← Book details A Jininsa Yake Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 28

Sashe 7

A Jininsa Yake Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai kai alheri ka k'ulla, sai dai ka san a wannan zamanin ba kowa yake son ayi masa za6in abinda ya kamace shi a ruywar sa ba. Ya fi son abinda ra'ayinsa ya ba shi. Ka ga kuskuren da aka samu. Ina alfari da kai Abba na, kuma ko a yanzu ka sake za6a min miji. Wallahi zan aure shi. Bai san lkcn da ya rungume ta, ya fara kwalla ba. Haka Ummi ke ta share hawaye, tana sawa Nusaiba albarka. Ta mike ta shiga hada kaya. Hayaniyar hama'a suka jiwo gaba daya jama'ar Naseer ne. Zarah ma kayan barci ne ajikin ta, ta dora zani ta sa hijabi. Suka doro cikin dakin. Zarah na fadin,"Amarya!Ta zaburo da gudu, "Antina! Suka rungume juna, sun sha kuka, sai da Umma ta raba su ita ma, ta rungume ta. Daga nan ta matsa ta gaida kowa. Su Malam Balarabe, Malam Umar. Ya gaisa da Sageer da amayar sa. Bayan an gama gaishe-gaishe. Malam Balarabe yasa aka yi addu'a, kowa ya shafa. Aanan suka lura babu Naseer tun shigowar su. Inna ta fara magana,"Jama'a wai ina dan Inna ne? Malam Umar ya ce,"Kai wai dama babu Naseer a wajen nan? Sageer ya amsa,"Ai kuwa baya wajen nan, tunda muka zo? Malam Balarabe ya ce,"Ah to ina ya je? Ya fadi, yana kallon Alh.Basheer. Ya ce,"Gaskiya ban san inda ya je ba. Kuma dama ina son ganin ka, idan ba za ka damu ba." Ya ce,"Bismillah Alhj, ba damuwa." Suka fito waje, yayin da Zarah da Nusaiba ke like da juna suna maida yadda abubuwa suka faru. Alh.Basheer ya kebe da M.Balarabe, ya kwashe bayanin da Nusaiba tayi masa kaf, ya gaya masa. Tun da ya soma magana, gaba daya jijiyoyin jikin Malam Balarane suka tsinke, jiri ya fara dibar sa. Allah yasa a zaune suke, da babu abinda zai hana shi faduwa. Tabbas ya san Naseer baya son auran nan, aka yi shi, amma ko alama bai ta6a sanin rashin mutunci da wulakancin da ya rinka aikatawa ba. Ya jima kafin ya ce,"Alhj wannan magana ta ban kunya, kuma Wallahi tallahi ban san komai a game da zancan ba. Nusaiba bata nuna mana ba, balle ta furta da bakin ta. Don girman Allah ka yi hakuri Alhj. Ya ce,"Ai magana ta k'are, tunda baya son ta, ni ina son abata kuma zan tafi da ita, ba tare da 6ata lkc ba. Amma D'a, ban sako mata shi cikin gara ba, sbd haka nan za ta aje shi ko ya kashe ko ya bar shi da rai, duk ya rage nasa. A karshe, ka gaya masa na gode. Allah ya saka da alkhairi. Kan M.Balarane yayi gingirinn! Kunya kamar ya nutse kasa. Idanuwan sa suka cika da kwalla, ya rasa me zai ce wa Alhj? Kawai sai ya juya ya dawo dakin, gaban kowa ya daga murya ya ce,"Nusaiba, don me za ki min haka???Akan me za ki zauna sama da shekaru 2 cikin wulakanci da bak'in ciki, amma muna tare, ki kasa gaya min? Ba ki min adalci ba Nusaiba, domin da kin gaya min da tuni na yanke hukunci, sai dai ya nemi