Sashe 2
A Jininsa Yake Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fashe da kuka sosai, irin wanda bai ta6a yinsa a rayuwar sa ba. Ji yayi an kamo shi,"Malam Umar ne,"Haba Naseer, ka yi hkr mana, ka roki Allah ya ba su lafiya. Wannan koke-koken ai ba su da amfani. An san ka na cikin tashin hankali, amma jurewa za ka yi, ka zama namiji. Zo mu je, yanzu za mu tafi, don a samu a bizne jaririyar wajen Zarah. Yi hkr d'an gidan Inna." Ya goge masa fuska, ya riko hannun sa suka dawo. Yarinyar na lullube cikin zani, ya nuna wa Naseer ita, yayi jim, yana kallon ta, sannan ta dauke kai. Ya matsa kusa da Abba ya ce,"Ka zo da waya?" Ya ce,"Ga ta, ai na riga na gaya wa su Alhj, suna tafe." Ya ce,"To shi kenan, bari in kira Sageer." Ya kar6i waya, ya matsa gefe,ya kira duk wanda yake son kira, sannan ya maida wa Abba wayarsa, suka dauki shatan tasi ta maida su gida. Suna bada baya. Su Alh. Basheer na isowa. Abinka da asibitin Shika, sai suka rasa ina za su dosa, don haka ya kira wayar Naseer. Tana ta bugawa, amma da yake tana gida, babu mai dauka. Ya kira ta Abba, su kuma sun riga sun kusa gida, saboda haka Malam Umar yabasu lambar Inna, suka kira. Naseer ya fita ya nemo inda motar su tayi fakin. Yana isa wajen. Ummi ta fara kwalla. Yana neman tsugunnawa. Alhjn yayi sauri ya kamo shi,"Sannu Naseer ya fargaba? Ya ce,"Mun gode Allah." Ya ce,"Malam Balarabe ya ce ashe doguwar suma Zara tayi ko? Ya amsa da kai? Ya dan rungumo kafadar sa,"Ka yi hakuri kaji? Allah zai ba su lafiya." Ya gyada kai, ya dubi Ummi suka gaisa, sannan yayi masu jagora zuwa inda suke, suna tafe yana maida masu yadda abin ya faru. Bayan sun gaisa da su Umma. An jajanta wa juna, sai Alh.Basheer ya nemi ganin Likita. Abn ka ga mai kudi, nan da nan ya sami duk abubuwan daya bukata watau daki na musamman da likita shi ma na musamman. Kan ka ce kwabo, an hada Zarah da Nusaiba waje daya, an zuba masu komai na bukuta. Ummi na rike da Bebi, yana to son a zuba masa abinci a bakin sa. Da yake akwai kayayyakin Zarah, ruwan zafi kuma tana da zuma da dabino sbd tana yawan cin dabino, sai Inna ta kawo, duk Ummi ta ba shi, sannan ta dan kada zuma a ruwan dumi, ta cika masa ciki, nan da nan ya koma barci. Ganin hankali ya dan kwanta. Inna ta ce Naseer ya koma gida yayi wanka, daga nan ya kwaso wa Bevi kaya da ita Nusaiban. Yana fitowa su Sageer na shigowa shi da Fa'iza, dole ya sake komawa, suka gaida su Umma. Ya kawo masu Bebi suka gan shi. Wucewar 'yan mintoci 15 ya karbi mukullin motar Nusaiba, tunda ga Sageer zai tuka a maida ta gida. Sun yi fakin kofar gida, suka yi sallama suka tafi, ba tare da sun tsaya wani surutu ba, domin Naseer baya ma son yin magana. Yana shiga gida, ya tu6e kayan jikin sa, ya zaro sauran kudin da suka rage cikin rafar da Nusaiba ta ba shi. Ya zauna bakin gado ya zura masu ido, jim kadan ya sauke numfashi, ya aje su bisa filo. Ya wuce bayi ya sakarwa kan sa ruwa. Bayan yayi wanka, ya kimtsa ya kawo wayoyinsa da kudade ya zuba aljihu. Ya fito ya nufi dakin Nusaiba. Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi Gaban hoton ta ya tsaya ya k'are mata kalo ba tare da ya san me zuciyar sa ke sakawa ba. Wadirof ya bude, ya d'ebo riga da Zani kala 5r. Yayi tsaye yana tunanin a ina zai ga kayan Bebi, tunda bai ta6a siyowa ya ce mata ga shi ba? Abinda ya yanke shawara shine ya shiga kanti, ya siyo. Wata zuciya kuma ta ce masa "Kai dai dudduba." Yana gama tunanin sa, ya nufi akwatuna ya fara budewa, abn ya ba shi mamaki, domin setin nan kaf kayan Bebi ne ciki a mak'are. Yayi shiru duk al'ajabi ya ishe shi, ya nemo jaka ya debi kaya iya dibar sa, kayan shafe-shafe, su pampas da setin bahon wanka, wanda komai na bukatar wankan Bebi. Akwai shi a ciki. Ya loda kaya a but, ya sallami Abba ya koma asibiti. Yana shigowa da kaya niki-niki, ya iske Zarah ta farfado, sai faman kuka take yi, sbd jin abin daya faru da Nusaiba. Su Umma na ta bata hkr. Ganin Naseer ya shigo, dukkan su suka fita waje.Ya matsa wajen ta ya zauna gefen gadon, da sauri ta fado masa ta sake 6arkewa da kuka. Idanuwan sa suka cike da kwalla, ya kasa cewa uffan tsawon lokaci. Sannan ya dagota, ya share mata hawaye ya ce,"Ya isa haka. Ya jikin? "Yayi sauki. Ashe abinda ya faru kenan? Ya ce,"To yaya za'ayi? Allah ya ba ku lafiya." Kwalla suka sake zubo mata ta ce,"Amin.", Na ga Bebin mu kamar Ameer ne aka dawo mana da shi." Yayi dan murmushi,"Shi ne ma, domin shi ma sunan za'a maida masa." Ta ce,"Yayi dai-dai." Suka k'ura wa Nusaiba ido, a lkc guda kuma suka kalli juna ya ce,"Allah yasaa ita ma ta farfado. Lafiya, kamar yadda ki ka tashi." Ta ce,"Amin yayana." Ta wuce da kanta kirjin sa, tayi ajiyar zuciya, ya sumbaci tsakar kanta, sannan ya gaya mata su Sageer sun zo shi da Fa'iza. Suna gaishe su." Ta dago a hankali ya taimaka mata ta kwanta tana fadin,"Muna amsawa." Ta bi shi d kallo, ta ci gaba da cewa,"Na san ba ka ci komai ba yayana, ka hada Tea mana ka sha." Ya kada kai,"Ban jin yunwa Zarah." Ta ce,"Ai kai ba za ka ji ya ba, amma tana nan tana cin ka." Yayi dan murmushi ya ja ha6arta, ya ce,"Hankalina bai gama kwanciya bane Zarah, sai na ga farfadowar yarinyar nan." Ta dan lumshe ido, ta bude wani dadi ta ji ya ratsa, ta miko yatsun ta, ya rike ta.. Ta ce,"Insha Allahu lafiya lau za ta farfado. Kar ka ka zauna da yunwa yayanmu, za ta iya yi ma illa." Ya sumbaci, yatsun ya ce,"Shi kenan, zan sha yanzu." Umma tayi sallama, ya mike da sauri yana amsawa, ita ma maganar abincin tayi masa, sannan ta bude jakar kayan daya kawo, ta debo wa Yaro kaya, ta dauke shi suka fice. Anan ya hada Tea ya dawo bisa kujera gaban Zarah yana sha, suna hirar Nusaiba. Bayan sallar la'asar. Alh. Basheer ya ce shi zai koma. Ummi ma ta ce me za ta tsaya yi, tunda ga su Umma ga Inna? Haka suka wuce, duk ba su ga farfadowar Nusaiba ba, idan Allah ya kai rai gobe, za su dawo. Bebi