← Book details A Jininsa Yake Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 28

Sashe 4

A Jininsa Yake Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ya tuna da bayanin Likita kuwa, hawaye yake zubdawa sosai, domin ya tabbata shi ya tara maya damuwar sa ta jefa ta wannan mawuyacin halin.A haka so da k'aunar Nusaiba suka zauna kwarai da gaske cikin zuciyarsa, har yana mamakin kan sa." ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi Kwanan ta 11 yau, ya gama kintsa Ameer, ya kwantar da shi cikin (Net) din sa. Ya dube ta, tana ta lissafin zucci, ya ce,"Za ki sha Tin ne kafin ki kwanta? Ta ce,"Had'o Abba." Ya had'o mata dai-dai wanda ta saba sha. Ya zo da shi bakin gadon, ya zauna. Ya debo a cokali ya ce,"Ungo, sha 'yar gidan Abbanta." Ta dube shi, tayi murmushi," Miss you."Dariya ta ba shi, ya ce"Za ki fara ko? Ai ni fushi na ke da ke."Me na yi Abba na? Ya mika mata, ta kur6e ya ce,"Batan kin kori kowa, mutane na son ganin ki, amma kin hana, me yasa? Hmm... Abba na kullum ina raba ka, amma ba ka ji. Me za'ayi da munafukai? Ya ce,"Na fa hana ki ce musu munafukai. Haka dazu ki ka cewa Umma, sa'ar ki ce? Ta dan 6ata rai, tayi shiru, ya miko mata Tea ta ki kar6a. Ya aje cokali ya dago ha6arta."Fushi ki ka yi? Da ni ki ke fushi, shi kenan bari in zo in tafi." Ta ce,"Yanzu saboda Allah Abba duk wanda ya nuna baya so na, ba munafiki bane? Yanzu dubi yadda ka ke k'aunar Naseer, amma k'iri-k'iri ya nuna min, baya so na, yayi ta wulakanta ni. Saboda Allah Abba me zan kira shi ba munafiki ba, tunda ya munafunce ka." Tunda ta soma mgn, gabn sa ya yanke ya fad'i, yayi sukuiti duk jikin sa ya mutu, ya rasa me zai ce? Ta zura masa ido, ta ci ga,"Abba ai dai ka san na maka biyayya da ka ce min shi ka za6a min, ban maka musu ba ko, Amma ka san Allah, shi baya so na, wannan cikin na jiki na ma, ya ce da shi zan koma gidanmu, baya so. Na ce ai ban je da d'a gidan sa ba, ko fan fadi gaskiya ba? Hankalin Naseer fa ya yi mummunan tashi, ya tabbata wata rana a surutanta za ta iya fadi a gaban kowa. Idanunwan suka kad'a, ya aje Tea bisa dirowa ya rufe.Ya kamo kafadunta 2, suka yi wa juna zuru kafin ya ce,"Wannan maganar bata dace ki na fadar ta ba 'yar gidan Abbanta. Naseer masoyin ki ne, ni ya gaya min yana son ki kwarai da gaske." Ta girgiza kai,"Na rantse da girman Allah, karya yake maka Abba. Naseer munafiki ne, ina gaya maka maganar nan, ka yarda da ni Abba." Ya sake ta ya kama kai. Ta bi shi da kallo ta ce,"Mamaki ma ka ke yi? Kai har yanzu ba ka san mutane ba, ka na dai kallo aka kashe Antina, me za'ayi? Yayi hucin zafi ya ce,"Duk na ji, amma kin san abinda na ke son ki da shi ? Ki kyale maganar nan, kar ki gaya wa kowa, ni zan yi maganin abin. Kin yarda? "ka dai gaya masa, idan na haihu zan aje Yaron, shi zai maida shi cikin lemon gwangw........................ Ya like bakinta,"Nusaiba na ce ki bar maganar nan, zan fa tafi abi na." Ta ce,"Yi hakuri." To kin yarda ba za ki gaya wa kowa ba? Na yarda, amma ka san Allah, ka yi hankali da wad'annan mahaukatan da suke zuwa 6arayi ne." Yayi shiru yana kallonta, duk ta dagula masa lissafi." Ba ni Tin mana." Ya dauko ya ci gaba da bata, sai zuba masa surutu take, shi kuwa bakin sa ya mutu har ta yi barci. Yayi tagumi bisa kujera, ya rasa abinda ke masa dadi.Ta dai ce ta yarda ne kawai, ba za ta sake fadi ba, amma abin maras hankali, ai ba'a sirri da