Sashe 22
A Jininsa Yake Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajinisa Yake3-05 Posted by ANaM Dorayi on 11:43 AM, 25-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______ Ta ce,"Ba zai wuce wannan yaron da ta kwallafawa rai ba. Ta shaku da Ameer ko alama bata son a raba su. Ameer kuwa dole ya koma gidan ubansa, sanin kan ta ne ba zai kyale mata shi ba. Alh. Basheer yayi shiru, Injiniya ke fadin,"Nusaiba manya, abubuwanta dariya suke ban, na ga yadda za'ayi wannan al'amari." Alh. Ya ce,"Ku kyale ta, zan yi maganin abin."Suka saki wannan shafin, suka kama wani, dare yayi Alhj ya tafi masaukin sa. Yana tunani tare ba tare da yayi wa Nusaiba maganar Ibrham ba. Koda dama bisa hanya yake, harkokinsa ne, suka kawo shi, hanya ta ratso da shi nan. ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Yana zaune cikin ofis a gida Nijeriya, misalin 11 rana. Naseer yayi sallama ya shigo. Ya amsa,"Lafiya lau. Ya jikin na Zarah? Ya ce,"An gode Allah. Wannan karon dai Likita ya ce dole ta huta daga wannan, saboda mahaifar ta ta yi rauni da yawa. Ya dan kada kai,"Ayya, gaskiya ya kamata ta huta, saboda lafiyar ta, ayi hakuri da abinda Allah ya kaddaro." Ya ce,"Haka ne. Dama tun jiya na zo in nuna maka Result. Ya fito na kammala Diploma." Ya washe baki,"Ah! Lallai abin ba wuya a wurin Allah." Yasa hannu ya kar6i takardu, ya duba,"Kai! First class! Gaskiya takardun sun yi kyau. Yana 'yar dariya ya shafi keya, ya ce,"Sun ba ni (Adimission ABU), Direct. Next month za'a fara Rigistireshon. Alhj ya miko masa hannu,"Congrat! Kai na ji dadi., Allah ya bada sa'a." Amin." Ya fadi bakin sa ya ki rufuwa, ganin yadda Alhj ke murna. Ya mike yana fadin,"Zan koma Abba, na gaishe ka." Ya ce,"To na gode. Zan tura ma da sako(Acconut) din ka, ba yawa, sai ayi Rijistireshon ko? Ya tsugunna yayi godiya.Alhjn ya jawo dirowa, ya dauko farar ambulan ya mika masa,"Wannan ma sakon ka ne." Cikin mamaki yasa hannu ya kar6a ya kara godiya ya fice. Yana shiga mota da rawar jiki, ya buda ambulan, don ganin me ke cikin su? Wasu zaradan hotunan Ameer, ya rinka zarowa daya bayan daya guda 24 kala-kala. Wasu tun yana dan wata 4 a zaune, wasu yana rarrafe, da yawa a tsaye yake. Ya zura wa hotuna ido, kamar ya sume, saboda doki da farin ciki. Ya sumbata, ya rungume ya ma rasa inda zai aje su. Take nan ya kira wayar Zarah,"Kin ga yadda Ameer dina yayi girma? Ta ce,"A ina ka gan shi? Hotunansa Abba ya zo min da shu, sai kin ga yaron Zarah, kamar dan larabawa." Ta ce,"Ka na ta sa min rai, yayana ka kawo min in gani mana." Ya ce,"Ki jira, yanzu zan baro Kaduna." Ta ce,"Allah ya tsare." Ya ce,"Amin. Ya kashe waya. Ya bi hoton hannun sa da kallo, can ya sauke numfashi, ya sake sumbatar sa, sannan yayi wa mota key, ya ya wuce. Yana isa Zariya. Su Umma ya fara kai wa hotuna suka gani. Umma ta dauki daya. Ya kai wa Inna ita ma ta za6i na ta. Daga nan ya cilla Shika ya kai wa Zarah. Wai ta ga hotuna kamar ta dauko Ameer yayi motsi a gaban su. Nan ya bar mata 2. Fitowar sa asibiti a hanya ya shiga shagon sai da (Gift) da (Frem) na sa Hotuna ya siyo kanana guda 24. Gaba daya hotunan sai da ya sa su cikin frem har da na wajen su Umma da Inna. Sageer an ba shi. Yakubu ma, ya samu har da dakin Hajiyar sa.Naseer B ma ya ce yana so a ba shi. Naseer kamar zai hauka ce, saboda son Ameer. Bayan kwana 2 daya koma Kaduna. Haka ya ga hoton bisa tebur din Alhj gaba dayan firem din mai kyan gaske. Ba k'aramin dadi ya ji ba. Shi yasa ya k'ara kaimi wajen addu'ar sa. Allah ya dai-daita auran sa da Nusaibansa. ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sati 3 tsakani, cikin Zarah ya k'i zama, wannan karon ko wata 7 bai kai ba, watan sa 6. Dole aka bi shawarar Likitan nan take aka juya mata mahaifa, don ta huta da wahala, domin ba k'aramar wuya take ci ba kafin ta haihu, ban da jinin da take zubdawa. Yaya za ta yi? Haka Allah ya kaddaro. Ubangiji yasa kaffara ce. Bayan ta gagije, lafiya ta zauna mata sai Naseer ya neman mata F.C.E. Ta samu a saukake, shi ya gama mata komai ta fara karatu. English/Islamic. Asabar da lahadi ya fita da ita koyon mota, tun tana tsoro har ta kware. Cikin sati na 3, ita ke kai kan ta makaranta. Shi ke nan ya sakar mata (Honda Civic) din sa. Shi yana amfani da Jeep kawai. Kasancewar