Sashe 20
Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
To ga tambaya, shin ya za'ayi Fa'izah ta so ni?
Ni dai (I can't do without her no matter what).
Ko kasan duk haukan kiyayyar da Fa'izah ke yi a kaina bana jin ciwo?
Ka san cewa har iyayena Fa'izah ta zage su tas akan idona ban ji komai ba, me yasa?"
Da sauri Majid ya amsa.
"Don kana sonta mana, so irin na halaka ga maza, wanda ya zarce halastaccen so ya hada da ribatar zuciya, so na fiye da kima don iyaye ba'a hada su da wata abar banza (mace).
Duk da ance so hana ganin laifi to amma banda iyaye. (They made us what we are today!
They are, therefore, incomparable to any worldly material).
Ka farka daga gigin son nan Fa'iz ka zama jarumi akan Fa'izah kamar yadda kake jarumi akan komai.
Sai dai in kiyayyar Fa'izah ta ci gaba wata rana zaka kita kaima.
Kiyayyar Fa'izah a gareka ta yi yawa, tafi wadda ka ce kayi mata.
Ni dai in ni Maajid ne bazan jure ba, mace ta fasa min kai... ta zagar min iyaye, mace!
Mace!!
Mace!!!
Woman, Imra'ah!
Ana maa Adhry!!!
Macen ma wata karamar yarinya Fa'izah da ta tashi a kauye irin Nigeria?
Ba zan dauka ba".
"Baka taba fadawa a son Woman din da ka rainawa kura bane Maajid shi yasa kake duk wannan cika bakin da kake yi.
Nima da irinka ne, haka nake da wannan akidar.
Ban taba zaton akwai macen da zata sani zub da kaina ba sai da Allah Ya dora min lalurar ciwon son Fa'izah.
Ko kasan har kasa na dire gwiwoyina ga Fa'izah?
Maajid SO BA KARYA BANE.
Sai dai ta wani bangaren ina cizawa ina hurawa.
Iyaye duka iyaye ne a zuciyar kowanne Da na halak Maajid.
Na zagi uwar Fa'izah yafi sau shurin masaki akan idonta a kunnenta kawai don bata fito daga family dinmu ba, ban taba tunanin yaya take ji a ranta ba, duk da yarinyar ce a lokacin.
Kuma kasan saboda mene?
Ba wani abu bane kawai Maman nata (we are not bloodly related).
Babanta yaje bautar kasa yayo (secret marriage) da ita daga Taraba da yake na gaya maka a zuri'armu ba'a auren (outsider).
Bayan wannan Aunty Mainuna bata yi min laifin komi ba, baya ga ALHERI.
Ko kallon banza nayi mata murmushi take mayar min a da can tana fadin yarinta ce, idan na girma zan gane wani baya auren matar wani, itama bata taba zaton zata auri bazazzagi ba tana cikakkiyar bafulatana.
Da Allah Ya tashi saka mata Maajid rana daya sai Allah Ya yiwa al'amarin nawa juyin waina da kaunar abinda ta haifa tun ranar da aka haifeta.......".
Labarin mai tsaho ne Maajid, (just bear in mind I have reason to love and respect Fa'izah and her mother to such an extent, and I'm ready to do everything to undo the hurt I caused to them).
In kuma ci gaba da jajircewa ga rike igiyoyin auren Fa'izah da duk iya karfin da Allah Ya halicceni da shi har sai na dinke ZUMUNCIN A.B family ya koma yadda ABUBAKAR BAMALLI ke son ganinsa, hakan kuma zai ci gaba ko babu tsohuwa Hajjah (to the last journey) insha-Allah, ni na lalata ni zan gyara, duk da ance ba'a bari a kwashe dai-dai, jikina na bani ni zan kwashe daidai Maajid, sai Fa'izah ta so ni fiye da sonda nake mata in Allah Ya bamu tsawon rai da lafiya".
Jinjina kai Maajid yayi, ta wani bangaren ya yarda ta wani bangaren bai yarda ba.
"To da ka dire mata gwiwoyin a kasa, ka roketa me?
Ta so ka?"
Ya yi dariya ya ce, "Ina!
Karewa ma kwarjini tayi min na kasa fadin abinda nayi niyya".
Maajid bai san sanda ya fashe da dariya ba.
"Amma ka ba da maza Pilot.
Zan so ganin wace ce Fa'izar nan da zata ki namiji kamar ka ko yankar naman jikinta yake yi kullum, sai dai in ba mace bace.
Tukunna ma cewa nake shekarun yarinyar basu fi ashirin ba?
In har kana da tsokar zuciya a jikinka Abubakar, kuma kana son in yarda kai namiji ne mai mazakuta a jikinsa ba bonono kake mana ba mata-maza ne, ka share Fa'izah kayi kamar ka manta da al'amarinta kada ka koma inda take sai nan da (atleast) watanni uku.
A kalla Fa'izah tayi haukarta ta gama ko da bata bari duka ba to 80% zai ragu tunda ta zame maka mutu-ka-raba daga kai har iyayenku.
Sannan ne zaka neman sulhu cike da juriya da kai zuciya nesa, ka hadiye duk wani borenta so zallah zaka yi ta (portraying) ka zama kalar tausayi ka nuna baka da katabus sai yadda aka yi da kai, ka kwanta kace
in takani za kiyi to ga bayan taka
Amma yanzu abinda yafi haka ma Fa'izah zata yi maka indai labarin da ka bani can baya da yanzu gaskiya ne, UWA ba abin wasa bace, ai na dauka ita kadai kayi ta yiwa shakiyancin.
Tunda kace ita Maman (have reason with you) baka da matsala da ita kun fahimci juna tuntuni.
Wacece Fa'izah?
