Sashe 15
Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani sashe na zuciyar Fa'iz Giwa ya ce.
"Shin me Fa'iza take taqama da shi ne haka da yasa ta ci galaba mai yawa haka a kansa, in ba don sharrin SO ba?
In ba don son ta ba da ya sameshi rana xaya baiga abinda ma zai sa shi yin aure a halin yanzu ba, bai shirya masa ba (at all) yana cin kuruciyarsa ne.
In ba don so da ba ya shawara ba, bai ga dalilin da zai sa ya baro aikinshi wanda kullum ranar Allah samu ne mai xumbin yawa a gareshi, ya zauna yana ganin baqin ciki ba.
Ko ma me zata yi tayi ta gama, however, yana son matarsa, saki a tsakaninsu yana ganin wataqila shi ne abu na qarshe da ba zai tava yi ba a rayuwarsa, sai in mai yanke hanzari ce ta cika umarnin Ubangijinta (mutuwa).
Mutuwar tashi ma, zai so ace daga hannun Fa'iza ce ba don Allah baya yafe haqqin rai ba, a ganinsa in tayi hakan wataqila gyambon zuciyarta zaya warke.
Tunani na qarshe da ya ziyarce shi, shi ne ta gama suman, qafarshi qafarta, kwas xin nan da zai tafi Amsterdam sati uku masu zuwa, tayi ta suman tana farfaxowa yana da ruwan da zai yi ta yayyafa mata, indai ba mutuwa zata yi ba Falillahil-hamdu.
Bai kai qarshen tunaninsa ba Bashir ya bude murfin motar da qarfi, ji kake butt!
Ya fito yana fadin.
"Kai, don ubanka ance ma ni bawan gidanku ne da za ka tsaida ni a gefen titi zafin rana na duka na?"
Fa'iz ya yi tsaki ya ce, "Kada ka sake zagar min uba Yaya Bash!
Ta yaya zaka kunna min hayaqi cikin mota in zauna ina shaqa, na tayaka sha kenan?
Iyaye kuma tunda ba ka ganin darajar su ni ina son kayana, kada ka sake ka sake zaginsu a gabana, na rantse ba zai yi maka dadi ba".
Bashir ya dubi Fa'iz sosai yana cikin wani irin yanayi na tashin hankali da bai tava ganinsa ciki ba, har wata rama ya yi, kafin ya baro Russia ba haka ya sanshi ba sam.
Jikin Bashir ya yi sanyi, ya koma mota ya zauna ba tare da ya yi magana ba sai da Fa'iz ya mula, ya kammala shan qamshinsa da harare-hararensa kana ya ja motar aguje tare da sakin qira'ar Abdurrahman-Sudaith a rediyon motar cikin Suratul Nisa'i.
Wannan ya taimaka wajen sanyaya zuciyarshi dake tafarfasa babu gaira babu dalili.
Bashir dai binsa yake da ido, da zuciya, ya kasa shiru, bayan sun jima suna tafiya yana kallon Fa'izun wanda idanunshi suka kaxa suka yi jawur.
"Wai kai me ke damunka ne?"
Fa'iz ya harare shi ta cikin madubi, "Ai ni babu abinda ke damuna face tawa matar da ta tsane ni tamkar mutuwarta, duk da bani da wani hali abin qi, baya ga shirmen quruciya na can baya, wanda da ace zata saurare ni ta saurari kalaman dake qunshe cikin baki da zuciyata da ta fahimce ni, kai kuwa ke da damuwa.
Baya ga baqin munanan xabi'un da kayo guzuri, shan giya, taba da bin matan bariki tamkar tsohon bunsuru, kai da wai an kaika ne domin ka zama ubana, mai dorani bisa hanya sahihiya, ka rikide ka zamo tantiri, wacce irin qiyayya ce ba zaka gani daga taka matar kamila Hadizatu ba?"
