Sashe 27
A Jininsa Yake Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajinisa Yake3-06 Posted by ANaM Dorayi on 12:04 PM, 25-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______ Suka yi farin ciki. Ta lallatsa ta nemo lambar Naseer. Suna gaisuwa, kudinta suka kare. Tir! Haushi ya kama ta, sai ga shi ya kira,"Menene Umma? Ta ce,"Ka yi Da. Nusaiba ta haihu yanzu." Farin ciki kamar yayi tsuntsu ya baro Ingila." Ina take Umma? Ta ce,"Ai tana ciki ba su riga sun fito da su ba, amma sun ce lafiya kalau suke ita da Bebin." Alhamdu-lillah! Allah ya amfana mana." Ta ce,"Amin. Haka ya kasance cikin doki, kamar yadda Zarah ke makaranta cikin zakuwa da son ta koma wajen Nusaiba. Kafin yamma gidan su ya cika da baki 'yan barka, angon karni kuwa ya ki barin mai jego sakat da waya, shi so yake ji kukan Bebi, "Bebi kuma ya ki yin kukan. Barcin sa kawai yake kwasa. Ranar suna, yaro ya ci sunan Alhj. Haka kuwa suke kiran sa(Alhaji) Ya ci gaba da girma tamkar Ameer, shi yasa idan Naseer ya rufe ido, baya ganin kowa illah 'ya'yan sa, tamakar 'yan 2. Watanni 3 bayan haihuwar ta. Alh.Basheer zai tafi harkokinsa Turai, ya wuce wa Naseer da hotunan dan sa, ya gan shi. Hankalinsa ya kwanta. Ya cire na Ameer daga firem ya zira wanda suke su 2. An ci gaba, renan Naseer Jah-Jah. Shi kansa yana mamakin kansa. ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Kwanci tashi, shekara ta zagayo. Naseer ya dawo cikin iyalansa, kamar yadda yake so. Bayan ya huta sati 1. Alhj ya kira shi suka tafi bargar dawakansa. Abin ya ba shi mamaki, irin dawakan da ya gani suna harbin iska. Sake da baki ya dubi Alhj yace "Abba za'a fara wasa ne? Ya dafa shi ya ce,"Haka na ke zato, idan na sami amincewar Jah-Jah." Bakin sa har kunne ya ce,"Abba in dora sirdi in hau? Yayi murmushi ,"Why not." Ya kira mai kula da wajen, ya ce,"Je kawo sirdi." Nan da nan ya dora Naseer ya haye jikin sa na rawa ya zagaye bargar dawakan. Kamar kar ya sauka, dokin yayi masa dadi." Abba yaushe za'a fara? Ya ce,"Yau da yamma za'a fara a tisaye, sannan akwai club guda 3 da na ba takardar gayyata wasan sada zumunci. DABAI ta dawo sabuwa." Ya ce,"Insha- Allah kuma gagara gasar masu gasa." Ya kamo shi suka nufo mota yana fadin,"Akwai wani kokari da na ke maka, amma ba zan gaya maka ko menene ba, sai Allah ya tabbatar da abin, za ka ji. Ka ci gaba da addu'a. Allah za6a mafi alkhairi." Ya dan rankwafa ya ce,"To Abba, na gode. Allah ya saka da alkhairi." Wasa ya kankama. (DABAI RIDERS) ta dawo duniyar tseran Polo. Tutar Naseer Jah-Jah ta yi sama ta neman ta wuce yadda take da can baya. Watannin 9 yana ketawa cikin kungiyoyin Polo, yana ba su mamaki. Kwatsam! Abinda Alhj ke masa kokari ya samu. Ba wani abuba ne, illa samun shiga shaharrariyar kungiyar wasan Polo ta kasar Potugal. Naseer fa kamar yayi hauka, don murna. Haka Malam Balarabe, bai san abinda zai ce da Alh.Basheer ba. Kamar yadda aka bukace shi, daya iso 15 ga wata, haka yayi sallama da kowa