← Book details A Jininsa Yake Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 28

Sashe 3

A Jininsa Yake Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya nufi ofishin likitan daya dauka na musamman, cikin zafinsa ya shiga, a tsaye ya fara fadin. "Wai me ke faruwa ne Doctor? Ban gane condition din yarinya ta ba! Shi ma ya mike cikin sanyin murya ya ce,"Cool down Alhj, zauna." "No I can't sit Doctor! Kullum yarinya sai k'ara rikicewa take! Why? Wai ba anan ku ka yi mata tiyata ba ne? Ya ce,"Alhj babu wata maganar an ta6o mata wata jijiya. Infact, aikin ta bai shafi ko'ina a jikinta ba, sai inda Bebi yake. Ka zauna mu yi magana, Please! Da kyar ya zauna, shi ma Lkita ya zauna." Dama kai na ke jiran zuwan ka mu yi magana. Nusaiba ta fada cikin matsananciyar damuwa, wacce har ta sanya ta fizge-fizge, alhalin tana da ciki. Babbar matsalar ce ga mai ciki idan ta sami kan ta a irin wannan yanayin, domin ya kan kai a rasa su duka. Shine za ka ga mutan kauye da suka jahilci abin sai su ce bugun jinin ne, maimakon a hanzarta kawo ta asibiti, don daukan matakin gaggawa, sai a shiga hayaki da shafe-shafen turaren aljanu. Daga karshe ka ga an rasa uwa da Da. Abinda na ke so ka gane anan, damuwa babu abinda bata haifarwa, amma ina son ku natsu, za mu bicike da kyau, mu gano aininhin abinda ke damunta. A halin yanzun muna Expecting comma ta shiga, abinda muke magana kenan da sauran Doctor." Alhj fa bai yarda."Wannan ba comma bace, ta6in hankali ne, sbd haka idan ku yi bincike a kwakwalwarta, ko nawa ne zan kashe! Ya ce,"Wannan duk ba matsala, yanzu zan rubutu gwaje-gwaje da hotunan da za'ayi. Idan an rubuta kudaden, sai aje a biya." Rubuta min, in je a biya kudin." Yana zaune Likita ya rubuta duk binciken da za'ayo. Tare suka fito, ya hada shida Yaron da zai raka shi ofisoshin da za su rubuta kudaden. Al'amarin Nusaiba kuwa ta rikita kowa, kuka kawai suke yi. Shi kan sa Bebin kukan yake tsalawa, yana jin yunwa, amma ta hana su yi 'yan dabara a lika shi, ya sha nono. Naseer ya doso wajen, tun daga Nesa ya tsinkari muryar ta. Da gudun sa ya karaso, yana tambayar Zarah! "Me ya faru?, Murya na rawa ta ce,"Nusaiba ta rikice Kai tsaye ya shiga dakin, ya zube jakar da ke hannunsa, ya nufi gunta yana fadin,"Ya haka Umma? Duk suka dare, suka ba shi wuri, tana kyallo ido ta gan shi, ta zaburo tana mika masa hannu, "Abba na! Abba na, ina ta nemanka za su kashe ni? Bai san lkcn daya rungumota ba,"Menene? Iye? Ba ki san akwai ciwo a jikin ki ba? Allah da ikon sa, shiru tayi, tana ajiyar zuciya,"Kai na ke ta kira Abba na, ka ki zuwa, kai ma ba ka so na ne? Idanuwansa suka cika da kwalla. Kowa yayi waje yana share hawaye. Ya jima kafin ya ce,"Ai gani na zo, me aka yi? Wa ya sanya min ke kuka? Ta zura masa ido ta ce,"Antina suka kashe min, shine suka zo ni ma suka danne ni, za su kashe." An ce miki Antinki bata mutu ba, tsaya ki gan ta. Zarah! Ya kira ta. Ta shigo, ya jawo