Bashir ya tashi zaune daga kishingidar da ya yi a kujerar baya tare da wurgi da abinda ke hannunsa ta taga gaba daya, ya antayo ashariya cikin harshen (Ukrain) wadda Fa'izun a duk zamansa a Russia shekaru goma vai tava jin wani ya yi ba, haka ya lailayota da turanci wadda Fa'izun bai san akwai ba ma, sannan ya shimfidota da Hausa ji kake.
"Abu kazan uban nan!
Uban waye ya xaura min auren?
Sharrin da zaka je kayi min a gida kenan Fa
iz?
Wato dama ido ka sa min a duk motsina ko me?
Duk tambadar da kake yi da Alicia na tava daga ido na dube ka da zaka ce ina neman mata?
Ai dama gwano baya jin warin jikinsa...".
Fa'iz ya yi saurin miqa hannu ya kashe qira'ar da ya kunna na karatun Alqur'anin dake tashi, ya juyo ga Bashir bayan ya kashe motar baki dayanta.
Ya yi rantsuwa da Allah ya sake rantsewa ya ce.
"Wallahi-wallahi ka sake zagar min iyaye sai na sauke ka a dajin nan yaya Basheer!".
Basheer ya dubi qwayar idon Fa'iz sosai har wani blue-blue take, jijiyoyin kansa sun tashi rada-rada saboda fushi da mazantaka, ya ce a ransa.
"Anya Fa'iz qanina ne?"
Fa'iz qato ne qwarai murzajje mai wasu irin qarfafan damatsa da ginannen jiki na Bamallin usli tamkar (Late) Abubakar Giwa a sanda yake nashi tashen quruciyar, yana nome manyan gonakinsa da hannunsa ba tare da ya nemi mai tayashi ba.
Irin mazan da jarumtakar su ce kadai tasa duka rabin rayuwar su cikin iska suke yinta, ruwa, hazo, zafin rana, sanyi ko duhun dare baya hana su lulawa cikin sararin samaniyar Subhana.
Wanda duk ya yi qoqarin dambe da su, mace ko namiji labudda uwarshi ta haifi wani kawai amma ba shi ba.
Savanin shi Basheer da (gulder), hayaqi da zina da ya jefa kanshi a Russia rana daya suka haxu suka tsotse masa jiki da kuzarinsa.
Sai dan banzan bakin tsiya da kaudi wanda ba a kashe shi a magana.
Inda suka bambanta da Fa'iz kenan, wanda kafin ya yi qwaqqwarar magana ma aiki ne jawur, sai lokacin da ya sa kansa.
Bashir ya ja bakin (glass) ya mannawa idanunsa, ya koma yadda yake da, wato kishingida, yana ta huci shi kadai kamar kumurci, bai qara magana ba.
Fa'iz ya ja motar a guje, bai tsaya ba sai a qofar gidansu dake unguwar Jabi Road cikin garin Kaduna.
****
A uwar dakin Mama take lallashin Bashir yana kunkuni cewa yake.
"Aure?
Aure??
Wane irin aure yanzun nan haka sabida Allah, mutum yana tsaka da cin kuruciyar sa, ko an gayawa Hajjah zamanin da irin na yanzu ne?
Kuma a rasa wanda za a aurawa wannan lukutar yarinyar mai shegen qarfin tsiya sai ni?
Salon in na mata ba dai dai ba ta hau ruwan cikina yadda take danne su Zanirah?
To ni yanzu ma daga gama karatu ban kama aiki ba anzo an dora min aure, ku ne za ku dinga yi min dawainiyar auren?
Sannan ni wallahi ba zama nazo yi ba, na zo ne kawai in ganku in koma.
Dama ace 'yar siririyar ku ka aura mini 'yar wajen Baban ABU sai in karva da godiya, me ma take ne da suna Fa'eez?"
Fa'eez dake gefe ya juya musu baya yana kallon tangamemen hoton Fa'izah da Zaneerah, sun sha goggoro ranar bikin Zanirah da Mama ta kafa a falon, ya wani irin juyo cikin (slow-motion) ya qwalalowa Bashir kyawawan idanunshi, ya ce.
