← Book details Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 27

Sashe 5

Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk kula mazan da Ummi ke yi ba ta taba yi mata fada ba sai ni da na yi sau daya, ni da nake da niyyar aure ma ba flirt irin na Ummi ba.

Da zuciyata daya nake son malamina, da gaske auren shi zan yi in Allah ya yarda.

I love you.

If you hate it, kill with an arrow.

But please not in the heart because that
s where you are.

Gud night.

Sakon da ya fara shigowa cikin wayar kenan da na saka layin da ya bani cikin kwalinsa.

Why will I hate it?

Na tambayi kaina cikin murmushi.

I do love it too!

Na baiwa kaina amsa.

Don haka na baiwa Malami na amsa.

You inspire in me a love so deep and powerful that cannot be destroyed by any arrow!

How I wish there is a way you could see into my soul.

My love on you is far to strong Mallam!

Daga wannan na kashe wayar gaba daya.
****
Washe gari tun asuba nice farkon yin wanka a gidan.

Ban jira Ummi ba balle Yaya Muftahun dake sauke mu ya wuce office, na yi tafiya ta ni kadai saboda fushin da nake yi da Aunty Rabi, ban yi ko tunanin wani abu wai shi kalaci ba.

Babban burina in dora idona a kan lecturer.

Kusan nice farkon shiga laccarsa ta karfe goma ta safe.

Kai!

Ni Fa
izah na shiga uku!!!

Don I become infatuated to him fiye da kima.

Akwai wani sirri dake cikin kwayar idanunsa da ba duk maza Allah ya mallakawa ba.

Sai dai kuma cikin rashin sa
a bayan ajin ya cika (class-representer) din ya ce ya mai da ita (fixed) karfe biyu na rana.

Kamar na fashe da kuka dai-dai lokacin da wayar da na jefa a jaka ta kama tsuwwa.

Cikin rashin kuzari na amsa da tunanin yadda zan yi in mayar da ita din kamar yadda Aunty Rabi ta yi umarni.

Muryar mace ke tambaya,
Dacta ne?
a, ba shi bane, wace ce?

Ke me maganar wace ce?

Matarshi ce!

Sai ta kyalkyale da dariya ta ce,
Ki ce Haulatu Sani Galadanci na gaishe shi, kuma inda hali yana jiranki a office dinsa.

Saboda ke ya dage laccar ku zuwa anjima.

He can
t wait to see you.... cross sword....!

Kunyar Haulatu ta kama ni ainun yadda ta yi ta canza murya ta shammace ni na yi tabargaza, na yi shuka a idon makwarwa.

Jiki babu nauyi na nufi inda Haulatu ta kwatanta min cewa nan ne ofishin nasa.

A ofishin akwai hoton gwamna mai ci a lokacin da na shugaban kasa, sai na Alh.

Dr.

Ado Bayero.

Sanda na yi sallama rubutu yake yi amma bai kasa amsa min ba.

Na samu kujera na zauna har ya kare, sai ya turo min folder din da yake rubutun nasa hannu biyu na amsa.

Ko da na duba (note) dinsa ne da na yi missing har guda biyu cikin hand-writing dinsa mai kayatarwa da ban sha
awa.

Idona ya kai ga dan karfen dake like saman kofar shigowa ofishin da ban rufe ba.

Sunansa ne radau DR.

NAZIRU SANI GALADANCI.

Wato Dr.

Yayan Haulatu ne uwa daya uba daya ta yi min irin wannan ninkewar?

Kai abin da mamaki.

Har mun yi sallama na kai bakin kofa sai na juyo na ce,
Na yi mantuwa ne
Ta me Fa
izah?

Na dawo a nutse na ciro wayarsa daga jakata na mika masa, yasa hannu ya karba yana fadin
Ya kika dawo min da ita?

Aunty Rabi tana ta fada ne, ita ce ta ce na dawo maka da ita, ba za a barni na rike waya ba sai na yi aure
Ya yi kasake cikin kallona da murmushi,
Sai na ji na kara son ki, na kuma kara yarda da cewa da ki kai ke din
yar babban gida ce.

Abin da ban taba ji ba a wannan zamanin
yammata kamar ku a jami
a iyayenku sun hanaku rike waya, kuma kun bi, anyway.

Ki ce ma Aunty Rabi ta yi hakuri, ba za ki sake rike waya ba sai kin zama matar Dr.

Nazir insha Allahu
[6/3, 4:13 pm] Takori: Da sassarfa na karasa ficewa daga ofishin ina murmushi.

Yinin ranar zungur na kare shi ne cikin tunanin Dr.

Nazir da maimaita ambaton sunansa cikin zuciyata sakan bayan sakan, minti bayan minti, awa bayan awa son Dr.

Nazir karuwa yake yi a raina.

Yana kara habaka a birnin zuciyata.
****
Soyayyarmu da Dr.

Nazir ta yi nisa da karfin da ta zama sananniya a tsangayarmu.

Tsegumi kam iri-iri an kawo min a kan yawan
yammatan da Nazir ke dasu cikin makarantar.

Na kan toshe kunnuwana ne kamar yadda ya ce, ko in yi hannun riga da duk wanda ya kawo min tsegumin.

Dr.

Nazir ya ware muhimmin lokacinsa wurin yi min (extra class) bayan kowacce laccarsa.

Nazir ya iya koyarwa.

A dalilin koyarwar da yake yi min
points
dina a jarrabawa ya kara karfi fiye da na baya.

Nazir ba shi da karfin idanu (short sight), a dalilin hakan yake amfani da farin gilashi mai kara karfin gani (lenses) ya yin rubutu ko karatu, ko ba da lacca.

