Sashe 24
A Jininsa Yake Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sun kusa rabuwa da Nusaiba kwata-kwata sai wata k'addara za ta hado su Shi yasa kodayaushe yana Kaduna tare da Ameer wai yana kawo mata shi ne ta gan shi. Dariya take yi, ta ce ta gode." ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sati 2 suka wuce Naseer na lilo tsakanin Kaduna da Zariya. A yau da la'asar ya isa bayan barin sa makaranta ya sa Ameer a mota suka zo. Suna tare da Nusaiba a waje suna shan iska. Alh.Basheer ya dawo, Naseer ya nufe shi suka gaisa daga nan Alhjn ya ce,"Yauwa tunda ga ka, shi kenan sai ka kai wa Malam Balarabe katin daurin auran Kanwar ta ka, wani satin." Naseer ya dask'are nan, har Alhj ya dauko jakar sa a mota ya buda, ya debo katuna." Ungo guda 10 ka ba shi. Haka kuma ga na ka nan, in za ka ba Friend din ka ne, in ba ka Twenty? Kamar ya ce,"A'a." Sai wata zuciya ta hana shi, ya ce,"Toh Alhj." Ya mika masa guda 30. Yasa hannu ya kar6a. Bayan sun yi sallama da Alhj, ya wuce ciki gida, ran sa 6ace, ya koma gun Nusaiba,"Me za ki 6oye min? Ashe Next week ne auran ki shine ko ki gaya min? Ni na isa in hana ne? Baki sake ta ce,"Shirin gaya maka na ke yi, sai Abba ya dawo ka tashi. Ayi hakuri. Ya suri Ameer,"Mu mun tafi. Allah ya bada zaman lafiya." Ya wuce ya bar ta zaune tana masa dariya. Yana zuwa, ya watsa katuna bayan mota, suka tafi. Iya wuya yake yau. Duk wanda ya ta6a shi, zai ji masifa, gida ya wuce da katunan bai kai wa Abba na shi ba. Yana zaune. Zarah da Ameer kadai ke hidimarsu cikin gidan Baya ko fahimce shi ba, suna kici ita da dan lelwn ta, suna girki. Yayi nisa a tunanin sa, kamar ya hadiye zuciya, don haushi. Me zai ci da katuna, banda ya banka wa 'yan iska wuta? Ya zabura a fusace ya fado kicin, babu magana ya hau bincike, ya 6aro mata da kayan cikin dirowar sama. Tayi tsaue tana fadi,"Yayana me ka ke nema? Ashana." Ta ga ya dauka, yai waje. Ta jefar da ludayi, ta biyo shi,"Yayana me za ka yi da ashana? Ya buda mota ya kwaso katuna, ya aje k'asa. Kafin ya kyasta ashanar ta kwashe su. Ya kama da karfin yana fadi,"Ki saki na ce ko? Ta dade bata yi auran ba, idan har sai mun je masu daurin aure! Ya fizzge iya rabon sa, ya watsar kasa, ya kyasta ashana. Ya cinna, yayin da Zarah ta buda ambulan, don ganin takardun da yake rawar jikin konawa? Kati ta gani ta zaro shi ta karanta. Dada masa duka ta yi a tsakar baya, yana duke yana cinna wuta, ta fadi da karfi,"Kai yaya na da kai ne! Duba ka gani,"Naseer Iliyas Balarabe aka sa! Ya mike ya fige katin a hannun ta, ya karanta. Gaba daya jikinsa yayi la'asar, ya zura mata ido, sannan ya dafe goshi, duk kunya ta kama shi. Ta ce,"Komai ba ka bincike, sai ka yanke hukunci." Ya rungumo ta, hayaki yayi sama, ta ce,"Ga dai sauran nan na cin wuta." Ya sake ta ya hau tsalle yana kashewa, tana masa dariya, duk da