← Book details Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 27

Sashe 8

Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A haka jama
ar gidanmu da
yan daurin aure duka suka taddamu wannan ya harari Fa
iz wannan ya tausaya mishi, babu wanda ya iya ce masa ko da sannu da zuwa bayan shekaru masu dama da suka kwashe basu sanya shi a idanunsu ba.

Shi kam Babana kujera ya samu ya kame yana kallon kowa daya bayan daya.

A lokacin Baban Kaduna wato Alh.

Mukhtar ya iso asibitin.

Da Dr.

Habib ya fito ya nemi son ganin daya daga cikinsu Baban Kaduna ne ya shiga.

Ya ce,
Muddin Fa
izah ba ta farfado ba nan da awanni uku, to zai yi wuya in ba coma bane ta shiga.

Sannan jininta ya hau, mugun hawa kuwa, zuciyarta ta tabu.

Kokarin da muke yi yanzu shine na jininta ya sauka, numfashinta da bugun zuciyarta su dawo dai-dai.

Na roke ku idan an samu Fa
izah ta farfado ku guji gaya mata awkward incidence ba ta hanyar da ta dace ba.

Domin sudden unpleasant shock ya kan harbi kwakwalwa har ya haifar da depression
Baba Muntari ya shiga sharar zufa, babu shakka ya shiga tashin hankali.

Ya ce,
Ba komi likita, shi kenan ai in an samu ta farfado din shi kenan.

Kuma ni ban san abin da aka gaya mata na tashin hankali ba, aurenta kawai aka daura da dan
uwanta yanzu-yanzun nan, bayan wannan ban san komai ba, dama can tana da makamancin ciwon hawan jini ko (something associate) ne bamu sani ba?

Dr.

Habib ya ce,
Lafiyarta kalau.

Sudden shock ne wanda zuciyarta ta kasa karba kawai.

To ko auren ne ba ta so?

Baban Kaduna ya ce,
Mai yiwuwa.

Biri ya yi kama da mutum, domin wasu daban sun zo neman auren ta.

Bari in je in same su in ji
.

Ya mike ya firto fuskarshi babu annuri sam.

Barau ya kira gefe suka yi magana don da shi ya fara cin karo, ya kuwa gaya masa komai a gurguje cewa, Fa
izah ba ta son Fa
iz tun tana kankanuwa, Fa
iz ya tsani Fa
izah, tunda aka haifeta basu taba zama a inuwa daya ba dai-dai da sakan daya.

Aliyu ta so ta aura kuma da bata samu ba ta dangana saboda Zaneerah.

Tun sanda Hajjah ta fara fito da zancen ya same ta cikin sirri ya ce kar a soma wannan kada gyara zumunci ya zama bata zumunci.

Su da aka yi musu haka suka zauna lafiya, to fa in babu soyayya a tsakani haka babu kiyayya, kuma su na jiya ne ba na yau ba, zamani kullum canzawa yake yi.

Zai fi kyau a dinga karbar canjin da ya zo da shi idan babu sabon Ubangiji ko halaka a cikinsa
Jikin Baba Muntari sanyi kalau kuma ransa ya baci domin shi ba haka Fa
iz da Hajjah suka gaya mishi ba kafin ya karbi waliccin auren nan.

Ya dauka cewa ko da hakan (doctrine) din su ne kuma umarnin Hajjah ne, to babu wani abu makamancin wannan tsakanin Fa
izu da Fa
izah.

Ofishin Dr.

Habibu ya koma ya dauko takarda da biro ya fito ya doshi Fa
iz wanda ke tsaye gefe yana kallon su cikin dimuwa, don ya amince ba ALHERI Baba Barau ke gayawa Baban Kaduna ba, ganin yadda fuskarsa ma
abociyar kamala ke tattarewa tana yamutsewa.

