← Book details A Jininsa Yake Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 28

Sashe 6

A Jininsa Yake Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajininsa yake 3-02 Posted by ANaM Dorayi on 08:53 PM, 20-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______

Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

To shi kenan ya wuce." Ya kamo ha6ar ta, yi dariya,"Yi dariya 'yar gidan Abba!
Ta fado kirjinsa, tana murmushi.
Ya rungume ta, ya runtse ido, wasu kwalla suka yi masa caa, fadi yake a ransa, "Son ki ya kama ni Nusaiba, ki yafe min don Allah.". (Hhhhhhh, Anzo gurin, ammafaaaa...uhm! Maji ma gani)

Bai ko san ta kici-kicin tashi ba, sai da ya ji tana kira,"Abba!
Ka shake ni!
Ya hanzarta sakin ta, yana goge kwallah. Ta bi shi da kallo,"Wash!
Ka wani matse ni Abba, ai sai in mutu."Ya tashi ya bata wuri, ya shige bayi ba tare da ya ce komai ba.
Jim kadan ya fito, ya wanke fuskarsa, kwance ya same ta, ya matsa gabanta ya ce,"Hirar ta isa haka, ki yi barci ki huta." Ta amsa da ka, ya duk'o ya sumbace ta, ya ja mata mayafi. Ya ja kujera ya zauna, ya sauke numfashi,"Allah ka ga iya kokarin da na ke yi. Allah ka taimake ni yarinyar nan ta sami lafiya.
Ta ce,"Ka kwanta mana Abba." Ya ce,"Zan kwanta, ke dai yi barcin ki." Ta rufe ido.
Tare da gyara kwanciya.
Da asuba ya fito bayi da alwalar sa, ya shimfida sallaya, yayi sallah. Ya jima yana addu'o'i kafin ya jiyo motsin ta.
Ya waigo yana kallon ta, ta tashi zaune, tayi mika tana salati. Ta kalli can, ta kalli nan, bai ce da ita k'ala ba.
Ta k'ura wa Bebin da ke barci cikin (Net) ido.
Ta dago kai ta dube shi, suka yi ido 4.
Yayi murmushi, ya ce,"Kin ta shi?
Fashewa tayi da kuka, ya taso da sauri ya zauna gefen ta."
Nusaiba, ke Nusaiba, za ki fara koke-koken nan ko?
Tayi shiru tana tunaniin Antin ta.
Hawaye na ta ambaliya.
Ya rik'o ta, ta kwace jikin ta, kuka take tana k'arawa.
Ya ce a ran sa,"Na shiga 3, yau kuma da kukan ta tashi." Ya matso, ta matsa. Ya ce,"Ni Nusaiba, ni ki ke gudu? Bata kalle shi ba, balle ta ce wani abu. Ya sake matsowa, ta matsa. Ya ce,"Shi kenan, bari in yi tafiya ta, in tafi ko? Ta amsa eh, da kai. Ya ce,"Tabd'i! Da magana yau,"Cikin ransa.Ya rasa yadda zai yi, dole ya sa mata ido, tayi ta kuka. Can kuma ta tashi ta fito koridon ta zauna, bisa kujera. Shi ma ya biyo ta nan ya zauna, yana gadin ta.
Jim kada ya ji kukan Ameer.
Ya mike ya ce da ita,"Ga Ameer can ya tashi, in kawo shi ya sha? Ta kyale, bai ma ishe ta kallo ba, ya shige ciki ya dauko shi, ya tsugunna gabanta,"Yauwa, 'yar gidan Abbanta kenan, dubi Bebin mu kuka yake yana jin yunwa, dan ba shi ya sha." Ta dauke kai, tamkar bada ita yake magana ba.
Abu fa ya gagara, dole ya dauko wa Ameer fida ya tura masa, yayi ta tsotson ruwa da glucose.
Kullum karfe 7 nan take masu. Alh.Basheer suna nan zaune kuwa, sai ga su.
Naseer ne ya fara hango su, ya mike ya nufo su.
Su ma tsayawa suka yi cak, ganin Nusaiba a zaune wajen.
"Yaya dai? Alh.Basheer ya tambaye shi, yayin da Ummi ta kar6i Ameer a hannun sa.
Ya ce,"Ai yau ko Ameer ta k'i ba shi nono.
Kuka kawai take yi,"Ya ce,"Likita ya zo?
