Sashe 19
Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya tsuguna a gabana ya dora hannu bisa tafin kafata, amma ya kasa sake furta komi, wani ajin yana motsawa yana so ya maida shi Fa'izun shi yana so har gobe har gaban abada kada Fa'izah ta juya shi ko ta ga (week-point) dinshi. (Na yaushe kuma Fa'iz?
TAKORI).
[6/3, 4:13 pm] Takori: Sai ya mike a hankali yaja da baya ya juya ya doshi kofa, sai da ya kai bakin kofar sai ya juyo kadan cikin fadin.
"Allah Yaji kan NAZIR S.".
A lokacin ne mutuwar da Ya Rabi ta ce min Dr.
Nazir yayi ta dawo min danya sharaf, tuni hawayen dake makale cikin idanuna suka tsinke baki daya.
Addu'a ce mai kyau ya yi ga masoyina na hakika, wato Dr.
Nazir Sani Galadanci.
Don haka na ce.
"Ameen Ya Rabbi".
A yayin da ya sanya kafarshi waje zai fita daga dakin.
Wani sauti ne ya fito tun daga karkashin zuciyata na zuciyar 'yan uwantaka va tare da yayi shawara dani ba.
"Haka zaka fita kayan ka duk jini?"
Sai bayan na furta ne naji kunya da alamun nadama, sosai idanunshi ke nuna cikin juwa yake karfin hali kawai yake na duk maganar da yake yi, a hankali yayi murmushi ya dan juyo ya dube ni.
"Za suke tuna min da irin kyakkyawar sallamar da muka yi da matata (a da) kanwata FA'IZAH A.A GIWA.
Don haka kada ki damu da su, ko nazo sanya (uniform) ba zan zubar da su ba, zan tafi da su har Great Britain".
Yayi murmushi (a karo na biyu)
ki sanya kayan da Momi ta baki
ya fice da sauri.
Oho kuma wai inji wohoho!
Kai ya shafa, ni dai tunda na rabu da alakakai falillahil-hamdu.
Dama abinda yasa ni tambaya ganin yawan jinin ne tunda haka yake so meye ruwan Fa'izatu?
Momi ta dube shi a yayin da ya kai kofar fita zuciyarshi a jagule, ta ce.
"Yanzun Fa'izu haka za ka shiga cikin mutane kaya duk jini?
Ka zo ga na babanku ka saka sai ka tafi".
Ya yi murmushin da Hausawa ke kira yake.
"Babu komai Momi, da naje (Airport) canzawa zanyi zuwa (uniform) ai".
Rabi ta ce, "Daga nan sai ina?"
Ya ce, "Ina da (interview) ne Aunty Rabi a kasar Birtaniya".
Idanun Rabi sukai rau-rau, hawaye na son zubowa ta ce.
"Haka zaka yi tukin jirgi Fa'iz da rauni a cikin kanka?"
Cikin kosawa da son ya tafi kafin likin da yayi ya balle, ya ce.
"Babu komi Ya Rabi, bi'izinillahi Rabbi".
Ta ce, "To baka hakuri da tafiyar zuwa sati mai zuwa kafin nan Fa'izar ta sakko ku tafi tare?
In ta zauna nan me zata yi mana?"
Fa'iz ya sake murmusawa cikin takaicin kalaman Aunty Rabi, ya ce.
"Shin cikin ku Ya Rabi wa ke da jan wuyan sanyata ta bini ba ma gidana ba har wata duniya a yadda take ji da taurin kan nan?
Yanzun ma dabara nayi mata muka rabu lafiya, ki rufa min asiri in tsallake in bar Nigeria Ya Rabi".
Yasa kai ya fice abinshi.
Bai isa (Airport) ba sai ana kiran sallar magariba, a yayin da ya karya motar ya shiga filin jirgin ne zugin da radadin da tsakar kanshi ke yi ya tsananta.
Ya kashe motar a wuri na musamman ya fita ya dauko jakar kayanshi na (boot) ya rufe motar, cikin sauri ya gama cike-ciken takardun da zai yi.
