Sashe 1
A Jininsa Yake Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajininsa yake 3-01 Posted by ANaM Dorayi on 06:55 PM, 19-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______ . .Duba da yawan makaranta Hausa yasanyamu fadada hanyar sadarwar mu daga whatsapp zuwa bude blog, daga bisani sai nafahimci kamar da yawanmu vamufiyason shiga blog ba, Bansan dalilin hakanba, sakamakon yawan korafe korafe dake riskata yasanyani yin nazari wace hanyace ke da sauki bayan wannan, karshe dai natino face book, sakamakon haka muka yanke shawarar bude page a facebook din duk domin fadada hanyoyin sadarwarmu wadda ba dan komai mukeva sai dan jin dadinku,insha Allahu Labarinmu nagaba zai kasance ta hanyoyi Uku, :-Whatssap. 08139787515 :-Blog Anamdorayi.mywapblog.com Saikuma ... :-Face book.. https://mbasic.facebook.com/ HAUSA-Novels-389304544597988/?_e_pi_=7% 2CPAGE_ID10%2C7370123473 Hakan amma bazai tabbatuba sai da hadin kanku.. Dan haka inna bukatar 20,Like a group din kafin mu sanya littafi na gaba.. Naku har kullum ANaM Dorayi --------------------------------------------------------;------------------ Ya koma rigingine ya kwanta, ya rasa dalilin da yasa Nusaiba ta tinkare shi da wadannan maganganun banzan. So take ta hada shi da iyayensa ko me? Idan kuma ta gaji ne, ai bai yi mata tirke ba. Iyakar ta Alh. Basheer ya ce ya aje masa komai na sa, sai me? Daran nan Nusaiba bata yi barci ba, gaban Ubangiji ta gurfana kamar yadda ta saba kai kukanta. Allah ya za6a mata alkhairi. Haka kuma tayi kukan bakin ciki yau ita da mijin auranta take cacar baki. Lallai rayuwa shirin Allah ce, amma ko a mafarki bata ta6a tunanin hakan ba a rayuwar ta. A kodayaushe zuciyar ta na shirya mata kyakkyawar rayuwa da jin dadi tare da gamsashshiyar soyayya ga duk mijin da ta aura. A kunnan ta aka yi kiran sallar farko, ciwon kai ya ce ga shi nan irin wanda bata ta6a jin irin sa ba. Da kyar ta sallaci asuba. Ta jawo filo ta jefa bisa sallayar ta kwanta. Dora kan ta, ke da wuya ta ji fitar Naseer kamar da gudu. Ta tashi zaune tana sauraron buga kofar falon sasn su Abba. Ta mike ta fito kofar falonsu a gwame. Tayi waje can sasan su Umma. Naseer ta ji yana fadin,"Zarah ba lfy, yanzu Inna tayo waya inje maza-maza. Kafun su Abba su gama salati, ya fice. Ta koma daki da saurin ta, ta dauko hijab ta suro jakar hannu.don ta tabbata haka Naseer ya fita babu ko sisi ajikinsa. Ta fito, ta iske su Umma ma tsaye suke a waje, ya tafi ya bar su. Makullin motar ta na cikin jakar ta bude ta dauko,"Umma zo mu bi shi a wannan motar." Ta ce,"Ba ni so ki na yawon nan Nusaiba, cikin ki ya tsufa." Abba ya ce,"Gari bai k'arasa waye ba ma, kun tafi ku 2 mata a mota? Gara ku bari gari ya waye sosai." Ta ce,"Ba komai Abba, Allah zai tsare. Umma zo mu je yanzun garin zai waye." Umma ta shiga suka rankaya. Malam Balarabe na tayi masu addu'a. Hajaran majaran! Suka iske Naseer da Inna, domin ance jaririryar ta mutu a ciki, sbd haka Likitar za ta yi iya kokarinta su fito da ita, idan kuma abin ya faskara, aiki za su yi mata. Nusaiba ta nemi waje ta zauna jinin ta ya k'ara hawa, kan ta kamar ya tsage, sbd tsabar ciwo. Bayan