wani uban, ba ni ba! Kowa yayi tsuru-tsuru. Nusaiba kuwa tuni ta fara kuka. Ya matsa gadabn Ummi ya tsugunna." Hajiya ki yi wa girman Allah, ki yi hakuri. D'a ne ka haife shi ba ka haifi halin sa ba. Ko alama ban san halin da suke ciki da matar sa ba. Ga mahaifiyar sa nan a zaune, ko ita da ke zama tare da su munafikin Yaron nan bai ta6a barin ta gane wani abu ba, balle ni da ban zama cikin gida. Maganar tafiya da Nusaiba kuwa kun yi dai-dai, domin ko ni ne hakan zan yi. Saboda haka kowa yayi shaida. Ni Balarabe na tsame hannu na akan komai daya shafi Naseer, duk abinda ya ga dama yayi rayuwa ce................ Ya fashe da kuka, jikin kowa yayi sanyi, matan da ke wajen ma tuni suka soma taya shi, musamman Umma da ta ji abin kamar saukar aradu. Sageer ma waje yayi kirjin sa na bugawa, ga ranar da yake jin tsoron zuwanta, kullum yana gaya wa Naseer. Amma kunnuwansa iskar duniya ta dode masa su. M.Umar da Alhj suka riko M.Balarabe,"Ka yi shiru haka,"Malam Balarabe, kar zuciya ya kwashe ka, ka yi masa baki." Ya dube su ya ce,"Ni Naseer yayi wa tijara haka, Babu komai, rayuwa ce!Ya dubi Umma ya ce gaba,"Ke dauko masa D'ansa mu tafi, ki kai masa kayansa, idan ya ga dama ya jefa shi bola! Malam Umar ya ce,"A' ba'a yi haka bane, duk ku zauna a sasanta magana. Ai in rai ya 6aci, hankali ke nemo shi. Alhj ka yi hakuri, mu zauna da Naseer mu ji ta bakin sa, don girman Allah kar ku yanke hukunci kai tsaye haka." Alhj ya kada kai,"Ban k'i taka ba. Amma Naseer ya riga ya k'are magana, sai dai hukuncin daya yanke ne ban yarda da shi ba, d'a kan ba na mu bane, na shi ne. Don haka anan za'a bar shi. Iya magana kenan." Malam Balarabe ya ce,"Magana tayi dai- dai Alhj, ku bar masa shi, ya san uwar da za ta shayar masa D'an shi. Ki dauko shi mu tafi, na gaya miki, idan kuma ki na nan, ni na wuce! Yayi waje. Malam Umar ya bi shi. Umma ta dubi Ummi, ta ce,"Don girman Allah Hajiya kar ku yi wa Yaron nan haka, shi bai san komai ba, ku tausaya masa." Tayi shiru, ta rasa me za ta ce? Yadda Alhj ya fusato, babu mai sa shi dukan D'an nan. Haka Zarah ta rike Nusaiba,"Amarya kar ki ta fi, don Allah ki taimake ni. Idan ki ka tafi da wa zan zauna? Suka k'ara fashewa da kuka. Ita dai Fa'iza ba baki, sai ido. Bata fahimce komai ba, take ta faman kuka. Alhj ya fice ya bar su nan, suna ta faman magiya. Jim kadan ya dawo tare da Likita. Shi dai ya ga ana ta koke- koke, a zaton sa duk na murna ne, yayi abbuwan da zai yi, ya gama ya ba su sallama tare da takardar magunguna da za ta ci gaba da sha na tsawon kwana 7.Alhj da kansa ya rink'a dibar kaya yana kaiwa cikin mota, har ya kwashe su duka. Ya kamo hannun Nusaiba, ya wuce da ita. Ummi ta biyo bayan su, suka bar Umma da jariri bisa gado, yana ta faman barci. Ta k'ara fasa kuka. Inna ta kamota tana rarrashi. Haka Zarah ke durk'ushe, hannu 2 bisa kai.

Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

Daga inda Naseer ke 6oye, yana hango su Alhj suka zo suka wuce a moTa. Yasa hannu ya goge hawayen da ke kuncinsa. Jimawa kadan ya hangi su Umma. Inna na dauke da Ameer, suka shiga motar da ta kawo su. Direba ya ja suka bar asibitin. Wasu hawayen suka sake zubo masa, yayi kamar ya hadiyi zuciya ya mutu. Ya nufi inda ya aje motar sa, ya shiga haka ya dawo gida, baya gani wuri sosai. Ya rasa inda zai je, sai yayi fakin kofar shago, ya shiga ya sallami su Abbas ya ce duk su tafi gida. Ya kulle kansa ciki, ya rasa abinda ke masa dadi a duniya. Cikin gidansu kuwa kamar anyi mutuwa, shiru ba ka jin motsin kowa. Jim kadan Zarah ta fito da jakar kayan ta, ta lallabo zuwa sasan su Umma. Ta leko a hankali, ta ga babu kowa, ta cire takalmanta ta wuce sadaf-sadaf kamar 6arauniya. Tayi waje kan ta tsaye tayi gidan su. Inna ta zura mata ido, kafin ta ce,"Ke kuma fa? Ta shige uwar daki da gudu. Inna ta biyota,"Na ce ke kuma fa? Kin shige da gudu. Menene na ce? Ta ce,"Allah Inna ni ma ba zan zauna ba. Haba ai wulakancin yayi yawa, ko alama yayana baya jin magana. Ta balbaleta da fada,"Laifin waye? Ai duk ku na sane, aka rasa wacce za ta gaya wa manya, don ayi maganin abin, sai yanzu da zance ya lalace, za ki ce Naseer ne baya jin magana? Maza dauko jakar nan, ki koma inda ki ka fito, tun kafin Babanki ya k'araso gidan nan, ya sameki." Ta 6arke da kuka, tana fadin,"Ba inda za ni Inna, idan har na koma gidan nan, to yayana ya dawo da Nusaiba. Kuma ku matsa min ku gani. Wallahi tafiya ta zan yi." Inna tasa mata ido tallafe da baki. "Ki ka ce me? Lallai wuyanki ya isa yanka, to zan ji idan kke ki ka haife mu." Ta yi zamanta bakin gado, har Inna ta gama babatun ta, ta fice." Na rantse da Allah ba zan koma ba, ya je ya ci kan sa a gidan, tunda shi ba'a gaya masa ya ji." Koda Malam Umar ya dawo, babu yadda ya iya yi da ita, ya gama fadansa da barazanarsa ko gezau zuciyar Zarah bata yi ba, kuma ta rantse ta maya, muddin suka bari ta bar nan, ba za su sake ganin ta ba. Shi yasa da ta dauko jaka ta fito. Inna ta dauko muciya ta kora ta daki, ta ce,"Koma daki marasa kunya, idan Naseer din ya zo ya dauke ki! Ta maida jaka ta yi zamanta cikin dacin rai da takaici tare da tausayin Nusaiba da karamin goyonta.
Sageer ma da ke zaune a dakinsa, babu abinda ya fi damun sa irin dan karamin yaron da aka aje. Alhalin bai san komai ba. Fa'iza ta ce,"Yakamata ku taimaka wa yaron nan a maida shi wajen Maman shi,"Wallahi shi ne abin tausayi, ba ka ji yadda na ke ji ba, kamar inyi tsuntsu kai shi wajen ta." Ya ce,"Shirun nan da ki ka ga nayi. Ameer kawai na ke tunani." Yayi hucin zafi, ya dauko waya daga aljihu ya nemo lambar Naseer. Ta dan jima tana bugawa kafin ya dauka, ya ce,"Ka na ina ne? Murya dishe ya amsa,"Shago." "To ina zuwa." Ya kashe waya, ya dubi Fa'iza,"Wai yana shago, bari in je in same shi." Ta ce,"To
Chapter 7 · 0% Book details