Sageer zai tafi sabis din sa bana, sai shagon dinkin sa yayi rauni. Ba sosai yake zama ba, su Abbas ne kula masa da shi. Idan ya taso makaranta yake zama ko ranakun da babu karatu. Kusan ace hankalin Naseer kwance yake, amma Allah kadai yasan abinda ke damunsa a dangane da son dawowa da Nusaiba gidan sa.Ba shi da bakin magana ne kawai, ko kuma mu ce babu wanda zai kai wa kukan sa balle a share masa hawaye. Shi yasa wani lokacin za ka gan shi a rame, wani lokacin kuma babu laifi. Bayan wata 2 da dawowar Alh. Basheer Jordan yana ta binciken halin da Nusaiba suke ciki da Ibrahim. Babu wani sauyi, kodayaushe nuna masa take ba za ta aure shi ba, shine dai ya k'i hak'ura. Jin haka yasa Alh.Basheer ya ce maza-maza ta dawo gida Nijeriya ta yi aure anan. Ta shiga shirin kaya, cikin bak'in ciki da 6acin rai har ta rink'a jin kamar ta cewa Ibrahim ya fito, don ta san tabbas Ibrahim na tsananin sonta. Amma da ta tuna abinda Sakina ta yi mata a filin jirgi, sai ta yi turus! A tunanin ta da kyar Sakina za ta bar ta sakewa gidan Ibrahim. Saboda haka ta watsar da maganar Ibrahim, ta ci gaba da shirinta ko gaya masa bata yi ba. Ana gobe za ta dawo. Alh. Basheer ya kira Naseer ya same shi a ofis. Yana zaune, yayi shiru yana jiran ya ji dalilin kiransa. Alhj ya dan gyara fuska ya ce,"Gobe Nusaiba za ta dawo maka da Ameer, saboda ta sami miji za ta yi aure. Shine nace zan gaya maka, idan sun iso, ka zo ka kar6i abin ka, ka sa shi makaranta, tunda da bakin sa. K'iris ya rage ba'a zare ran Naseer ba, daga inda yake zaune, domin ilahirin kwakwalwarsa sa ta daina aiki.Yayi zugudun, kai sunkuye, bai motsa ba, balle ya ce wani abu. Alh. Basheer ya zura masa ido, jim kafin ya sake fadin. "Ka na iya tafiya, dama shi kenan sak'on, da zarar sun iso, zan kira ka a waya." Ya dago ya dube shi, ido cike da kwalla, sun kada jajur, bakin sa dauke da magana, sai dai ya kasa furtawa, sai ya ce to kawai. Da kyar ya mike ya nufi kofa. Alhj ya bi shi da kallo. Goge hawaye yake da bayan hannu. Yasa kofa zai buda. Alhajin ya kira shi. Ya waigo a gigice, yana amsawa. Yayi jim kafin ya ce,"Don Allah ka gaida min Malama Balarabe da kyau." Ya hadiye miyau, ya ce,"Zai ji Insha-Allahu." Ya buda, kofa ya fice. Ya shigo gida karfe 7 na magariba. Kwanciya yayi a dakin sa ya rasa abinda ke masa dadi a duniya. Zarah ta yi tambayar duniya, ya kyale ta. Ta yi mita har ta gaji, bata samu wata amsa ba, duk ranta yayi mata k'unci. Cikin dare ta farka, ba shi cikin dakin." Ta fito ta biyo shi, yana falo zaune cikin duhu, sai da ta kunna fitila sannan ta gan shi. Ta matsa gaban sa ta ce,"Ikon Allah, watau yayana she akwai wani lokaci da zai zo, wanda ba dole ba ne in san me ke damunka? Gaskiya ne.............. Ya katse ta,"Zarah ba wata magana bace. Ameer ne za'a dawo min da shi. Nusaiba za ta yi aure." Ta numfasa ta koma dirshan ta zauna kafin ta ce,"Amma yaya ka na da abin mamaki. Nusaiba za ta yi aure, ba dole ta dawo maka da danka ba? Menene abin damuwa a nan? Yayi mata wani mugun kallon da bai ta6a yi mata irin sa ba, ya ce "Babu! Rok'ona gun ki shi ne ki koma ki sha barcin ki. Please and Please!Ta bi shi da kallo, bata ma san me ke bata mamaki ba. Ta buda baki za ta yi magana, ya kwarara mata tsawa,"Ki tashi na ce ko? Ban son jin komai nace! Idanuwanta suka cika da hawaye, ta tashi da gudu ta nufi. Sashin ta kuka kala-kala ta rink'a yi, kamar yadda tunanin ta yake kala-kala. Lallai son Nusaiba ya zauna masa, ko kuwa don yana ganin ita bata aje masa da ba ne, shi yasa ya fara yi mata kwakwazo? To ai daga Allah ne, kuma bata bakin cikin soyayyar sa da Nusaiba. Me yasa zai juya mata baya yau? Kafin safiya, idanuwanta sun kunbura. ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Naseer na kallon ta, tana shirin tafiya makaranta. Ransa ya k'ara 6aci. Tana ta wanke- wanke a kicin ya biyo ta, bayan ta ya rungume, ya sumbace ta, ya rada mata,"I'm sorry. Jini na ne ya hau, kar ki yi fushi da ni sweet Zarah." Ta runtse ido, hawaye suka zubo, ya juyo ta ya share su." Ya isa haka, ai ya wuce ko? La66anta na rawa ta ce,"Yayana ba na bakin ciki. Ko ka fara son Nusaiba, kuma ina maku murna idan da za'a ce gidan nan za ta dawo. Amma menene na yi min ihu saboda na fadi gaskiya? Saboda ban aje maka da ba ko?