kuwa na lkie da Zarah. Naseer ya tasa su yana ta fama kallon abin sa, son sa na k'ara kwarara jikin jinin sa da bargonsa suna kashe jijiyo har bisa fatar sa. Karfe 9n dare ya baro Shika. Zarah tare da Bebi ta kwana, ko ya motsa, ita ake mika wa ruwan dimi ta ba shi, duk da jikin ta babu kwari sosai. Shi kuwa Naseer kasa runtsawa yayi, saboda tsabar tunanin abubuwan daya aikata wa Nusaiba, wadanda a yau yake ganin suna so su zame masa da na sani. Lokacin sallar asubahi ya yi, ya tashi ya je yayi alwala, ya bada farali. Da kansa ya shiga kicin, ya shirya duk abubuwan da yake son tafiya da su asibiti. Yayi wanka, ya kimtsa. Karfe 7 saura kwata, ya dauki hanyar Shika. Karfe 8:30 Nusaiba ta farfado da surutai tare da sambatun da babu wanda yake fahintar me take fadi.Likita ya ce ba damuwa, za ta wartsake nan bada dadewa ba. Suna fa jin dadi, musamman Naseer da zuciyar sa ke cike da zullumi. Ko su Alh.Basheer da suka zo, sun yi farin ciki kwarai, anan suka iske su Malam Balarabe da Malam Umar. Shi yake gaya masu cewa Bebi sunan marigayi watau Iliyas ya ci. Wasa-wasa Nusaiba ta kai har dare bata gane kowa, sai sambatu. Likita dai sai kara basu hakuri yake yi, yana jadadda ma su za ta warware. Amma haka suka kwana da ita, ba barci. Surutai babu ma'ana. Abinda yafi basu tsoro, shine yadda harshen ta ya karye, tana magana kamar wacce ta sami matsalar shanyewar gefen jiki. Da safe kowa ya zo da kuzarin sa, turus! Yake yi, saboda abin akwai ban tausayi, ballatanta da idanuwan ta suka bud'e waras! Tana kallon kowa, amma bata sanin ko waye. Murna fa ta koma wa kowa ciki, domin al'amarin Nusaiba k'ara gaba yake yi, abin tamkar tabin hankali. Kwana 3 kenan. Da sassafe ta tashi da wani kuka mai tsuma zuciya da ban tausayi, babu abinda take kira, sai "Antina! Alhali ga Antin ta tana tallafe da ita. Ita ma kukan take yi, tana fadin,"Ga ni fa nan amarya, ba mutuwa na yi ba."Ta tsura mata ido zuru! Shi kan sa kallon mai ban tsoro ne, sbd idanuwan a juye suke, duk sun firfito waje. Zarah ta sake fadin,"Kin ganni? Ni ce amarya, ban mutu ba. Ki daina cewa za ki mike da gudu, kin ga (Operation) aka yi miki. Duba ki gani, kin ga Bebin mu? Ga Umma ga Inna. Yanzu yayan mu ma suna tafe. Ki na son ganin su ko? Ta girgiza kai, ta ce da karfi,"Antina ta mutu na ce! Wayyo Abba na, sun kashe Antina! Da gudu Zarah ta bar dakin, ta zube barandar waje, ta fasa kuka. Kwatsam! Sai ga su Ummi, tun daga nan suna jin ihun ta, tana kwala wa Abbanta kira. Ummi bata son lkcn da ta watsar da kayayyakin hannun ta ba, suka fada dakin. Su Umma na rirrike da ita. Alh.Basheer yayi azama ya rungumota,"Ga ni Nusaiba, ga ni, ki yi shiru." Amma kara fadi take,"Abba na ka zo sun kashe min Antina! Hankalin sa yayi mummunan tashi, ya dubi su Umma."Ina Doctor ne wai? Ta ce,"Sun zo har su 4. Nosis sun zuba magunguna cikin karin ruwar nan, sun mata allurai, har yanzu barci ya ki zuwa." Alh.Basheer yayi waje,