kusan minti 40. Likitan ta fito ta ce, maza-maza su je su biya kudin aiki. Ta mika wa Naseer takarda, hannunsa na rawa ya rike ya duba. Dubu 35 zai biya. Umma ta ce,"Ka fito da kudi ko ko? Ya girgiza kai,"Sai na koma gida, kuma ina jin kudin da ke gidan dubu 10 ne kawai, banki kuma ba su fito ba, ya za'ayi kenan? Ya tambaya hankalin sa tashe. Kafin Umma ta ce wani abu Nusaiba ta miko rafar kudi, ga wasu yi maza kaje ka biya. Ya bi tada kallo kafin yasa hannu ya kar6i kudi ya kwasa da gudu ya nufi wajen biya. (Allah sarki baiwar Allah, Allah yahadamu da mata masu tausayinmu da kaunarmu) Duba da yawan makaranta Hausa yasanyamu fadada hanyar sadarwar mu daga whatsapp zuwa bude blog, daga bisani sai nafahimci kamar da yawanmu vamufiyason shiga blog ba, Bansan dalilin hakanba, sakamakon yawan korafe korafe dake riskata yasanyani yin nazari wace hanyace ke da sauki bayan wannan, karshe dai natino face book, sakamakon haka muka yanke shawarar bude page a facebook din duk domin fadada hanyoyin sadarwarmu wadda ba dan komai mukeva sai dan jin dadinku,insha Allahu Labarinmu nagaba zai kasance ta hanyoyi Uku, :-Whatssap. 08139787515 :-Blog Anamdorayi.mywapblog.com Saikuma ... :-Face book.. https://mbasic.facebook.com/ HAUSA-Novels-389304544597988/?_e_pi_=7% 2CPAGE_ID10%2C7370123473 Hakan amma bazai tabbatuba sai da hadin kanku.. Dan haka inna bukatar 20,Like a group din kafin mu sanya littafi na gaba.. Naku har kullum ANaM Dorayi Nusaiba fa duk ta rude, ta k'ara rikicewa musamman yadda ta ga Nosis na shiga suna fita. Likitoci 2 ke kan ta, suna ta k'ara kokarin su, domin ba sa son ayi mata aikin. Allah da ikonsa kuwa Likitan da aka kira, yayi nasarar ciro matacciyar jaririyar, sai dai Zarah nan take numfashin ta ya dauke. Ba ta ba dalilinta, komai ya daina aiki a jikinta. Suka yi caa kanta, latsa nan, gwada can. Amma ba alamar motsi. Likita ya tura a dauko (Oxygen). Su Nusaiba na tsaye. Nos din ta fito da gudu, jim kadan ta dawo da shi da shige dakin. Zuciyar Nusaiba ta soma bugawa, ta nufin dakin tana fadin,"Shi kenan Antina! Su Umma suka rirriko ta, su ma kukan suke yi. Inna ta ce,"Zo ki zauna Nusaiba, kin ga ba ke kadai bace. Ki kwantar da hankalinki, ki yi mata addu'a. Tana shiru. Naseer na iso wajen, bai yarda da yanayin daya gansu ba. Ga Nusaiba na kuka tana ta fadin,"Shi kenan Antina." Ya ce,"Menene Umma? "Ba komai, ji ka ka gaya ma su ka biya kudin." Ya tsura wa Nusaiba ido, duk ta fita hayyacinta, ya ce,"Ki yi shiru mana." Ta ja hijabi ta rufe fuska, sannan ya wuce, ta biyo bayan sa. Yana isowa kofar. Likitin na fitowa. Ya mika masa takarda da siri,"Doctor an biya kudin,"Ya ce,"O.K, ka rike risit din za'a maida ma ku da kudin ku, an riga an ciro Bebin. Ita ma uwar sai dai ku yi hakuri.... Nusaiba ba ta gama jin bayayin ba, ta yanke jiki ta fadi, nan take ta hau fizga. Gaba daya suka yi caa kanta har da Likitan. Abin kamar bugun jinnu, duk gabobinta sun sandare, idanuwa sun kakkafe, baki kumfa. Likita ya ce, a kai ta ofishin sa. Naseer ya dauke cak! Ya kai ta ofishin, ya kwantar bisa dan gadon su. Su Umma ne biye da shi kamar za su yi hauka saboda tashin hankali. Shi