← Book details Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 27

Sashe 12

Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai wannan rana na ga wulakancin duniya da takaici da bakin ciki wanda ke kokarin fin karfin juriya da karfin halin da nake tinkaho da su.

Nake amfani dasu ko yaya ne wajen ganin na kwato hakkina daga iyaye da dangina na A.B baki daya.

Sai da idanuna suka lafa daga zugin da suke yi min na kuma tabbatar da basu tsiyaye din ba kamar yadda nake tsammani.

Na shiga toilet dinmu wanda dama like yake da dakin barcinmu na wanko fuska da ruwan famfo mai sanyi, tuni zuwa lokacin an kece da kidan kwarya mai dadin amo da dadin sauraro.

Wanda sautinsa ke amsa kuwwa cikin kwakwalwata yana zabalbalar min da ita.

Ji nake shine amo mafi rashin dadin sauti da na taba ji a rayuwata tunda uwata ta haife ni.

Mawakiyar waka take yi cikin lasifika tana kiran sunana tana hadawa da na Fa
izu Abubakar-Hafizin Hajjah, angon Fa
izah sanyin idaniyar Hajiya Hadiza Giwa.....

Kin isar, kuma kin cika, baki taba gazawa ba uwar zuri
ar Abubakar Bamalli....

Allah ya ja kwananki ya kara miki lafiya ki ci gaba da kulle tsintsiyar Abubakar Bamalli.

Takawarki lafiya uwar maza uwar Muntari, uwar Na
ibi uwa ga Ahmadu, uwar Ibrahim, Sani, Salisu da Sadi.

Ki bani mota ki kaini Makkah Hajjah Giwar mata, Giwar mutanen Giwa.....

Da gudu na fito daga bandakin ba don komi ba sai don tagarsa tana tsakar gidan dai-dai inda tsohuwar ke zaune tana wakar mai kama da banbadanci tana rawa daga zaune, saboda ba ta iya mikewa saboda kibar da ta yi mata katutu.

Sai na ji kamar tana amfani da wakar tata ne da karin (tune) ko kuwa (melody) mai gaya min cikin tsakiyar kaina cewa, abin da Hajjah ta yi dai-dai ta yi, ina so ko bana so kuma ba zan taba yin nasara a kan A.B ba, sune suka riga suka yi a kaina.

Wannan tunanin kamar anyi min wata irin allura mai kashe lakar jikin dan Adam ta karar da kuzarinsa, ta raba shi da BURIN sa da duk wani buri da ya ciwa rayuwarsa.

Hawaye na malala ta kowacce mabubbuga ta idanuna yana kwarara a kan fuskata na tube kayan jikina dake kamshi na fita hankali ma zan ce ba na tashin hankali ba na canza wasu.

Sai
da na saurara na tabbatar su Adda Hanne da iyalanta su Zaneera da
yan kanzaginsu sun shige gidan Baba Na
ibi dukkaninsu don su kama Ummi, na sulale ta gareji ina jan trolley dina wadda ban cika da kayan da za su wahalar dani ba na bi ta baskwata inda babu
yan biki, mazan kuma duk basa nan, na bi ta hanyar da suke bi zuwa masallaci na fice daga gidan.

Maigadin yana can yana baiwa tantabaru abinci.

Tafiya nake bana ko waiwaye da wata irin sassarfa mai hade da gudu-gudu kamar zan tashi sama, bana ko ganin abin da yake gabana, ban kuma damu ba wai don mota ko babur sun buge ni ba, gara su buge nin in mutun in huta da nufin A.B a kaina.

Don dai ba zan iya kashe kaina bane tunda na san abin da zan tarar idan na aikata hakan, babu mai kamasho ciki da za a raba bana mutuwar kafirici tare ni kadai zan dauki dakon abuna.

Amma shiga ta duniya ba ni kadai zai yiwa illa ba, zai yi laga-laga ne da zuciyar duk wani da ya kwana ya tashi cikin zuri
ar Abubakar Bamalli, su rasa kwanciyar hankali da nutsuwarsu irin wanda na rasa tunda kowannensu cikin farin ciki yake da yankan kauna da kisan mummuken da suka yi mini, ni kadai ce cikin halin kaka-nikayi.

Nema na su rasa alhalin sun san ba mutuwa na yi ba shine kadai kokari na karshe da zan iya, tunda kalmar fatar bakina da duk wani bore na ya gaza, abin dariya ne ma abin a zauna ayi ta dariya.

Tunda su dai burin su ya cika, gara in mutu da su tausaya mani, su dubi al
amarina da zuciyar hankali da tunani.

Da wannan tunane-tunane da zancen zuci da tafiya a kan hanya da kan titi bayan horn da zagi iri-iri da ga motoci da babura na bude ido na ganni cikin tashar motar garin Giwa.

Ni da kaina na tabbatarwa kaina bani da wurin zuwa cikin danginmu kaf din su a karbe ni, in ka dauke gidan Baban Kaduna.

Sai dai kuma ai abin da kunya da nauyi, gudun auren dansu nake yi da suka tsuguna suka haifa, kiyayyarsa ke neman kashe ni da raina.

Kuma su zamo sune mafakata idan ina da kunya?

Bugu da kari wanda ake bata kashin domin sa ba zai wuce can din ba, tunda baya Giwa wanda na rantse da in ga azzalumar fuskarsa na gwammace in yi arba da (arm robbers) cikin talatainin dare zai fiye min alheri da kwanciyar hankali fiye da sake arba da Fa
iz a sabuwar duniya da nake rayuwa bayan ta kuruciya ta shude da shi a ciki da duk wani al
amarinsa da na sani.

