← Book details A Jininsa Yake Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 28

Sashe 23

A Jininsa Yake Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan da nan idanuwan sa suka kada,"Kin san abinda ki ke fadi kuwa Zarah? Kin maida ni jahili kenan, ban san Allah ba? Ya juya mata baya, ban ta6a zaton wannan maganar ba daga gare ki Zarah."Take nan ta amsa laifinta, sai dai ka fin ta mik'a hannu, ta kamo na sa, yayi waje ya bar kicin din. Tana kokarin biyo shi, ta ji tashin motar sa. Tana fitowa wajen Mai gadi na rufe get, ya riga ya fice. Ta koma falo ta zauna, tana mai nadamar furucin ta. Daga ita har Naseer babu wanda ya fahimci karatun ranar. Shi kam Naseer caji 2 ke kan sa, shi yasa ya kashe wayayinsa, baya son magana da kowa. Bai dawo gida ba sai bayan issha, yana shigowa falo, ya ji ta a jikinsa, kiris ya rage ta kada shi. Mafarin daya rike ta sosai kenan. Ta ce,"Yayana na tuba. Allah na tuba ba zan sake ba." Yayi ajiyar zuciya mai karfi, ya kamo hannunta, suka zauna. Ya dube ta ya ce,"Magana makamanciyar wannan kar ki sake min ita, idan ki na son farin ciki na a duniya." Ta kama kunuwanta 2, ta ce,"Ba zan sake ba yayana." Ya jawo kafadar ta, ta kwanto masa,"Ya wuce, shi kenan." Ta ce,"To yaya su Nusaiba, sun iso? Ya ce,"Ni wayoyina ma kulle suke tun safe, ba na son ya kira ni, so ban san halin da suke ciki ba." Ta ce,"Hakuri za ka yi yayana, su gani suke har yanzu ba ka son ta ne." Yayi shiru ya rasa me zai ce? Ta dan dube shi. "Zo mu ci abinci ko? Ya ja hancin ta, ya ce,"Sure." Suka tashi suka nufi tebur don cin abinci."A dai- dai wannan lokaci Alh.Basheer da Nusaiba tare da Ameer suka shigo gida. Alhj ya dauko su daga filin jirgi. Ummi ta tar6e su, murna kamar su lashe juna. Duk da Ameer bai santa ba, ya saki jikinsa da ita sosai. Da yake shi ba mai bakunta ba ne. Bayan sun ci abinci, an yi masa wanka yai barci, ita ma ta kintsa, ta tafi kiran Abbanta, yana falonsa kwance labarai yake kallo. ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Tana shigowa ya tashi zaune yana fadin,"Zo nan 'yar albarka." Tana murmushi ta zo gun sa ta zauna. Ya ce,"Yauwa. Magana za mu yi. Kin tuna alkawarin da ki kai min a asibiti? Ta dube shi,"Wane alkawari Abba? Ya ce,"Lokacin da rigamar auran ki da Naseer ta taso. Ina ganin laifina ne, amma ki ka ce a'a, kuma ko nan gaba na sake za6a miki wani mijin, za ki aure shi. Kin tuna? Ta kada kai, ta ce,"Na tuna Abba." To za ki iya ciki min shi? Ta dan yi shiru, kafin ta ce,"Zan cika Abba na, umurnin ka kawai na ke jira." Ya rungumo kafadar ta ya ce,"Allah yayi miki albarka. Kafin nan na riga na gaya wa Naseer za ki dawo masa da Ameer. So kafin ya zo, ki tsaya ki duba wannan takardar, wasika ce daga mijin da na sami miki." Ina fatan za ki aje hankalin ki waje daya." Ya sa hannu kasan filon kujera ya dauko amblun, ya mika mata ta amsa jiki ba kwari. Tashi ki je ki karanta, ki