Don haka ganin ya nufo shi da takarda da biro fuskarshi babu alamun rahama, sai ya ji hanjin cikinsa suna dunkulewa wuri guda.
iz ya daga dara-daran idanunshi da suka kada suka yi jawur ya dubi Baba kallon rashin fahimta, ya motsa baki zai yi magana amma ya rasa me zai ce ne.

Baba ya ce,
Karbi ka rubuta min saki uku yanzun nan Fa
iz ya ja da baya ya soma hawaye ya ce,
Baba Fa
izah za ta farfado ne, amma ni ba zan yi saki ba....

Baba ya ce,
iz har ka yi kaurin wuyan in fadi ka musa min?

In ka kashe ta za ka auri gawarta?
iz ya shiga girgiza kai
ya ce,
Shin Baba a kan me za ka yanke wannan danyen hukuncin gare ni?

Ka sani muddin ka takurani na rubuta takardar nan shi kenan, in na tafi ba zan kara dawowa kasar nan ba, kuma ba zan.....

Wani irin mari Baba ya share shi da shi, sai ga habo ta hancinsa.

Ya kai hannu zai sake sharara mishi Babana ya rike hannun tamau.

Suka juyo suka fuskanci juna su biyun, kowanne zuciyarshi na tafasa, inda Baban Kaduna ya yi amfani da gadarar shekaru biyu da ya tserewa Baban ABU da su ya ce,
Ni sa
anka ne Ahmadu?

Ko ko akwai irin wannan wasan tsakaninmu?

Babana ya ce,
Babu ko daya, amma a nan kam ka yi zalunci in ka takurawa daya don amfanin daya.

Aure kuma Fa
iz ba zai saki ba in dai a kan don kar wannan yarinyar ta mutu ne.

Mutuwa lokaci ne kuma tana kan kowa, sannan lazim ce baka isa ka kara mata dakika daya daga wanda Ubangiji ya riga ya rubuta mata ba.

Ni dai ni na haifi Fa
izah in kuwa ni din ne to in ta mutu na yafe, zan dawwama da farin cikin cewa da igiyar auren Fa
iz ta mutu cikin cika burin mahaifinmu Abubakar Bamalli.

Sai dai fa abin bai kai da duka ba, Fa
iz ya wuce duka!

Sai dai in Fa
izah ta kashe kanta a kan shirmen banza ta mutu kafira ba ruwana, amma aure ko ka kunce sai na sake daurawa.

Ba a haifi dan da ya isa ya ki bin umarnin A.B Family ba, ba a haifa ba in dai ina da rai, ba kuma za a haifan ba.

Fa
izu jeka abinka sai na neme ka, kada ka kara wahalar da kanka zuwa asibitin nan
iz ya juya da sauri ya fita duk gaban rigarsa ya baci da jinin dake fita daga hancinsa.

Ya dauki motar Aliyu da suka zo a ciki ko rufewa bai yi ba ya yi ribas da gudu ya fita daga estate din baki daya ya bar garin Giwa baki daya ya nufo Kaduna.

Yadda ya shigowa Mama falo ya firgitata, sai dai kuma ba ta yi mamaki ba sam, habon ne da bacin da rigarsa ta yi da jini ya daga mata hankali, amma ba ta nuna ba.

Tozali na farko da Abubakar Fa
iz dinta bayan shekaru takwas.

Amma ta ganshi cikin wannan halin mara dadi da kyawun gani.

Ta yi tagumi ta zuba mashi ido sai zufa yake.

Daga bisani ya mike ya ware karfin A.C falon gaba daya da fanka, ya yi kwance rashe-rashe a tsakiyar falon yana lumshe ido yana budewa a hankali, shi kadai ya san abin da ke cin zuciyarsa, sai ko Ubangijin da ya halicci zuciyar ya sirrantata ya sanya mata hijabi don ta zama sirrin dan Adam da Ubangijinsa.

Ita Mama zato take ma Fa
iza ce ta fasa masa hanci, ta ce cikin ranta, ai tayi da sauki da ba kan duka ta rotsa maka ba.

