← Book details Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 27

Sashe 10

Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na ce,
Ku bace min da gani ko in kakkarya ku na rantse yanzun nan, manyan munafukai algungumai, ai daku aka kulla komai amma babu wadda ta gaya mini.

Tsakanina daku sai Allah ya isa!

Ai kamin in rufe bakina na nemi kowaccensu daga yaran har manyan na rasa.

Na ci gaba da gunza kuka ban ko damu da radadi da zugin da jikina ke yi mani ta ko ina ba.

Muryar Yaya Aliyu daga tskar gida ya tabbatar mani ya shigo gidan.

A yayin da Ummi ke fadi mashi cikin kuka........

YAYA ALIYU FA
IZA TA HAUKACE!

Wadannan sune kalamai mafi firgitarwa da Aliyu Na
ibi ya taba ji a tsayin rayuwarsa.

Baya ga dogon salati da ya ja ya dire ya tsarkake Ubangiji ya yiwa Annabi salati, sai ya sanya hannu ya zare hularsa da takalmi ya ce,
Tana ina?

Hajjah dake sharbar kuka zaune a kofar kicin ta yi mashi nuni da hanyar store.

Aliyu ya shigo a hankali ya kunna fitilar da na kashe ya zauna gefena a hankali, ya dubi yadda na yi jina-jina, face-face cikin hawaye, jini da majina, ya matso kwallar da ta tarar masa cikin ido.

Shin wane ne da wannan danyen aikin haka Fa
izah?

Na ja shesshekar kuka cikin dusasshiyar muryar da ta dushe gaba daya,
Kadan kenan tun yanzu kan DAN DA KOWA KE SO.

Nan gaba in na batawa Fa
iz mai yiwuwa a nakastani ko a hura wuta a babbaka ni Aliyu?

Ba dukan kawo wuka ba, ko yankani A.B za ku yi gunduwa-gunduwa ba ni auren nan.

Na gwammace in bi yawon dandi, da dai in yi karashen rayuwata a matsayin matar FA
EEZ BAMALLI!

Aliyu ya kaskantar da murya ya ce,
izah!

Abin bai yi zafin haka ba ai.

Kash!

Ki bar furta kalmar nan ta
DANDI
ba don ni ba, ba don halina ba, ba don halinsu ba su duka iyayenmu.

Sai don darajar da Allah ya yi miki ta
ya mace mai cikar mutunci
yar manyan mutane, kuma
yar gidan mutunci kamar A.B.

Su wadannan da kika bi kika tadawa hankali meye ruwansu ne?

Me ya shafe su?

Aure dai sun yi kuskuren daurawa.

Amma igiyar warware shi da kwance shi ba ta hannunsu balle su kwance ko su warware.

Duk wannan kakabi da zagi da tashin hankali ba nasu bane, ba su ya kamata ki yiwa ba tsakaninki da Fa
iz ne can.

Amma ina ruwan Ummi, Hajjah ko Zanirah?

Na galla masa harara na ce,
To shin ina na ganshi balle in yi mishi Yaya Aliyu?

Ni kam yadda nake ji a zuciyata baki dayan A.B nake jin haushi.

Har kai din wallahi
Murmushi ya yi, ya rausayar da kai,
Ta ina laifin wani ke shafar wani?

Har da Yaya Aliyu?

Fa
izah
eez shi ya nemi aurenki da kansa domin gyara zumuncinku da ya gurbata a baya
Ban san sanda na lailayo ashar ba na ce,
ZUMUNCIN me?

In dai wannan shi ake kira gyara zumunci to ba shi bane, sai dai kara lalata shi.

Na ji zan iya yafewa Fa
iz dukkan abin da ya yi mani, amma ba ta hanyar aure ba.

In dai har an yarda a raba auren nan in auri Dr.

N na YAFEWA FA
IZ DUK ABIN DA YA YI MANI A BAYA!
[6/3, 4:13 pm] Takori: Aliyu ya ce,
A da har an tayar mani da hankali da aka ce dani wai
izahna ta haukace!

Ashe lafiyar kanwata lau.

To share hawayenki ki bar ta da hakarkari tunda kin ce haka shi kenan.

Yanzu abin da za ayi Fa
iz za ki yiwa wannan bayanin ta lallama da salama da kwantar da kai.

Kin san an ce..... mai nema shine a kasa har kullum.

Don haka kada ki ji komai don kin roki Fa
iz wani abu wannan hakkinsa ne a yanzu.

Shi ke da ikon yi ko ki.

Don haka dole ki aje rawanin kiyayyar gefe ki roki Fa
Yanzu Fa
iz ya canza, ba shi da wannan muguwar azzalumar fuskar da kike fadi, ke tsoronki ma yake ji!

Kin san an ce abin da ya baka kuka wata ran shi zai baka dariya.

Haka abin da ya baka tsoro wata ran shi zai baka dariya.

Baki ga ya kasa zuwa ba?

Amma ina ruwan su Zaneerah, Ummi da tsohuwar Allah HAJIYA HADIZA?

Na girgiza kai hawaye na zuba na ce,
Yaya Aliyu kai kadai ke sona a cikin gidan nan tunda har ka goyi da bayana ka gane abin da nake so su gane suka kasa ganewa, wato Fa
iz ba mijin aure bane, ba masoyi bane abin neman tsari ne.

Don haka na dauki shawararka, ka je ka baiwa su Hajjah hakuri domin na zage su sosai
Aliyu ya yi murmushi ya ce,
Har na ji dadi, ni Aliyu Baban Fa
izah!

Allah yasa nima tawa Fa
izar ta yi min biyayya haka tamkar mai sunan ta.

Share hawayen nan duka A beg...