hannayensu ya hada,"Kin gan ta? Antinki ce. Ta fizge hannunta, ta saka ihu,"Ba ita bace! Allah ba ita bace,"Antina ta mutu Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi Ya rufe bakinta ya ce,"Shi kenan na ce, shi kenan ba ita bace." Zarah ta yi sauri ta fice. Sannan tayi shiru. Ya dube ta ya ce,"Abinda ki ke yi, ba shi da kyau, ki na jin Bebin mu na kuka, kin ki bashi nono, me ki ke nufi? Ta ce,"Abba na ina naga Bebi kuma? Ga shi can a waje, yana kuka."Ta ta6e baki ta ce,"Ban haihu ba, Antina ce ta mutu. Ya kamo ha6arta ya ce,"Dube ni, ki saurara da kyau, za ki ji kukan Bebi. A kawo shi ya sha? Tayi shiru, tana kallonsa. Ya sake kiran Zarah, ya ce ta kawo Bebi,. Ta zo da shi a shawul, ya kar6e shi, ta tsaya tana kallonta! Ya ce,"Yauwa, dube shi ki gani." Kyakkyawan kallo tai masa! Ya ce,"Yauwa, dube shi ki gani, kyakkyawa da shi." Ta leko ta dube shi,"Abba na wannan k'aton Yaron ai ya girme ni." Ya ce,"Ban son shirme, ba shi ki gani, idan bai sha ba, ki min duka." Ya dora mata shi bisa jikinta, ta 6allo wa Zarah harara, sannan ta dubi Naseer,"Abba na ka ce wa matar nan ta fita, ban son ganin ta. Munafuka kawai, duk sune suka kashe Antina." Hawaye suka kawo wa Zarah, ta juya ta fita. Ya ce,"To ta fita, ba shi ya sha. Ta ciro ta ba shi, ya kama sai tsotsa yake yi, bawan Allah ya sha kuka, shi yasa bai jima ba, barci ya kwashe shi. Naseeer yayi zuru, yana kallon su, tsabar tausayinta yake ji, kamar ya ce wayyo Allah. Ta ce,"Abba na ka daina kallo na mana." Ya ce, "Ah! Ai kowa dole in kalle ki, tunda ina son ki, kin zama abar kallona. Ko kuwa? Ta sadda kai, tana dan murmushi. Ya dan k'ara matso ta, ya ce,"Kin ga har yayi barci, to ke ma ya kamata ki kwanta ki yi barcin, ki huta ko?Ta yi hamma mai tsawo, yana rufe da bakinta, kafin ta ce, "Barci?" Kin ga ni ban son shirmen nan na ce. Kawo Bebin a kwantar da shi, ke ma ki kwanta ki gani." Ta ce,"Bar shi kawai, ya yi min dadin rikewa." Hirar su kawai suke yi, abin ya ba kowa mmk, har Alh.Basheer ya gama zirga-zirgar sa, ya dawo. Ummi ce ta mayar masa da yadda aka yi, ta yi shiru ta natsu. Ya shigo dakin a hankali Naseer ya mike yana masa sannu da zuwa, da ta fasa wata irin k'ara, gaba dayan su gigicewa suka yi. Naseer bai san lkcn daya koma gun ta ba,"Menene? Idanuwanta rufe tana fadin,"Ban son ganin sa! Ban son ganinsa!! Munafiki ne............. Ya rufe bakin ta, yayin da Alh.Basheer yayi waje da sauri. Naseer ya ce,"Ban son abinda ki ke yi Nusaiba, gaskiya ni ma zan tafi." Ta ce,"Na daina Abba." Ta ci gaba da surutu k'asa- k'asa,"Munafikin banza, munafikin wofi, ya wani shigo wa mutane ko kunya." Yayi shiru, ya kyaleta, kwalla suka zubo masa, ya share. Wannan al'amari da me yayi kama? Kuma fa duk shine sila ko? Ya tambayi kan sa. Wasu hawayen sharshar! Suka fito, ya sake gogewa. Alhj kuwa yana tare da su Ummi, shi ma sai da ya share kwalla, sannan ya mayar da yadda suka yi da Likita, kuma nan ba