suka tafi tare da Alhjn. Sun gwada shi, sun ga iya kwarewar sa a zahiri ko dama Alhj ya sha kai masu SD filet din wasaninsa na gida da waje. Kwarai sun gamsu da wasan Naseer, kuma da alamun za'a samu da shi. Can Alhj ya baro shi yana fafatawa cikin turawa. A lokacin ne ya k'ara tabbatar cewa komai in ka na da ilimi ya fi tafiya dai-dai, musamman a wannan zamani. An bashi gida da motar hawa. Naseer ya kasance ba shi da wata matsala sai ta kewar iyalan sa. Ita ma sun kusa magance ta. Cikin watanni 2 takardun zamansa dindin a Potugal suka kamala, ya sami izinin shigowa da iyalansa. Babu son kai. Zarah ce ta fara zuwa a matsayin ta, ta babba. Ameer yayi kukan son biyo ta, amma ina makaranta, ta hana. Wai! Wa ya gane min Zarah a Potugal? Ta shakata kwarai tsawon wata 1, ta koma Nusaiba ta damk'o hanya. Haka suka kasance suna yi wata guda-guda babu matsala balle tashin hankali. Kowacce ta zo Naseer yana jin dadin kasancewar tare da ita, bisa adalci da tsoron Allah. ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Shekara 5 Naseer yayi karfi sosai a k'asar Potugal a fagen tseren Polo. Yayi farin jini kwarai da gaske, kowa na son shi. Sau da yawa wasu kungiyoyin na kawo masa cafka ta hanyar ninka masa abinda yake samu, amma ya kauda kai, saboda Alh.Basheer. Domin a halin yanzu arziki sai dai ya ba wani, bai ma san iya wadanda suke cin gajiyar sa ba a gida Najeriya. Duk shekara idan ya je hutu. Bayan dawowa ba tare daya buda wata cibiyar siye da siyarwa ya zuba matasa sun samun abinci ba. Hatta Naseer B dan hassada, ya saduda ya nemi gafara, ya dawo yana cin arzikin da Allah yayi wa Naseer. Yayi farin jini ba na wasa ba a Potugal, domin har tallace-tallace yake wa manyan kamafoni ta hanyar sana'arsa. Ba kananan dololi yake kamawa ba, kowacce talla yayi. A 'yan shekarun nan biyar. Nusaiba ta hada 'ya'yanta 4 a gidan Naseer, 2 maza, 2 mata. Hakika hankalin Naseer a kwance yake, kuma Alhj ya lura karfi sosai a club din sa, tseren dawaki sai dai ya ba 'yan baya tirenin. Saboda haka yayi iya yin sa wajen Injiniya Ahmad Kaita ta hannun sa ya samar masa a aikin yi ta 6angaran karatun da yayi, don kar ya tafi a banza. Allah mai ko! Takarda kawai aka ba Naseer ya je inta-biyu ofishin(Internet Globl Services) reshen Potugal, take nan suka yarda da takardunsa. Ya sami shiga aiki. Duk da haka bai bar Polo ba, amma ya zama na manya, wanda ake son tafiya da shi, musamman a gagarumin wasan duniya. A farkon wannan watan Zarah ce ke da zuwa Potugal, a filin jirgi ya je ya dauko ta. Suka shiga harkokin su kamar yadda suka saba. Zarah na nason ziyartar Singafo da Malesiya, don haka washe gari suka wuce suka kwana 4. Kwana bibbiyu a kowace k'asa. Sun ci gaba da hutawa a Potugal. Sati 2 dai-dai da zuwanta, ciwon ciki mai tsananin gaske ya murda. Zarah kamar ba za ta yi rai ba. Naseer ya gaggauta kai ta asibiti. Babu 6ata lokaci ta ga Likita ya bata kwararrran bincike. Allah da iko tare da yin yadda yaso. Wai