Ya ce,"Ka tsaya nan, kai kuma koma gun ta, bari in nemo Likitan." Ya koma wajen ta.
Alhj ya zaga ya wuce, ita kuwa Ummi ta lafe.
Jimawa kadan suka dawo da Likita. Abin ya ba Naseer mamaki daya ga Lkita ya zo, ya tsaya gabanta bata zage shi ba.
Ya ce,"Nusaiba, tashi mu shiga ciki, mu yi wata magana." Kai tsaye ta mike ta wuce. Naseer ya saki baki, shi ma ya taso ya biyo su. Ta zauna bakin gado, ya jawo kujera ya zauna ya ce,"Kukan me ki ke yi?
Ta ce,"Antina ta mutu ko?Ya ce,"An gaya miki bata mutu ba, Antin ki na gida." Ta runtse ido wasu hawayen suka tsunke mata, ta sa hannu ta share. Ya ce,"An ce kin ki ba Bebin ki nono, saboda me? Haka za muyi da ke saboda Allah? Ta dube shi da kyau ta ce,"Doctor ka yi min wani taimako don Allah, lambar Abba na zan ba, ka kira min shi." Idanuwan Naseer suka k'ara yo waje, ya koma da baya da baya ya fito waje. Shi kuwa Likita k'ara tsura mata ido, ya ce,"Abban ki? Ta ce, eh. Ya ce,"Ina zuwa." Ya leka yayi kiran Alhj da hannu. Ya taso daga inda yake zaune ya zo. Likita ya kamo hannun sa, ya shigo da shi a hankali. Kan ta na duke ya ce,"Wannan Abban naki ki ke nema? Tana yo ido hudu da shi, ta mike hawayenta suka yawaita, ta ce,"Abba! Wani tsananin farin ciki ya kama Alhj, dole kwalla suka cika idon sa, ya ce,"Bebin Abba! Ta rugo da gudu ta rungume shi. Tuni Ummi ta fado dakin ta hade su ta rungume, kuka suke saboda murna. Haka Naseer ke sharar kwalla. Amma ya rasa abinda zuciyar sa ke sakawa game da wannan al'amari. Tabbas Nusaiba ta warke, to me zai biyo baya? Da alamun zai shiga magana, yanayin da ta nuna. Yayi ta maza ya shigo. Alhj Basheer ya rungume shi, suna wa juna barka. Likita ya fita, ya bar su cikin farin ciki da murna maras misaltuwa.Bayan sun natsa. Ummi ta dubeta, duk ta rame ta ce,"Sannu Nusaiba, Ubangiji Allah ya k'ara karewa." Ta ce,"Amin. Ta miko mata Bebi ta ce,"Kin ga Bebin da aka ciro miki? Ta dan dube shi, tayi murmushi , ta dauke ido,"Na gan shi Ummi ta. Kwalla suka taru fal a idonta, ta kasa shanye su, sai da suka zubo. Abban ya rungomu kafadunta, ya ce,"Yi hakuri daina kuka, komai ya wuce Insha-Allah." Ya ce,"Allah ya yarda Abba. Bari in yi sallah." Ta mike ta wuce bayi ta jima bisa sallaya, tana yi wa Allah godiya daya dawo mata da rayuwarta dai-dai. Ta dawo gefen gado ta zauna kusa da Abban ta. Ya jawo ta jikin sa, ta dan numfasa ta ce,"Abba lokaci yayi da zan gaya maka wata magana, ina fatan za ka gafarce ni." Naseer na jin haka, ya mike ya bar dakin. Abba ya ce,"Babu komai Bebina, gaya min, me ke da mun ki? Ummi ta sa masu ido tana kallo. Ta k'ara gyara zama ta ce,"Na san za ka yi mamaki, idan na gaya maka cewa tun aure na da Naseer, babu kwanciyar hankali tsakani na da shi. Ai kuwa Alh ya sha mamaki, ba shi da kadai ba har Ummi da take zaune. Ya kara dubanta, baki sake, ya tambaya, "Saboda me? Ta ce,"Abinda na fahinta,"Abba, shine ya kar6i aure na ne kawai don ka cika masa ido, ba zai iya ce maka a'a ba. Amma a hakakin gaskiya Naseer baya so na, kuma ya nuna min kiyayya, ba don Antyna na tsaye ba, ina ganin wuyar da zan sha, ba 'yar k'arama bace.

Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

Shi yasa na ke son ta, domin tayi min komai, kuma tayi iyakar kokarinta wajen jawo hankalinsa zuwa gare ni, sai dai haka bata samu ba, saboda babu sona a zuciyar sa." Ransa ya 6aci kwarai, ya ce,"Me yasa tuntuni ba ki gaya min ba? Ta ce,"Saboda kai ne Abba. Ba na son wani tashin hankali ya shiga tsakanin ku. Kuma ina ganin ai ya girmama ka ne, tunda ya kasa fitowa fili ya nuna maka baya so na. Shi yasa na yi ta kokarin zama da shi shekara daya da rabi, sai da Allah ya kawo rabon wannan Yaron, sannan ya shiga daki na. Daga baya na yi tunanin bai kamata mu zauna muna cutar da juna ba, shi yana jin haushi na, ni ma ina jin na shi. Sai na same shi a daran da wannan abin zai faru, na yi masa magana. Abba cewa yayi idan na k'ure shi, zai 6atacciya, dole in koma gidan mu, har d'an baya so, ya bar mana...................!!! Tana shiru. Ummi ta cafe,"Ina, inda kuma yayi karya kenan. Ai ba mu kai masa ke da Da ba." Alh.Basheer yayi shiru, zuciyar sa na tafasa, abin kamar a mafarki yake ganin sa, domin ko alama bai ta6a mafarkin Naseer zai ci amanar sa haka ba. Ya dubi Ummi ya ce,"Har hada mata kayan ta mu tafi." Ta mike tana fadin,"Ashe ga damuwar da ta kusan hallaka rayuwarki Nusaiba, kenan. Yayi wa kan sa. Kuma sai Allah yayi miki sakayya." Nusaiba ta kada kai,"Ba haka bane Ummi ta, ba laifin sa bane, kar ki manta soyayya, gamon jini ce, laifin sa 1, shine daya danki amanar da ba zai iya rikewa ba."Alhj ya ce,"Duk laifin iyayen sa............ Tayi saurin katse shi."A'a Abba, iyayen Naseer ba su da laifi kuma ina mai tabbatar maku yadda ya yaudare ku, haka ya yaudare su. Ba su san komai ba a game da zaman mu. Sun rike ni tamkar 'yar cikin su. Idan na ce ga abinda su kai min, na yi masu karya, sai Allah ya tambaye ni. Abba, rokon da zan maka daya ne, don Allah, don son Annabi kar ka k'ullaci kowa akan maganar nan, ni ce baya so, to ka dauki 'yar ka. Ai shikenan, an gama magana." Ya ce,"Haka ne Nusaiba, ki yi hkr, ni ma na gane kuskure na, ni na jawo miki duk abinda ya same ki." Ta ce,"Ban ta6a ba ka laifi ba Abba, ba kuma zan ta6a ba ka ba.
Chapter 6 · 0% Book details