← Book details A Jininsa Yake Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 28

Sashe 25

A Jininsa Yake Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

dai ta kasa magana, sai dariya. Zarah ta ja kofa." ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Ya tsaya ya k'are mata kallo, sannan ya sauke numfashi. Ya tako a hankali ya tsugunna gabanta, suka dubi juna, ta dan kauda kai, tana murmushi. A natse ya kwantar da kan sa bisa kafafuwanta, ya nisa yayi dan shiru. Haka ita ma take kallon sa idanuwanta suka kawo kwalla. Bata san lkcn da ta dora kan ta bisa bayan sa ba. Sun jima shiru haka kafin ya ce,"Na gode Allah, na sake gode masa daya nuna min wannan rana. Haka kuma na gode wa Abba daya sake mallaka min ke. Na yi kuskure gare ki Nusaiba wanda baya misaltuwa, ba na kuma son tuna su. Ki yafe min Nusaiba. Ta ce,"Tuntuni na yafe maka yayanmu. Ya wuce." Ya dago ya ce,"Na gode." Kin san wani abu? Ta kada kai. Ya lalibo aljihunsa ya dauko kudi, ya kamo hannun ta ya dora mata, ta ce "Na menene? Kudin ki ne, canjin ki dubu 15 da ki ka ba ni a asibiti. Ta saki baki tana kallon sa,"Kai yayanmu, shekara 2 da rabi? Ya sake kwantar da kan sa, ya ce,"Ba zan ta6a mancewa da su ba Nusaiba, domin daga ranar da ki ka miko min su. Allah ya manna min son ki a raina. A lkcn ba wai ba ni da su ba ne, amma ba su da amfani, tunda ban san yadda zan yi in ciro su ba. Alhalin ina matukar bukatar su. Da gaggawa. Kin min abinda ba zan ta6a mancewa da ke ba rayuwa, kin taimake ni a lkcn da na wulak'anta ki na.......... Ta rufe bakin sa."Na ce ya wuce yayan mu, ka daina tunawa." Ya dube ta ido cike da kwalla,"Kar ki yi kokwanto Nusaba, Ina son ki! Ina son ki!! Ina son ki Nusaiba!!! Ta ce ,"Na sani." To kice kina so na in ji, ko sau 1 ne." Ta yi dan murmushi ta ce, "Ina son ka yayan mu. Ga kuma kudin ka har canji na bar ma ka." Yahayo shimfidar sosai, ya ce,"Kin saye baki na ke nan? Ta yi 'yar dariya,"Na siya." To me ki ke sha'awar sha? Ta ce,"Uhm.......Cock, irin mai dan inabin nan. Ka gane ai? Ya tsura mata ido, tana masa dariya. ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Zaman lafiya mai ban sha'awa ga kowa ya dore a gidan Naseer. Hankalinsa kwance, ba shi da matsala. Ya k'are Digirinsa. Shine gwarzon shekara, wanda ya fito da ajin farko a fanni da yake karanta, sannan ajin farko cikin jerin wadanda suka zo na farko a sauran kwasa- kwasai a wannan shekara. Don haka yana daya daga cikin masu rubuta jarabawar tantance masu tafiya Turai don karo ilimi tare da tallafin gwamnati. Kowa yayi masa murna. Shi kan sa ganin abin yake kamar a mafarki. Allah yayi gaskiya ya ce tashi in taimake ka. Tabbas hake ne, Naseer ya ga Zahiri. A Kaduna suka rubuta jarabawa 'yan makwanni tsakani sakamo ya fito. Naseer ya haye ya ci Nasarar tafita Ingila. Shirye-shirye ya kankama a lokacin cikin Nusaiba ya fara tsufa, domin kuwa ya shiga wata na 7. Ranar da zai tafi daren kasa barci yayi, saboda tunanin shekara 1 ba zai ga iyalansa ba, wad'anda ya riga ya aje su cikin ransa, baya son kasancewa da kowa sai su. A duk inda yake. Allah.Allah yake ya yi yadawo gida, saboda tsabar son da yake musu. Amma babu yadda zai yi, yana son ci gaba kuma a yanzu ya tauna dadin karatu ya dandana ya gane fa'idar sa. Kan dole ya dake zuciyar sa. Washe gari karfe 8 na dare jirgi ya cilla da su birnin Sarauniya. Sun kama karatu gadan-gadan, amma kodayaushe cikin waya suke da iyalansa. A haka watan haihuwar Nusaiba ya tsaya. Umma ta sa ido sosai a kan ta, babu ranar da bata zuwa Hanwa. Allah da ikonsa da safe ta fara nakuda, ga shi Zarah na da jarabawa kuma ta karshe ce, don kammala NCE din ta. Duk da haka ta hada kayan haihuwa ta wuce da Nusaiba asibiti. Sai da ta tabbtar an shiga da ita dakin haihuwa kafin ta kira Umma ta gaya mata asibitin da suke. Nan take Umma ta watsar da abinda take, ta biyo hanya. Tana isowa 8 dai-dai, sannan Zarah ta bar mata Ameer, ta wuce jarabawa, ta iske an shiga, sai da ta sha surutu, ta samu aka ba ta fefar. Da namiji Nusaiba ta sake Haifa, lafiya lau daga ita har Bebin. Umma da Ameer na murna. Nan da nan ta kira wayar Ummi, ta shaida mata ta sake sabon ango.... ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------
Chapter 25 · 0% Book details