A yayin da ya shiga (pilot's changing room) domin sauya kayan jikinsa zuwa na matukan jirgin sama ya tuna da abinda ya ce da Fa'iza, ya yi murmushi.
A lokacin ne cikinshi ya soma kugi, wani irin kugi da bai taba yi mishi ba, yana tuna mishi rabon shi da kwakkkwaran abinci tun dirar shi Nigeria daga Russia.
Yanzu kam da zuciyarshi tayi sanyi, hankalinsa ya kwanta da samun kalami mai dadi daga Fa'izah yana jin zai iya hadiyar abinci ko abin sha.
Abinda bai taba samu ba tun tasowarsu (kalami mai dadi daga Fa'izah) ko da yake shima din haka bata taba samun rana irin ta yau daga gareshi ba.
Don haka ya yi (marking) ranar (as precious).
Wata rana mai dumbin tarihi a cikin ranakun rayuwarsa.
Fa'izah tayi kuskure da take tunanin zan iya sakinta koda daya ne balle uku rigis, saboda shima haukan da ake zaton mata ya sameshi ko me?
A yadda yake jinta a zuciyar nan tasa, yake jinta a ko'ina na ruhi da bargon jikinsa?
Shi kam bai san ma yana son Fa'izah ba sai yau din nan, ashe ada hasashe yake, ba don wani kyawunta ko kyakkyawan girman da tayi ba, a'ah yin Allah ne kurum, shi ya daura masa ta yadda bashi da harshen da zai fassara soyayyar Fa'izah a zuciyarsa, tun ranar da ya bar Giwa zuwa kasar Rasha.
Ya tuna rotsen da tayi mishi, sai ya girgiza kai ya yi murmushi.
Kuruci dangin hauka kenan.
Fa'izah na ganin hargaginta da (power) dinta shi zai kwatar mata 'yancin da take so, har yaji tsoronta ya sake ta?
Tsoron sa Allah-tsoron sa ranar da zai dawo gida Nigera daga wannan tafiya da zai yi wanda ya tabbata idan taji tsiyar da ya shuka mata a takarda ta nemi tsire shi da mashi, wannan ne hukunci na karshe da yake tunanin Fa'izah zata yanke masa in ya dawo.
Bai kai karshen tunaninsa ba (computer) ta shiga ankarar dashi lokacin tashinsu yayi.
Za su tashi ne karfe uku na sulusin daren ranar ta Alhamis daga (airport) din Abuja zuwa Wales din kasar England ba kamar yadda ya kintata da farko ba, wato karfe goman dare, don haka lokacin haduwarsu da Majid ma ya canza don sunyi 'transit' a
Scotland'.
Karfe sha biyu na safiyar washegari suna Wales.
Kowa dake cikin jirgin ya fita in ka dauke (pilot) Fa'iz Giwa, yayi shiru shi kan
sa bai san me yake tunani ba har saida wani abokin aikinsa ya ankarar dashi za'a rufe jirgin, sannan ne ya daura idon shi akan jakar kayanshi ya dauka ya mike ya fito.
Monica da kawarta Divya, suna daga cikin fasinjojin jirgin da Fa'izu Abubakar ya biyo zuwa Scotland, zai sake kwasa zuwa Ingila.
Sunzo ne musamman daga Abidjan domin halartar kallon wasan kwallon kafa na gani da ido a (Chelsea UK).
Ta gabansu Pilot din ya gifta a (reception) jaye da 'yar jakar kayanshi a hankali akan (marbles).
Tsakanin Monica da Divya, an rasa wadda zata fara dauke ido a kansa har ya kulewa ganinsu ya bi (lifter) zuwa (underground).
Monica ta tabo Divya.
"Kin sanshi ne?
Irin wannan kallo haka?"
Divya ta girgiza kai, "Kamar nasan fuskarsa, ya taba debo mu daga Paris zuwa Ukraine".
Divya ta ce, "Bahaushe ne fa tamkar mu ba Balarabe ba, sai dai ta ko ina babu fuska".