shi. Dan saukin ta ma, bata kula kowa sai shi. Daran nan bai runtsa ba saboda tunani. Safiyar yau kuma daga ya ce, bude baki ayi burosh, shi ke nan ta fasa kuka. Yayi rarrashin dunuya, ta k'i yin shiru, ta k'i kuma mgn, a haka ta shafe sama da mintu 30 ita da kan ta ta yi shiru. Ta gyara kwanciya, ya sanya mata ido, tana ta ajiyar zuciya, har barci ya sace ta. A lokacin shi kuma ya fara na shi hawayen da kyar ya iya tsaida su, saboda tsabar tausayinta. Ko me yasa ta kuka? Oho! Ya tambayi kan sa, ya ba kan sa amsa. Idanuwan sa suka kara ja, kamar garwashin wuta, dama ga rashin barcin da bai yi ba jiya. Yana nan zaune zuru, ya ji motsin Ameer, shi ma ya farka. Ya tashi ya zuba masa ruwan dimi a fida ya zuba glucose ya karkada, sannan ya dauko shi suka fito waje, ya zauna a kujera yana ba shi har ya shanye. Idon sa 2, amma baya kuka, yana ta 'yan wasannin sa. Naseer na taya shi. Muryar Alhj kawai ya ji yana masa sallama, ya dago da sauri yana amsawa. Tare suke da Ummi da Antin Jordan. Ya mike yana masu sannu da zuwa. AntIn Jordan ta kar6i Bebi tana fadin,"Sannu Naseer, don kai ne abin gaisarwa. Yaro duk ya rame." Yana murmushi ya tsugunna, ya gaishe su.Alhj ya ce,"Mutuniyar barci ta ke yi ne? Ya ce,"Eh. Ummi ta ce,"Yauwa mun yi sa'a, shigo Fatima ki gan ta."Suka dungoma cikin dakin, shiru suka yi suna kallon ta kawai, don kar su yi surutu ta farka. Sun kusa minti 10 a tsaye, sannan suka fito dan koridon. Naseer ya baza darduma, suka zazzauna. Ya koma gefe ya zauna, suka ci gaba da tambayar sa yanayin jikin na ta? Ya ce,"Da sauki, an gode Allah, amma ko dazu ta sha kuka, kuma ta k'i magana, abinda ma ya sa ta barci ke nan." Antin Jordan ta goge kwalla, ta dubi Alhj,"Gaskiya yaya idan babu wani ci gaba a fita da ita waje kawai." Ya ce,"Wannan maganar na rai na, akwai iiya kwanakin da na dibarwa Likitocin nan din ne, idan sungaza, zan dauke ta." Ta ce,"Wannan tashin hankali da yawa yake." Ya ce,"Jarabci ne, mun gode Allah, muna rok'onsa sauki. Kai Naseer ka yi ta hakuri, ka ji? Ya ce,"Hak'uri na mu ne duka Abba." Haka suka kasance tare, jama'a na ta zuwa kamar kullum. Koda ta farka. Naseer ne kawai ya shiga, ya kai mata Bebi. Allah da ikon sa babu kuka, sai hira kamar ma ba ita ta sharari kukan dazu ba. Yayi mata burosh, ya bata Tea, ta sha. Abin yana ta 6a Antin Jordan mmk har ta tambaya,"Yanzu ina shiga, sai ta fara Ihu?, Ummi ta ce,"Ko za ki gwada ne? "Don daukan alhaki? Na gan ta ta taga, ya isa. Allah ya yaye mata." Ta ce,"Amin. Kwananta 7 ta koma Jordan. Ranar da ta tafi, ranar Kausar ta iso da mijinta. Bata 6ata lokaci ba, ta fadawa dakin, kanta ta yi ta rungume ta sa kuka. Wani ihun da Nusaiba ta yi, dole ta sake ta, tana kallo, jiki na rawa. Ta runtse ido, tana zagi tana fadin. "Ban son ganin su. Ban son ganin su! Naseer ya rirrike ta. Mijin Kausar ya fito da ita, me za ta yi ba kuka ba. Haka ta fada jikin Ummi, tayi ma isar ta. Naseer kuwa da kyar ya shawo kan Nusaiba tayi shiru, ta daina zage-zage. Ba karamin Huashi Kausar ta bata ba, sbd ta6a tan da tayi.Yini guda masifar da ta rink'a yi kenan,"Wata munafuka ta zo ta cakume ni za ta kashe ni! Sai bayan la'asar tayi barci. Kausar ta je gun ta, tayi mata addu'o'i. Hawaye na zuba. Da yamma lilis suka koma Kaduna. Haka Kausar ta tafi da bak'in ciki, a duk lkcn da ta tuna hawaye, ke zubar mata. (Allah sarki Nusaiba
Chapter 4 · 0% Book details