jimawa, za so zo su tafi da ita dakin hoto. Jama'a sun sha Zagi da tsinuwa lkcn da aka zo daukan ta, har da Naseer din da yake fada aji, ya zama munafiki, tunda yana gani zai kyale a tafi a kashe ta. Dole Likita yasa aka kawo masa wata allura, da kan sa ya zurkud'a mata. Take nan ta wuce luuuu....!!! Ba rai, ba dalilinsa. Sannan da masu daukan ta suka gara ta wajen hoto.Har aka dawo da ita, bata sani ba, nan suka bar ta tana ta barci. Hankalin kam ba a kwance yake ba. 'Yan dubiya na ta zuwa gaishe ta, amma tana barci, da yawa daga cikin su daga Kaduna suke zuwa. Haka Antin Jordan kodayaushe sai ta bugo ta tambayi jikinta. Bizar ta kawai take jira a gama, ta kamo hanya. Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Sakamakon duk gwaje-gwajen da aka yi mata suka fito. Likita ya kira Alhj ofishinsa, shi kuma ya kira Naseer, domin mijinta ne, hakkinsa ne ya san halin da matar sa ke ciki. Kowanne ya ja kujera ya zauna gaban Likita. Shi kuma ya firfito da sakamako, ya ci gaba da bayani."A gaba daya binciken da mu ka yi, babu wata matsala a tattare da ita. Kwakwalwarta lafiya lau, zuciya ma haka, k'oda lafiya lau, haka jirin ta lafiya yake. Saboda haka abin nan dana fara gaya maka Alhj, shi din dai za mu ci gaba da kula da ita akan shi." Alhj ya ce,"Yanzu ka na nufin tsabar damuwa ce ta jefa ta a wannan yanayin? Ya ce,"Kar ka yi mamaki, damuwa tana sanya hawan jini, kuma babu ga mai juna biyu. Saboda haka za mu ci gaba da bata taimakon daya dace, sannan daga wajen ku a matsayin ku na iyaye da mijin ta, rarrashi ne kawai. A ring'a lalla6ata, a kodayaushe, hanklinta ya zamana a kwance yake tare da samun isashshen barci. Insha Allah za ta warware, sai kun yi mamaki."Alhj ya munfusa, ya dubi Naseer,"Ka ji ko? Wannan aikin ka ne, ko dama kai kadai take son gani, mu duk mun zama munafukai. Don Allah ka yi hakuri da ita, sannan a rink'a had'a mata da addu'a. Idanuwansa cike da hawaye ya amsa,"Ya zama dole Abba, Allah ya taimake mu." Duk suka amsa da Amin." Tun lkcn aka bar wa Naseer ragamar komai ahanununsa, kowa ya koma gida, sai dai su zo akai-akai su duba ta, shi ma ta, taga, idan har idan ta 2, idan kuwa har ka ga wanin Naseer a kusa da ita, tabbaci hakika barci take yi. Zarah ma an sallame ta, ta koma gida, amma kodayaushe zuciyar na asibitin, shi yasa bata iya daurewa kullum ne sai ta zo, koda za ta wuni a waje tana lek'en taga tare da renon Ameer. Haka Likitocin ta ke iyakar kokarin su ba dare, ba rana akan ta. Magana ce ta kudi. Alh.Basheer kuwa ya saki komai ya dace ayi mata, komai tsadar magani. Shi kuwa d'an gogon, bai gajiya da yi mata hidima, shi ne cin ta, shine shan ta. Kullum yana like da ita, suna hiar shirme, domin kuwa shirme ce, yanzun nan za'ayi magana dai-dai, lkc guda sai ta ya6o shirmenta. Babu abinda ya dame ta.Idan dare yayi kuwa tana barci, zama yake bisa kujera ya zura mata ido, yana yi mata addu'o'i. Idan
Chapter 3 · 0% Book details