haka wasu sun k'one, wasu kuma sun yi dameji. Ya kwaso yana nuna mata,"Ni yanzu yaya zan yi? Katunan nan har da Abba? Ta yamutsa fuska, ta dubi Ameer dake tsaye gefenta, ta ce,"Mu ina ruwanmu ko sweetyna? Ya amsa da kai, yana dariya. Ta mik'a masa hannu,"Come on give me five! Ya bata hannu, suka kashe. Ta sure shi, ta ce,"Zo mu tafi abin mu, kar abincin mu ya kone. Baban ka ya zare! Ya kawo mata wawura, ta kwasa da gudu. T-shirt da wandon dake jikin ta ya bata damar gudu sosai. Ameer dariya yake yana murna. Kicin ya iske su suna ta yi masa dariya."Don Allah ki aje girkin nan, ki zo ki raka ni." Ta kama k'ugu, ta tambayi Ameer,,"Mu muka ce ya konawa Abba kati? Ya girgiza kai,"A'a, ta dube shi ta nuna shi da ludayi,"Ka ji ko? Saboda haka ba ruwan mu." Ya matso ya manne da jikinta,"Don Allah ki daina wasa, ki zo mu tafi."Ta k'are masa kallo kafin ta ce,"Jira ni ina zuwa." Ya sumbace ta, saboda Ameer yayi waje. Ta sauke numfashi, ta ce,"Allah na gode maka amarya za ta dawo." Ta sauke girki ta kashe (Cooker), ko dama sitiyu ce, ta rage mata. Daki ta je ta dora (After dress) akan kayan jikin ta, ta yafo mayanin ta fito, ta kulle gida. Ta same su a mota. Suka tafi Ameer na bisa cinyoyin ta. Shi kuwa waya ya dauko ya kira Sageer a Bauchi."Banza, ka na can za'a sha shagali! Shagalin me? Amaryar Zarah za ta dawo." Ah haba don Allah? Komai yayi dai-dai kenan." Ya ce,"Walllahi ni ban ma san Abban na ta ya hakura ba, kati kawai ya ba ni dazu." Cikin murna ya ce,"Congrats. Insha Allahu zan zo a daura da ni, wannan dole ne. Yaushe ne? Next week,"Ai kuwa zan zo da yardar Allah." Suka yi sallama ya aje waya. Ya dubi Zarah,"Ya ce, yana gaishe ki." Ina ansawa. Amma ba ka gaya masa ka zare ba, har ka kona katunan." Ya dunkule hannu ya dora bisa kuncinta. Allah zan kwashe miki hakora, ki kiyaye ni! ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Ya kuwa kama, ya danna masa cizo, ya janye da sauri yana dariya. Su ma suna yi masa. Ya shafa kan Ameer ya ce,"Ta koya ma mugunta ko? Ya lafe a kirjin ta, suka kwakume juna. Naseer ya sha mamaki da suka kai wa su Abba ragowar katin da suka rage masu kyau guda 15. Malam Balarabe ya ce idan ya na son k'ari ya zo ya ba shi. Kunshi 1 ya fito da su, wani samfu daban kuma bugun Malam Balarabe. Abin ya daure wa Nasrr kai, ya ce,"Ni fa ban gane ba? Umma ta ce,"Ai ba za ka gane ba, domin Abbanka da Alhj sun barka cikin duhu. Amma tun ranar da ka zo da Ameer gidan nan. Alhjn ya gaya wa Malam cewaR Nusaiba za ta dawo." Ya shagwa6e fuska,"Saboda Allah ya za'a min haka? Da na mutu fa kafin lokacin saboda damuwa? Zarah ta ce,"Sai a rufe ka mu ci sadaka. Ya harare ta. Umma na fadin, gaya masa dai Zarah. Take nan ta ba su labarin abinda yayi dazu. Me za su yi ba dariya ba. Koda ya je Kaduna dariya suka rinka yi masa, musamman Nusaiba. Shirye- shirye ya