Me take takama dashi da zata ce bata son ka Fa'iz baya ga kyawun da take da shi?
Me aka yi aka yi ta?
Sai dai in muna-mata ce ba mace ba wadda tasan me ake so a namiji.
Takamar diya mace kowacce iri ce kafin a daura mata aure ne, amma yanzu Fa'izah ta zama nama, bata da sauran abin tinkaho.
Duk yawan kiyayyar ta fa muddin ta dauki ciki Fa'iz ta kare, domin a lokacin ne zata shiga fargabar ba zata so danta ya yi maraici ba, kuma ba zata so a kirata bazawara ba, ko kada ku rabu ta rabu da 'ya'yanta, Zata shiga tunanin yanzu fa ta zama (second-hand) ba zata je gidan da babu mace ba, kuma kasan ba son kishiyar nan suke yi ba, kuma idan ta fita, ba zata samo yaro kamar ka ba ko da ta samu mara mata din.
Zata shiga fargabar me zata je ta tarar gidan mutumin nan dama ta zauna da wanda bata so din ita azo a tadda ita tunda ku zama da mace fiye da daya al'adarku ne.
Kiyayyar diya mace tana da wasu magunguna guda uku wadanda in kana dasu, wallahi sunan kowacce diya mace "sorry" ko ko ince (finished product).
Na farko mace na son yawan kyauta na abinda tafi so daga hannun mijinta, kyauta wadda zata ratsa mata zuciya ba gayan kudi ba.
Sannan mace Allah ya yi ta da son a nuna an damu da ita, duk inda kake, ka nuna mata tana ranka kana tuna ta da so da kauna.
Tana kuma son a darajja ta (kada ka nuna mata danginka sun fita, suna kuma kada ka nuna musu ta fisu) ka barwa kanka wani sirrin na zuciyar ka.
Tana so ka kwantar da kai ka bata hakuri in ka bata mata rai.
Da fari zata nuna shariya ne, amma zuciyarta sanyi take, tana hucewa a hankali.
Idan ka matso 'yar kwalla zaka ji ta ce, "Shi kenan, ya wuce".
In ka kawo kyautar nan in ranta yana bace zata ce, "Ni bai dameni ba" ko "bana so ka bar abinka" amma a cikin zuciyarta sonka karuwa yake yana fidda rassa.
Haka kayi kokarin ka fahimci duk wani (likes and dislikes) dinta shima ka dage da gujewa/aikatawa.
Ka rike amanarta, kada ka dinga zancenta da kowa ko da 'yan uwanka.
Duk inda kake, ya zamanto kana yawan nemanta tare da nuna mata ita kadai ce a gabanka saurin mata basa burgeka ko da ba hakan bane (in reality) a zuciyarka.
In kayi riko da wadannan Fa'iz kiyayyar Fa'iza komin girmanta babu inda zata je.
Fa'eez ya dube shi cikin mamaki.
"Who taught you all these?"
Maajid ya yi murmushi.
"Matar Yayana (psycologist) ce muna dasawa da ita sosai.
Tana yawan bani 'theory' akan mata da abinda suke so.
Ko baya ga haka ni ba irinka bane da inji kadai kasa gaba. (All work without play make jack dull boy) ina karance-karancen Novels domin samun nishadi (mostly authorized by women).
Kuma ina soyayya da mata kala-kala a kasar mu.
Ina zaunawa da kanne na mata ina jin hirarrakinsu da damuwoyin da suke ciki da mazajen su, ina sakar musu fuska ni ba (terror brother) bane irinka".
Fa'iz ya kyabe baki ya ce, "In ka gama surutunka don Allah tashi muje mu samu (hotel) in kwanta in huta.
Zazzabi ke neman rufeni sabida jinin dana zubar.
An gaya ma Fa'izah na kamar sauran matan da ka fahimta ne?
An gaya ma Fa'izah zata tsaya ta saurari mutum har yayi mata wani dogon sharhi in ta tsane shi?
Koko an gaya maka Fa'izah abin hannun maza ya dameta da zan bata abu, ta amsa bata kwada mini ba? (Above all) ma ta yaya kake tunanin ni Abubakar Mukhtar zan yiwa mace kuka har in tsaya lallashinta ta samu kafar wulakanta ne?"
Maajid ya kunna sigari ya dasa ma lebbansa, ya ce cikin murmushi.
"Meye kuma ya rage baka yi ba?
Yanzun nan fa ka gama ce min ka durkusa da gwiwoyinka a gaban Fa'izah ba matse maka baki nayi ba".
"Tsugunno daban, kuka daban.
Ko da na tsugunnawa Fa'izah bance mata komi ba balle inyi mata kwallah.
Da in yiwa Fa'izah kwallah don ta so ni wallahi gara mun dauwama a haka.
In na sami sararin aiki inje gidansu ko ta taga ne in leka in ganta in dawo bakin aiki na kada Allah Yasa ta biyonin, an gaya maka a matse nake da mace kamar ka?"
Maajid ya fashe da dariya, ya ce.
"Ba'a rabu da Bukar ba an haifi Habu.
Amma da ka tabbata sakarai, haka kawai Allah Ya halatta maka abu ka haramtawa kanka?
Fa'izah dai mace ce dake shekarun shekarunta na (teenager) ba abinda tafi bukata a yanzu irin kasancewa da namiji da zama gidan mijinta, musamman da kace duk tsararrakinta an kaisu dakin aure.
Ka zauna nan kayi ta rikon aure, ta yi saurayi mai debe mata kewa koda da hira ne asarar wa?"
Ya kai mishi wani mugun kutufo a kwibi, ya ja jakarsa keey...!
Ya taka da gudu ya shige (lifter) ya barshi a baya.