yi nazari akai, kafin Allah ya kai mu gobe inji ta bakin ki." Ta mike ta wuce babu wani ishashen kuzari a jikinta. Ameer ta tsurawa ido, ta fashe da kuka. Shi ke nan za'a raba ta da shi. Rayuwa kenan, abinda ya kamata ita da Babansa su ba shi tarbiyar da ta tace Hakan ba zai samu ba ko? Ta tambayi kanta, gocewa ta sake yi da kuka. Can wata zuciya ta ce,"Ba ga Antin ki ba? Ai za ta iya rike miki shi tsakani da Allah. Ta goge hawaye, ta ce,"Haka ne. Na san Antina za ta iya." Ta ci gaba da share hawayen, tana ajiyar zuciya. Ta dauko ambulan din dake gefe ta jujjuya ta, sannan ta farke ta, ta warware ta fara karantawa, "Gaisuwa irin ta addinin Islama. Kafin na ce dake komai, ina mai neman gafarar tarin laifin da na yi miki. Da ace ki na cikin hankalin ki a lokacin da na ke tare da ke a asibiti. Da kin tabbatar da cewa na tuba, na kuma fad'a cikin kaunar ki, son ki ya kama ni, a lokacin da zaman mu tare ya zo k'arshe. SAKI DAYA na yi miki ya ke ma'abociyar hakuri. Amma ki sani, a duk bagun numfashin da zuciya ta za ta yi a duniya, tare da bikon soyayyarki. Da ace zan sake samun wata dama ta auran ki, na yi rantsuwa da wanda ya halicce ni, zan nuna miki za6i na gari Abba yayi miki. A karshe ina addu'ar Allah ya raya mana Ameer, rayuwa mai kyau cikin addinin musulunci. Mai son kiNaseer Iliyas Balarabe! Bata gaskanta idon ta ba, balle ta yarda da abinda ta gani a rubuce. Ta sake maimaitawa. Ta tsaya kasake tana sauke Numfashi. Me ke cikin ranta wanda bata tantance shi ba? Kamar farin ciki ne ya kamata, to me yasa hawaye ke neman kubcewa? ----------------------------------------------------------------------------------------------- Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Gaba daya ta kidime. Ta sake duba takardar bisa sunan mai ita Naseer Iliyas Balarabe! Ta cicci6o Ameer ta rungume shi tana fadin,"Tare za mu koma gidan Babanka! Allah na yafe masa! Da kyar ta sami barcin kirki. Da safe ta tafi gaida Alhjn, tun daga fuskarta ya shaida tana cikin walwala, ba kamar dawowar ta jiya ba. Bayan sun gaisa, ya ce,"Kin ga sak'on? Ta amsa da kai, tana d'an murmushi. Ya dan dago habarta, ya ce,"To yaya? Ya fito bazawarin? Ta fado jikin sa ta kudundune fuska,"Kai Abba! Ya fasje da dariya,"Shi ke nan, na bari, to tashi ki ji." Ta mike ya ce,"Na san anjima zai zo, sai da ba shi da labarin komai, illa Ameer da zai dauka. Za'a ci kwalliya ko? Ta tashi da gudu, ta bar dakin. Ya kama dariya yana kwanciya bisa kujera,"Bebin Abba kenan 'yar albarka.," Karfe 9 da rabi Naseer ya iso gidan su, don gaida iyayen sa kamar yadda ya saba duk ranar asabar da lahadi. Yana shigowa. Malam Balarabe ya hau fada,"Kai menene dalilin kulle wayoyin ka. Alh.Basheer na ta neman ka tun jiya, bai same ka ba? Ya ce,"Uhm.............Ba su da caji ne. Ya ce,"Amma kai k'aryar ka ko hanyar masallaci bata sani ba Idan babu Nepa, ba akwai jenareto ba? Yayi shiru." Watau abin zai dawo ko? Da sauri ya ce,"A'a Abba! Ya ce,"To mike maza! Yana neman ka." Ya mike yana fadin,"Sai na dawo. "Umma ce kadai ta amsa mashi. Ya wuce babu kuzari. ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sha daya yana ofis din Alhj ko zama bai yi ba, yace ya ke can gida ya dauke shi, an riga an gama kimtsa kayansa. Tafe yake kawai, amma ko alama baya son ganin Nusaiba, kar kwadayin dawo da ita ya taso masa. A haka ya iso. Yayi ta maza yayi sallama falon. Ummi ke zaune a falon ta yi masa sannu da zuwa, ya tsugunna ya gaishe ta. Ta kira Mariya, ta ce ta kira Nusaiba, ita kuma ta haye sama abin ta. Yayi zuru a zaune kirjinsa na duka. Mariya ta kawo masa tiran kayan motsa baki. Bai ta6a komai ba, wani lafiyayyen kamshi ya doki hancinsa. Ya ware ido saitin kofa. Zuwa can Nusaiba ta ratso rike da hannun. Ameer. Ya zura masa ido, ashe ma kadan ya gani, kyan Ameer a hoto. Jikin sa ya dauki rawa. Nusaiba ta daki zuciyar sa sosai. Bai daina kallon su ba har suka iso tsakar falon, tayi masa sannu da zuwa. Baki sake ya amsa. Ta zauna ta dubi Ameer ta ce,"Ga Abba." Ya kura mata ido ya ce,"Abba? Ta yi dan murmushi,"Babanka ne, je ka." Ta tura shi ya nufo Naseer. Mikewa yayi ya tarbe shi, ya rungume, "Oyoyo Abba na! Ya jima da shi a kirjin sa, kafin suka zauna, ya dora shi bisa cinyoyinsa, suka bi juna da kallo. Ya ce,"Ka sanni? Ya girgiza kai. Ya ce,"Baba ne. Ka ce Baba inji? Ya ce,"Baba." Ya sumbace shi a dukkan kuncin sa. Sannan ya dubi Nusaiba, suka hada ido, yayi dan murmushi, ya ce,"Kun dawo lafiya? Ta ce,"Lafiya lau, ya su Antina da su Umma? Ya ce,"Lafiyar su lau, sun ce a gaishe ki." Ta ce,"Ina amsawa." Suka yi shiru na dan lokaci, kafin suka sake kallon juna. Kowa yayi murmushi, ya dauke ido. Naseer ya kama yatsun Ameer ya hau kadawa, ya rasa abinda zai ce. Ameer ne ya katse shirun,"Baba, wai tare za mu tafi? Ya tallafo kuncin sa ya ce,"A'a za ka zauna tare da Mama tukuna ko? Ka na so? Ya kada kai,"Ni zan bi ka." Ya kwanto jikin sa ya lafe. Ya k'ara rungume shi, ya dubi Nuasaiba, murmushi kawai take yi kafin ta ce,"Yaro ya san gaskiya." Ya ce,"Wace gaskiya? Ai kyan sa ya zauna tare da ke in rink'a zuwa ina ganin sa." Ta ce,"A gidan wani? Ya 6ata fuska ya ce,"Anan gidan na ke nufi, idan son samu ne, mu kasance yana ganin mu tare kowane lokaci, shi zai taimaka ya san mu ne iyayen sa. Ta dan kada kai,"To ai kuma ba zama na zo yi ba gidan. Matsalar kenan." Ya sauke numfashi yayi shiru, ba don shi da abin fadi ba. Ta ci gaba da cewa,"Yanzu za ku tafi a fito da kayayyakin?? Ya dan kalle ta, kin kosa ne mu tafi? Ban ce ba, ayi hakuri." Haka hirar ta ci gaba su kamo nan, su kamo can, alamun babu natsuwa a tattare da Naseer. Sun sami awa 2 tare. Ya kwaso kayan Ameer ya taho da shi, hankalin sa tashe. A Zariya kowa na murnar ganin Ameer, shi ta shi ragaggiya ce, sbd zullumin
Chapter 23 · 0% Book details