kankama. Da yawa mutane ba sun san Nusaiba bata gidan Naseer ba, sai da suka sake ganin kati, musamman jama'ar Alhj. Ranar juma'a da daddare Sageer ya iso, don haka da shi aka daura aure. Washe gari karfe 1 da rabi na rana. Antin Jordan ta dubi Naseer ta ce,"Lalai kai mai sa'a ne, ka yi wa Allah godiya, domin yayi maka baiwa." Ya sunkuyar da kai,"Na gode Anti." Ya wuce ta bi shi da kallo. Ibrahim ya fado mata, tausayin sa ya kamata. Ranar daya zo Injinya na masa bayanin hukuncin da Alhj ya yanke har ya bar wajen, fadi yake,"Ai dama na san Abba baya so na. Wannan karon ma har da Nusaiba, tunda ta iya barin k'asar nan, ba tare da sani na ba." Ta girgiza kai, ta ce a ranta,"Matar mutum kabarin sa." A ranar Nusaiba ta tare su Kausar suka rako ta. Suna shigowa Zarah ta kar6e ta, suka rungume juna, ta kamo ta zuwa sashinta. Kausar na ta fama da tsohin cikin ta, ta ya6e bakin gado. Naseer ya shigo, bayan sun gama cin abincin, suna shirin komawa. Ya ce,"To ga motar can sun shawo man sun dawo." Kausar ta ce,"Na ga ka na rawar jiki ne Jah-Jah, sai wani korarmu ka ke, ni fa ina nan an sai jibi zan koma." Ya ce,"Ga Jah-Jah nan a gaban ki, kin yi wani turus, in za ki kai jibin? Aka kwashe da dariya. Ta ce,"Anan gidan kuwa." Ya ce,"Ina, taso maza in lalla6a ki in sa a mota, kar ki caza min aiki. Ina angwancina, ace in taso asibiti zan kai ki." Ta ce,"Gaskiya ne, ba laifin ka ba ne, tana ji ta yi shiru, shi yasa ka ke kara fadi. Ta na shiru. Antin Jordan ta shigo. "Kausar cicci6o mana, sai da nace ki yi zaman ki gida, ki ka ki." Simi-simi Naseer ya fice. Kausar ta ce,"Ya ka tsere? Dawo mana mu ci gaba. Ka na Angwanci ko? Ya waigo a bakin kofa, ya amsa da kai, ya wuce yana dariya. Duk an watse. Kowa ya koma muhalinsa. Ba ango kadai ba, hatta Ameer yana murnar ganin Maman sa a cikin gidan, yayi ta tsalle-tsallensa ya bi can, ya bi nan. Amma yana cin abinci. Zarah ta yi masa wanka, gadon ta ya haye yayi barcin, bai nemi Maman sa ba. Tana zaune misalin 9, nazarin litattafanta take yi. Naseer ya shigo. Ta dube shi tana. Murmushi,"Ango kenan. Kamshin nan yayi Wallahi." Ya tsugunna ya dada mata duka a baya,"Ba kya ji ko? Ta ce,"Na kai ka rashin ji? Ya ciji kunnanta, ta shafi wajen, ta ce,"Amarya na jiran ka, tashi mu je in raka ka." Ta aje littafi ta kamo hannun sa, ya mike ya rungumo kafadar ta, suka fito zuwa sashin amrya. Ta turo kafar tare da sallama ta shiga. Amarya ta sha ado, sai wanda ya gani. Zarah ta ce,"Kai amarya, ai sai yayan mu ya mance sunansa." Ta sunkuyar da kai,"Antina kin dame ni tun dazu." Ta ce,"To babu ruwana, ga shi nan na kawo shi amana, gobe in an ga ya susuce, ke ce." Ta kama baki tana 'yar dariya. Ya kamo kunnanta,"Shi yasa nace ba kya jin, zo ki wuce." Yana rike da kunnan ya kai ta kofa, suna dariya. Ta tsaya ta ce,"Amarya ya kore ni, sai da safe kenan."Ita