Zarah ciki gare ta na sati 2 a wajen mahifa. Naseer yayi wa Likitan ta bayanin matsalarta. Nan da nan aka buda bakin mahaifa aka maida cikin mazaunin sa. Ta sami kulawa sosai a asibitin har ta wartsake. Yayin da Naseer tuni yayi waya gida, ya shaida masu halin da ake ciki. Kowa ya sha mamaki. Shi yasa tana murmurewa ta fara amsa wayayinsa masu gaishe ta, musamman Nusaiba da ta kan bugu sau 3 zuwa 4 a rana. Mafarin zamanta a Potugal kenan tana samun taimakon daya kamata. Anyi wa yara hutu. Nusaiba ta aje su wajen Umma, ta zo duba Antinta, sati 2 ta koma gida. Sannu a hankali cikinta ya wuce wata 7, ya shiga na 8 kuma Bebi lafiya lau, kowa na ta murna, musamman Naseer da yake tausaya wa Zarah. Rashin da, ga ta ita ma ita kadai wajen iyayen ta. Satin da za ta shiga wata na 9, jini ya goce kamar famfo. Da kyar suka tsaida jinin suka shiga binciken mai ya kawo hakan. Ai da gudu Likita yasa aka gara ta tiyata, bai yi bayanin komai ba, sai da ya ciro k'aton Bebin namji, sannan yayi mata duk abinda ya ga ya dace, don tsira da lafiyar ta. Daga Bisani ya kira Naseer ofishinsa yake gaya masa matsalar da Zarah ta samu. Mahaifarta ta fashe gaba daya, wanda dole ya kasance ya fitar da ita baki daya, hakan shine wajibi a gare ta, don zaman lafiyar ta. Kuka ne kadai Naseer bai yi ba, amma ilahirin hankalinsa ya tashi. Gani yake yi kamar ma cire mahaifar, zai iya jawo mata wata matsalar, sai da likita yayi masa bayani sosai, sannan ya gamsu. Yayi addu'ar Allah ya k'ara mata lafiya, ya kuma bar mata abinda aka samu, ita ma ta rink'a ganin abin ta. Ko gida Najeriya hankalin su ba kwance yake ba, duk Nusaiba ta k'osa a kammala mata biza ta tafi. Bayan kwana 3 kuwa ta isa Potugal. Antin tana a kwamce, duk ta rame ta dushe, bata san lkcn da ta fara zubda hawaye ba. Ga Bebi kato, gwanin sha'awa kuma duk 'ya'yan Naseer da shi suke kama, har matan. Nan ta zauna tare da Bebi (Aliyu), zuwa lkcn da Zarah ta yi sarai, tsawon kwana 12 a asibiti, kafin Likita ya bata sallama suka dawo gida. Sai da Zarah ta yi 40, ita da Aliyunta, sai k'ara murjewa suke, ita dai Zarah ta ki sakin jinkinta dashi, gani take kamar shi ma mutuwar zai yi. Sun dawo gida Najeriya yana da kwana 45, gaba dayan su da Naseer. Gagarumar walima ya shirya, bata wasa ba, 'yan uwa da abokan arziki suka taru, aka taya juna murnar samun Aliyu tare da fatan Allah ya raya shi cikin danginsa, rayuwar Islama. Sati 1 Naseer yayi ya dawo Potugal. Tun Zaran na fidda rai da Aliyu, tana ganin yau zai mutu ko gobe har ta zo ta saki jikinta, zuciyar ta ta zauna waje daya ta daina ba Aliyu mutuwa. Watansa 9 kenan yayi girman mamaki, da kan shi yake mikewa tsaye, yana nema cira k'afa yayi tafiya. Yana kuwa shan ja wajen 'yan uwan sa suna son yayi tafiya dole. Rayuwar su mai dadi suke sha, tare da abokan huldar shi, domin a halin yanzu Sageer yana lakcarin a nan (State Poly) da yaransa 3. Kausar na da 2. Zumunxin su kodayaushe k'ara k'arfi yake tare da k'aruwar arziki.