Duk da na san babu jituwa ko kankanuwa tsakanin Hafizin Hajjah, Fa
izu Abubakar da iyayensa da suka haife shi, Baba Muntari da Maman Kaduna, wani sako na kololu zuciya da kwakwalwata ya tuna mini da cewa DA har gobe sunansa DA a zuciyar iyayensa, ko da kuwa Hitler ne mai daukan rayukan al
umma babu dalili.

Da wannan tunanin sai na fada motar garin Zaria, wadda za ta kai ni har ABU in har DA shine DA a zuciyar iyayensa komin muninsa ko munin halinsa da munin ayyukansa, to kar in nemi gidan Baban Kaduna gara in koma ga tawa uwar wadda bana baiwa muhimmanci cikin rayuwata da hujjata ta banza mai cewa, ita ma ba ta bani kulawar da Allah ya ce ta bani.

Na tabbata idan duk duniya ta taru ta ki ni ta juya min baya a lokacin da bani da kowa, bani da gata, uwar da ta haife ni ko ba za ta kulani ba, ba za ta kore ni ba.

Wadda ta sunkuya ta kawo ni duniya Fa
izun ke kamo sunanta yana zagi a duk lokacin da ya so, a dalilin ta haife ni kuma bare ce ba ta hada jini da iyayensa ba.

Bayan wannan ba ta yi masa laifin komai ba.

Babban abin da ke damuna a wannan duniyar hujjar Fa
iz ta aure na?

Har ya iya bude baki ya furta hakan bai ji kunyar kowa nawa ba?

Duk da ba a auren na gani ina so cikin zuri
armu shi ya furta kuma an ba shi saboda fifikon da yake da shi a zuciyar Hajjah!

Ko da zan mutu, zan so kafin isowarta (mutuwar) in samu amsar wannan tambayar, mene ne dalilin Fa
iz na aure na?

Tunda na amince an halicce shi ne da kiyayyata ya girma ya rayu cikinta, ya bar kasar Nigeria cikin rainonta (kiyayyar), ya kuma yi gammon abarsa ya tafi da ita Rasha, ya kare shekarun da ya yi baya gida cikin soyayya da Ummi..... da kiyayya gare ni.

Na ce, kyawun da na yi ne wanda a da bani da shi, da tsabtar da na yi a yanzu wadda yake goranta min bani da ita a baya, yake kyara da hantara da wulakanta ni a kanta, su suka sa ya zo yanzu ya ce zai aure nin.

Hajjah ta ce ba su bane, ta kuma kafa hujjar ta da cewa, tunda Fa
iz ya tafi har ya dawo tsayin shekarun nan ko hotona bai taba gani ba, balle ya ga canzawar da ni nake ikirari.

To mene ne?

Mene ne hujjarsa?

Yana nufin alkhairi gare ni?

Yana yi min tanadin alkhairi?

Yana nufina da alheri da wannan auren ko ko ya yi shi ne don karasa cimma mummunar manufarsa a kaina ta ganin ya raba ni da duk wani farin cikin rayuwata?

Na wulakanta na tozarta na tagayyara a rayuwa?

Ina ruwan Fa
iz da duniya ta da burinsa kawai ya raba ni da jin dadina dake cikinta?

Tunaninnikan da nake ta yi kenan suna ci gaba da soya min zuciya, fuskata jage-jage da hawaye, domin iyaka tsinkaye da dan tunanin da Allah ya hore mini sun kasa bani amsar tambayoyina ko da guda daya daga ciki, har mai tasin da nake ciki ya hau kan titi dodar ya kama hanyar Zaria.

Mu karasa a
A littafi na 3
Takorin ku ce.
[6/3, 4:13 pm] Takori: ZUMUNTAR KENAN?-3
Mai taxin ya gaji da gaya min gamu cikin Zaria, ina zamu dosa?

Na zama kamar mutum-mutuma, kurma, makauniya don tunani, saida ya bubbuga kujerar danake zaune nace masa gida mai lamba tamanin cikin gidajen malamai na jami'ar Ahmadu Bello.

Gidan da ya zamto mahaifata, dandalin quruciyar rarrafe da tata-ta ta, kafin in gujeshi zuwa inda nake ganin ya fishi farin ciki da walwala, a yau gani na dawo da qafafuna, na kuma gwammace in qarashe sauran rayuwata cikinsa ko da ace yafi kurkuku rashin Dadi da taqaita farin ciki.

Wata irin doguwar ajiyar zuciya na saki, na ciro kudin da suka rage min kaf ko qirgawa banyi ba na baiwa mai tasi, ya fitar min da jakata daga bayan motar sa, ya yi min godiya mai yawa ya ja motarsa ya bar harabar wajen.

Zan iya kimanta lokacin da qarfe takwas na dare sanda nake tsaye qofar gidanmu, domin ina iya hangen tanqareren agogon falonmu wanda hasken qwan lantarki ya wadata, kuma an dage labulen wawakekiyar tagar falon.

Rashin motar Baba ya tabbatar mini bai shigo cikin gida ba, ya shiga cikin (city) kamar yadda ya saba duk bayan sallar isha'i.

Don haka naji dan sanyi da qwarin gwiwar cira qafa da tura jakata.

Sai dai a take wani irin tsoro da shakka suka lulluve ni, idan Momi ta yarda ta qyaleni in zauna Baban ABU zai qyaleni ne bai gayawa iyaye da 'yan uwansa ba?

Kuma wane mataki zai dauka a kaina tunda ga dukkan alamu bai dauki al'amarin nan da sauqi ba?

Hakan dai nayi shahadar quda da yin qarfin halin danna qararrawar qofar shiga falon (door-bell), sai da na danna sau uku kafin a buxe.

Walida ce, zata yi magana nayi hanzarin kai hannu na rufe bakinta, muryata na rawa na ce.
Chapter 12 · 0% Book details