Ta shige kitchen ta sakar masa labule ta janyo masa kofa.
****
Karfe biyar na yamma agogon dake dakin asibitin ya nuna, wanda ya yi dai-dai da lokacin da na ja dogon numfashi tare da ware dukkanin idanuwana kan likitoci biyu dake kaina.

Dr.

Habib da Dr.

Imoh suka dubi juna suka yi murmushi tare da zare na
urar da suka makala mini.

Kwata-kwata na mance komi, ban san abin da ya faru dani ba da har ya kawoni gadon asibiti.

Dr.

Imoh ya ce,
Ya ya dai Fa
ija?

Na yi murmushi na ce,
Bani da lafiya ne na ganni a clinic?

Dr.

Habibu ya ce,
Of course Fa
izah!

Za ki dinga fama da migraine (ciwon kan barin kai guda) lokaci zuwa lokaci.

A duk lokacin da kika ji ya tashi, akwai kwayoyin da zan baki ki dinga hadiya kin ji ko?

Na gyada kai.

Suka juya suka fita suka jawo min kofar.

Nurse ta shigo ta gyara min kwanciya ta fita.
uwa da iyayena suka shiga shigowa mutum uku-uku suna duba ni suna fita.

Shigowar Ummi da Zaneerah daga karshe ya tariyo min abin da ya faru awanni shida da suka gabata.
.......

An daura aurena da FA
EEZ, FA
EEZ BAMALLI.!.....

Fa
izun gidan Baban Kaduna......

Fa
iz Yayan Zaneerah, Fa
iz mugu, azzalumi, makaryaci, maketaci mai cin amanar ZUMUNCI da tozarta shi a gaban ko a bayan idon kowa...

Munafuki, masharranci....

Fa
iz da na sani?

Fa
izun Hajjah?

Fa
iz da na tsana tamkar mutuwata......

Fa
izun da ya nuna min tsanar da a duniya babu wanda ya nuna min kwatankacinta, mai cin mutuncin mahaifiyata!

Fa
iz!

Fa
iz!!

Fa
iz Mukhtar Abubakar Bamalli Giwa......!!!

Na mike zaune sannu a hankali ina bin Ummi da Zanirah da kallo, wadanda bayan kalmar sannu da jiki basu kara ko tari ba.

Na kai hannuwana duka biyu na rike kaina dake juyawa yana sarawa tamkar ya tsage.

Idanuwana suka kada suka yi jajawur suka kankace, na dubi Ummi, Zanira, Yaya Aliyu da Babana da suka shigo daga baya.

A lokacin ne hawaye suka soma zuba min tarara!

Na bude baki zan yi magana na kasa.

Wani kunci da bakin cikin da ba zan iya fassarawa ba ke azalzalar tsakiyar kirjina, na kai hannuna na dafe kirjin na ce cikin rishin kuka,
Baba anya kana sona kuwa?

Da hadin bakinka aka yi min haka?

Da saninka aka daura min aure da Ya Fa
In kun hanani Nazir ku rasa wanda za ku lika min duk cikin zuri
armu sai Hafizin Hajjah?

Baba kana sane da tsakanina da Fa
iz tun tali-talin kuruciya har girma!

Baba Fa
iz fa ya tsaneni nima haka!!

Makiyinka baya taba rikidewa ya zama masoyinka, har abada Baba.

Don me baku hada shi da Ummi dake son shi yake son ta ba?

Ya ya kuke so na yi da nauyin so, kunya da alkawarin da na yiwa Dr.

Naziru?

Na shiga rurin kuka mai tsima zuciyar duk mai imani, balle MAHAIFI.

Amma Baba bai ce komi ba, karewa ma fita ya yi daga dakin baki daya.

Su Aunty Hauwa duk suka sake shigowa, ashe suna kofar dakin basu tafi ba.
Chapter 8 · 0% Book details