj na tare da baki. Yayi sallama ta gaishe su. Alhj ya bi shi da kallo. Ya ce "Dama na zo ganin ka ne, bari in jira ka." Ganin mutane a wajen yasa ya amsa." To ina zuwa."Naseer ya fita, motar sa ya zauna yayi ta ji