"Yaya Bash!
Ahir!
'yan iskan idanunka bisan matata!
Na gaya maka, na qara (warning) dinka, o.k?"
Mama ta dafe kai, "Fa'iz, yaushe ka koyi rashin kunya ne for Allah's sake waye baya kuskure a bisa rashin sani?
Ka bari Bashir ya dora idonshi bisan ummi kamin ya yi wadannan sambatun banzan mana.
Bashir, kana magana ne akan wasu kwailayen yara mitsi-mitsi daka tafi ka bari shekaru takwas a baya da suka wuce.
To wadannan...".
A yayin da ta miqe ga daya 'enlargement' din dake can hanyar kofar fita na Zanirah da Ummi, shima ranar bikin Zanirah ne sun sha ankon beig swiss laces mai ratsin silver da goggoro kalar adon leshin, wato (silver), wanda in ba ka daga idonka sama ba baza ka hango shi ba saboda anyi (placing) dinsa da nisa, ta taka kujerar cin abinci, ta dauko ta sauko fuskarta cike da annuri ta dora ma Yaya Bash akan cinyarsa.
"Ga Ummin Hajjah".
Bashir ya kurawa Ummi ido na 'yan dakiku yayin da kalmomin da suka shiga fita daga bakinshi bai san dasu ba...
"How does this girl turn to slim?"
Duk da tension din da Fa'iz yake ciki wanda Bashir din ya hada masa sai da dariya ta kama shi, ya yi murmushi cikin takaici ya tashi ya bar dakin yayin da Mama ke kyalkyala dariyar jin dadi tana kallon idanuwan Bashir da ke neman zazzagowa akan hoton.
A ranta ta ce.
"In banda anfi karfin Ummi me zata yi da Bashir don Allah?
Ita kam tana fatan Ummi ta zam silar kimtsuwar xanta daga halin da ya tsunduma kanshi babu gaira babu sabar, don duk komi yana dawowa kunnenta, duk da Fa'iz ba duka yake gaya mata ba sai dai ya ce tayi masa addu'a, ya canza hali rana daya.
Ta daga hannu sama ta godewa Allah Al-khaliku sarkin qaga halitta da ya suranta Ummi kirar da ta fi karfin namiji ya wulakantata.
Ta sani da yawa kamilallun mata 'ya'yan gidan tarbiyya suke shirya mazajensu masu mugayen dabi'u irin na Bashir, don haka ta kara godewa Hajjah tare da binta da kyakkyawar addu'a a zuciyarta na Allah Ya ja kwananta cikin zuri'arta har kansu (junior) ko ana so ko ba a so.
Allah Sarki Maman Kaduna, a wannan ranar bata yi bacci ba, kwana tayi akan kafafunta tana kai sunan Fa'iza ga mai duka, kan ya karkato da hankalinta taso Fa'izu.
Mama hawaye take da idanunta, a yayin da take rokon mai cusa soyayya da ya cusa soy
ayyar Fa'iz a zuciyar Fa'izah.
Soyayyar da babu kamarta a duniya wadda ta fi gaban wadda take yiwa Nazir Galadanchi.
Babu abinda ke damun Mama irin ganin yadda Fa'iz ke neman ya susuce kamar baya ji sosai, sai kayi magana sau uku kafin yasan da kai a gabansa, tunani yake ko da yaushe.
Tun dawowar shi bai iya ya tsaya ya ci wani ginannen abinci ba kullum sai tea, lemo, snacks.
Jiya kam da ta shiga boys qutarers nemansa yana wanka ta tadda hotunan Fa'iza sunfi kala goma anyi enlarging dinsu an kafa a kowanne kusurwa na daki da falonsa, musamman cikin bedroom, tayi tunanin ina ya samo hotunan?
Da ta tambayi Yahya ya ce shi ya aika ya karba mishi wurin Walida.
Mama kam ta tabbatar hakkin Fa'izah ne ya kama Fa'iz.