Monica ta hadiyi miyan da ya tsaya a makoshinta, ta dafe kirji ta rufe ido tana ta faman gyada kai kamar kadangaruwa, wata irin soyayya na cinta Fa'izun bai san suna yi ba wai kunu a makota.
Sun hadu da Majid a filin jirgin saman Wales, ba abinda Majid ya fara hangowa sai lafceciyar (plasta) akan Fa'iz da goshinsa.
Hannu ya mika ya rungumo kafadunsa suka karasa wani dakin hutawa na musamman dake cikin filin jirgin, suka zauna a tare cike da gajiya da tsamin jiki na kwanan zaune.
Majid Abduljalal Balaraben Syria ne wato (Shaam), tare suka yi karatu da Fa'iz a Russia da Johari da wani bakar fata Solomon Bayaraben Nigeria (they are very close to each other) don haka sun san tarihin juna, sun kuma san damuwar junansu.
Majid bai tabbatar ba, amma jikinshi ya bashi anyita ba dadi da Fa'izah.
Hasashen shi ya hasaso mishi ita ce ta yiwa Fa'iz wannan raunin.
Fa'izu ya ja numfashi ya sauke, da gasken-gaske cikin damuwa yake mai yawa, wadda ta kasa boyuwa akan kyakkyawar fuskar shi.
Maajid ya bubbugi kafadunshi, ya yi murmushi ya ce.
"WO-MAN!
Inka fahimci kalmar ko?
Tana nufin Wo!
MAN ka shiga uku kenan!".
Duk halin da Fa'iz yake ciki sai da Maajid yasa shi dariya, ya yi mai isarsa kafin ya ce.
"Maajid!
Maajid!!
Ya aka yi kasan cewa Fa'izah ce ta rotsa ni?"
Ya ce, "Oho maka wannan kuma!
Ni dai na san kai ba makaho bane balle ince faduwa kayi ka ci da baka ka fasa goshi ka fasa kai, na kuma san ba dambe kayi ba aka fi karfinka da (giantness) din nan naka Fa'iz.
Na kuma tabbata ba gidan giya kaje wani yasha ya bugu ku kayi rigima ya rotsa maka kwalbar ba".
Sai ya sake tintsirewa da dariya, ya ce.
"To amma saboda Allah me yasa ka kirani adai-dai lokacin da kasan ina tsakiyar yakin neman soyayya a tsakiyar rikici da Fa'izah?
Shin ko kasan wannan kadan ne da ace ban yi mata karyar saki ba da ta kwankwatse ni gaba daya da gilasai?'
Majid ya yi tsaki ya ce, "Kai ka so duka wannan shirme na Fa'izah.
Ni kam yana daga cikin abinda ya hanani aure yanzu, wato fargabar irin macen da zan debo ma kaina, don ni dai ba zan auri matar da bata so na ba wallahi.
Idan wani ya ki ka da wuni, wani da kwana zai soka.
Ba'a san maci tuwo ba sai miya ta kare, don haka mu bamu fara cin tuwon ba ma balle miyar ta kare, yanzu ne muka fara laluben har sai mun lalubo mai son mu.
Mu matuka jirgin sama, muna bukatar mata masu matukar son mu, wadanda kullum muka fita sai sun kai goshinsu kasa sun roka mana kariyar Ubangiji saboda kullum rayuwarmu cikin sadaukarwa take, za'a dawo ko ba za'a dawo ba.
In zamu fita su faranta mana, hakazalika in mun dawo.
Sannan ba nymphos ba (masu yawan bukatar Da namiji) ka gane?
Don haka ne naga wautarka da rashin azancin ka wurin nemo auren yarinyar da tun fil'azal kai tafi tsana sama da komai a rayuwarta wai a matsayin (life-time partner) dinka.
Kada ma kayi gigin kawo mana Fa'izah a yanzu, ta hada maka zafin da zaka tura rayukan al'umma cikin (solar-system).
Ka barta tukun, zuwa wani dan lokaci har ta sauke zafin kanta".
Ya yi murmushi mai hade da sautin dariya.
"Yau Majid so kake ka kasheni da dariya.
Da alama kana da (good experience) akan WOMEN din nan.