Nasa habar zanina na share hawaye tas, duk jikina rawa yake da karkarwa.

Aliyu ya ce,
Kada ki damu da su Hajjah, su tunaninsu kin samu motsi a kanki ne.

Don duk kuka suke miki na tausayawa.

Ni kam na san babu yadda za ayi Fa
izata ta haukace a kan Fa
iz, faruwar hakan na nufin kenan FA
IZ ya yi galaba a kan FA
IZAH!

Na ce,
Never.

Idan har na yi hauka saboda Fa
izu na ji kunya na fadi babu nauyi, kuma ban haifu cikin Maimunar da yake zagi ba tunda ban rama komai ba, tunda na bar Fa
iz cikin nasa hankalin.

Wata ma zai je ya auro wadda ta fini ya ci gaba da rayuwarshi normal ni ko in kare a pyschiatric da Asylum
Cikin murmushi sosi Yaya Aliyu ya ce,
Yauwa, ashe dai kin gane.

Amma in ya baki takarda kika yi auren ki da Dr.

Nazir kinga ai kin tusa mishi haushi ko baya sonki zai ji kishi, tunda akwai igiyar aure da ta taba gittawa a tsakanin ku, ko ya ya ne.

In hakan ta faru da kyar ma zai iya zaman kasar ko ya kika ce?

Na yi murmushi da kumburarriyar fuskata na ce,
Shin Yaya Aliyu ina zan ga FA
IZ BAMALLI?

Yaya Aliyu ya ce,
eez na cikin kasarmu mai dimbin albarka yanzu haka.

Za ki ganshi yau, gobe, jibi ko gata.

Muddin ranakun nan suka wuce baki ga Fa
eez ba, to kirayi auren ku da suna tabbatacce na muddin rai.

Domin sune ranaku na karshe da za a kammala bikinku a kai ki gidansa kina so ko bakya so.

Don haka ki yi duk kokarin da za ki yi ki ga Fa
iz cikin kwanaki uku
Na yi zugum ina kallon sa, na ce,
Shin don me ka boye min tun a daren ranar Yaya Aliyu?

Wallahi-wallahi da duk yadda za ayi ba zan bari a daura auren nan ba......

Na ci gaba da kuka.

Aliyu ya rasa me zai ce mini?

Shi kam dabararsa ta kare kuma.

Sai ya ce,
Ni kaina Fa
izah yanzu ba na ce miki ga hakikanin inda Fa
iz yake ba, rabona da shi tun ranar da ya dawo
Da lallami da ban baki gami da dabara irin na Yaya Aliyu yasa na tashi daga store na je na kwanta a gadon Hajjah.

Daga Ummi har Zaneerah babu wanda ta yi gigigin shigowa don kam su tsorona ma suke ji.

Yarinyar da za ta bude baki ta zage Hajjah cikin A.B ai abar tsoro ce, balle nasu iyayen karan-kada miya.

Yau da Baban ABU ya ji kalaman nan da na kade har ganyayyakina.

Cikin daren na dinga shesshekar kuka ni kadai ina watangaririya a kan gadon Hajjah, daga wannan gefe zuwa wancan.

Na turza na turza cikin kowanne lungu na zuciyata wurin bin shawarar Yaya Aliyu ta ki amince min da hakan, wato in kwantar da kai in roki Fa
iz Allah-Annabi amma na kasa.

Ya ya zan iya zub da mutuncina ga Fa
iz in nemi wani abu daga gare shi, ashe ma ya isa kenan!

Never (fau-fau).

Dole ne ma ya bani, in ba ta tsiya ba ta tashin hankalin da bai taba gani a rayuwarsa ba!

Shima ya sani ko a lahira ba zamu yi makwabtaka ba balle zaman inuwa daya a duniya ko a lahira!!!

Wai ta ya ya ma Fa
iz zai nemi aurena, kamar yadda Yaya Aliyu ke cewa?

Ni fa Fa
izah da ya tsana?

Ni kazama dakikiya
yar Maimuna?

Uhm!

Ko don yanzu na yi idon gani na zamo abar kwatance cikin mata?

Da da nake a
uwarsa kankanuwar yarinya mai rauni da bukatar kulawar yayyu irin sa me ya hana ya kauna ce ni?

Ta ya ya yake tunanin ni Fa
izah zan mance kiyayyar da Fa
iz ya nuna mini tun ina ficiciyata har na kawo yanzu?

Sanda yake aikowa su Ummi kayayyaki BAN DA NI.

Ya tambayi lafiyar kowa BAN DA NI.

Ya nuna banbaci kiri-kiri da fifiko tsakanina da sauran
uwana......

Ya yabesu ni ya kushe ni..... ya zagi uwata a duk sanda ya so, ya dauko Ummi daga makaranta ni ya barni a jeji ko in mutu ko in yi rai ba damuwarshi ba ce.

Ba don komai ba sai don saboda tsabagen tsana da kiyayya!

Shin meye dalilin auren yanzu?

Don na yi girma na yi kyau na zama kyakkyawa.....

Don na yi kwakwalwar karatu wadda a da bani da ita.....

Don na yi kyawun da duk cikin A.B babu kwatankwacina balle tsarana!

Kaico da masu halin son zuciya irin Fa
iz Giwa.

Wani da shan wahalar raino, ilmantarwa tare da real kauna ga Fa
izah shekara da shekaru bai samu ba sai shi.

Wani da kwashe shekaru yana hidimtawa Fa
izah da inganta rayuwarta positively ba a bashi ba sai shi.

Ga masoyi na gaskiya irin Dr.

N mai wuyar samu a wannan lokacin, mai sadaukarwa so da kauna dukkan hakkokin da Allah ya ce a basu bai samu ba sai shi.
Chapter 10 · 0% Book details