Amma in ba fadi aka yi ba za ka yi zaton na kwalisa ne.

Don yana mai kyau sosai.

Nazir mutum ne da ya iya tsara magana da hafizin harshen da Ubangiji ya hore masa.

Iya maganarsa da kirkinsa ya taka rawa mai yawa wajen sanya zuciyata ta zamo kangararra, bana ji bana gani.

Da kaina in ban ganshi ba sai na bishi office, har sayayya mu kan fita wasu lokutan.

Tun Ummi na hana ni har ta gaji ta rabu dani.

Wai ni Fa
izah tsatso daga A.B House nice mai bin saurayi har office, nice mai fita da saurayi.

Wannan ba karamin kona ran Ummi yake ba.

Har ta gaji ta tseguntawa Aunty Rabi.

Aunty Rabi ta samu Yaya Mufty take sanar da shi, inda ya ce,
A kawo mishi sunan Nazir cikakke zai yi bincike a kansa.

In mutumin kirki ne a kyale ni, kwana nawa ne zamu gama karatun mu koma gaban iyayenmu?

Domin Hajjah ta soma fadan mu dawo gida haka karatun ya ishe ta.

Abu ya ki ci ya ki cinyewa tamkar cin kwan makauniya
Aunty Rabi ta ce,
In kuma ba mutumin kirkin bane ba fa Mufty?

Ya ce,
Zan san abin yi a kai
Ni kam duk surutunsu da harare hararen su basa damuna, na yi nisa a son Naziru.

Wani irin so nake dandana mai wuyar fassarawa, wanda ya zarta na Yaya Aliyu fintinkau!

Idona ya rufe a son Naziru, lokutana baki daya na Dr.

Nazir ne.

Tambayar da jama
ar dake tare damu ke wa Ummi shin Fa
izah ta san Dr.

Naziru (use and dump) ne?

Ta ya ya yarinyar
yar gidan mutumci wadda ta san ciwon kanta irin Fa
izah ta yarda cewa Dr.

Nazir auren ta zai yi?

Shin Fa
izah ta san yawan
yammatan da Dr.

Nazir ya yaudara ya watsar a Kano?

Shi fa dama duk inda kyakkyawar mace take nan idonsa yake, zai nuna mata so ya yi ta yi mata facaka, amma da an ce ya fito ayi aure ba kya kara ganin keyarsa
Ummi ta kan girgiza kai, don bakin ciki ta rasa me za ta ce, sai dai ta ce,
izah kam ta yi nisa ba za ta ji kiran ba
A yammacin wata talata mun dawo daga Ado Bayero Mall (Shoprite) ni da Nazir ya sauke ni dai-dai inda ya ga su Ummi a zaune a (seaters) na dalibai karkashin wata bishiyar dalbejiya mai inuwa, bai ko tsaya sun gaisa da su Ummi ba don ya san Ummi ba ta goyon bayan tarayyarmu daga ita har shakikiyarshi Haulatu, ita ma ta bi sahu don tsoronta na kar mutuncinta ya zube idon su Aunty Rabi dake matukar ganin mutuncinta, ranar da Nazir ya yi (dumping) dina.

Ko ba don wannan ba Nazir baya sakar ma dalibanshi fuskar da raini zai shiga tsakani.

Ko mata da yake nema tamkar bunsuru ba dai cikin tsangayarmu ba can a wasu tsangayoyin ko waje yake neman abinshi.

Na yi musu sallama duka suka amsa min a sanyaye, na aje ledar hannuna gefen Haulatu ina fadin
Wash Allah!

Na gaji da yawa.

Dr.

N (sunan da nake kiransa) ba dai yawo ba, shi dai a je shopping burinsa kenan
Suka dubi juna suka kau da kai.

Cikin nutsuwar da ban san tana da ita ba Ummi ta ce,
izah rayuwar da kika zabawa kanki kenan?

Tarayya da maza irin su Dr.

Naziru?

Yau da Hajjah za ta ji wannan mummunan labari ina kike tunanin za ta tsoma ranta?

Da kin sa zuciyarta ta yi bugawar farat daya.

Wallahi-wallahi tun wuri ki sake hanya tun dare bai yi miki ba.

Nazir ba dai-dai yake da tsarin rayuwarki ba, kuma aurenku ba zai taba yiwuwa ba.

In kin manta kin fito daga zuri
ar A.B ne nake tuna miki
Haulatu ta cafke
Ina mai matukar jin kunyar ranar da Yaya Naziru zai yi dumping din ki, (as if you had never been in existance), shi yasa nake so ki kwaci kanki tun kafin zuwan wannan ranar, domin mai hali baya fasa halinsa, kuma sannu ba ta hana zuwa sai dai a dade ba a je ba.

Nazir dai dan uwana ne, karewa ma shi ya sha nono ya saki na kama, uwarmu daya ubanmu daya.

Amma bana goyon bayan ki mallaka mishi soyayyarki.

Abin dai da baki son a ta da to dole ne a fadi, ba auren ki zai yi ba
Na yi murmushi na ce,
Kun gama?

Shin ina kaunar da kuke ikirarin kuna yi min din Haulatu da har ba za ku so abin da nake so ba don cikar farin cikina?

Kuna kina da Dr.

N ne don tsoron kada ya yi min yadda yake yiwa sauran
yammatan da ya nema a baya, shin ku Allahn musuru ne?

Kun san gaibu?

Kuma shin shi halin dan Adam baya canzawa ne?

Dr.
Chapter 5 · 0% Book details