kansa Naseer hawaye ne ke sauka bisa kuncinsa. Likita ya miko masa takarda,"Sa min hannu nan, dole a cire abinda ke cikin ta, don tsira da rayukansu." Bai jira Naseer ya gama sa hannun ba, ya fice da saurinsa. Jim kadan wasu Nosis suka shigo da gadon daukan maras lafiya, dukkan su da kayan dakin tiyata a jikin su. Irin kayan suka sanya wa Nusaiba, suka maida ta gadon da suka zo dashi, suka gara ta dakin tiyata. A tsakar wurin Naseer ya zube ya kame kan sa hannu 2, ya rasa duniyar da yake." Me zan gani yau? Inna-lillahi- wa"Inna-ilaihir-raji'un! Umma ce tayi karfin hali ta kar6i waya hannu Inna, ta kira Malam Balarabe,"Mallam ka yi maza ka zo, abubuwa sun rinca6e, daga Zarah har Nusaiba ba mu san halin da suke ciki ba. A zaton da mu ke yi ma dai Zarah babu ita. Nusaiba kuwa yanzu suka wuce tiyata da ita." Hankalin sa yayi mummunan tashi, salati yake yana k'arawa, har ya rufe gida, ya kama hanya. A mota ya kira Alh. Basheer ya labarta masa halin da suka wayi gari da shi. Subhanalillahi! Babu 6ata lkc suka baro Kaduna. Malam Balarabe na isa. Shi Malama Umar ya iso. Yadda suka same su zazzaune haka su ma suka nemi wuri suka zauna. Naseer na nan dunkule a kasa. Malam Umar bai ko shaida shi ba, sai da ya jima a wajen. Ya tashi ya matsa gun sa ya tsugunna ya dago kan sa,"Naseer! Tashi daga k'asan nan, zo nan ka zauna." Ya kamo shi ya taso da kyar, suka zauna bisa kujera, yana rungume da kafadar sa. M.Balarabe shi ma ya taso, ya tsugunna gabn su ya ce,"Sun bada gawar ne? Ya girgiza kai, hawaye suka kara kubce masa, ya ce,"Sun ce ba mutuwa tayi ba, doguwar suma ce, shine suka sa mata (Oxygen)Gaba dayan su suka sauke numfashi, suka yi hamdala ga Allah, tare da addu'ar Ubangiji ya ba su lafiya. Kamar wucewar minti goma da zuwan su Abba. Likita ya fito, duk suka mike suka nufi gun sa,"Yaya Likita? Yayi dan murmushi,"An yi nasara,"Bebi, na nan lafiya lau, shi da uwar sa. Za'a fito da su nan bada dadewa ba. Kowa sai hamdala. Umma da Inna suka rungume juna. Duk da haka hankalin Naseer bai kwanta ba, so yake ya gansu da idon sa, ya tabbatar da lafiya lau suke. An ba su izinin ganin Zarah na minti 5r. Haka suka yi tsaye gaban gadon suna mata kallon tausayi. Inna ta fara barin dakin ta dawo wajen ta zauna, tayi shiru hawaye na tsitaya, babu abinda za ta iya yi, komai Allah yayi, dai- dai ne. "Yan mintoci bayan fitowar su daga wajen Zarah, aka kawo ma su Bebin da aka ciro wa Nusaiba. Bebi ne katon gaske jajur da shi, sannan babu abinda ya bambata shi da Ameer. Illa girma daya fi shi. Kowa yasa masa albarka, suka mika wa Babansa. Ya zura masa ido kamar ya lashe shi so da kaunar Bebin suka kama zuciyar sa. Kwalla suka cika idanun sa,"Allah ka raya mi shi." Ya fadi a ransa.. A lokaci guda daran jiya ya fado masa, nan da nan ya mike ya ba Umma Bebi, ya fice da sauri ya sami wata kwana, ya hade kai da bango. Babu abinda ke yawo cikin ransa, sai maganganun daya cacca6awa Nusaiba, a idonsa yake ganin lokacin da ta miko masa rafar kudi, duk a tunanin take ganin halin da ta shiga. Wanda komai zai iya faruwa da ita. "Da mutuwa tayi da shi kenan, ta tafi ta bar ni da hakkinta a wuya na?" Ya