Sashe 24
Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na dago idanuna jike jagab da hawaye,
"Kada ka kuma yi min zancen wani Fa'iz, nazo (partyn) nan ne don Ummi da Bashir, don me zaka zo kana tambaya ta wani Fa'iz bayan mun rabu tuntuni?" Dariya Surajo ya yi, "Aradu bonono Fa'iz yayi miki wai rufe kofa da barawo, waye ya ce miki Fa'iz zai iya sakin ki?
Ko jiya shi ya kirani daga England ya ce in taimake shi inzo in tsaya tare da ke, bai yarda da kowa ba cikin abokanmu sai ni.
Wane irin saki babu ko dadin ji?
Kina hauka ne?"
Wani irin rugugi naji cikin kwanyar kaina, da kyar in ba motsin kwakwalwa bane.
Na zazzaro ido ina duban Surajo ina auna abinda yake fadi cikin hankali da tunani.
Nasan Surajo mutum ne mara wasa, na sanshi da can don ya so Ummi aka nuna ba za'a bashi ba ya hakura.
Abubuwan da suka faru suka shiga dawo min sabbi kar, wato yanayin Fa'iz bai nuna damuwa ko bacin rai ba a sanda yake min rubutun cikin takarda, babu wata alama ta nuna damuwa a fuskarshi.
Me ya hana Baba bai lallasa ni ba, kuma su Aunty Rabi babu wanda ya yi fushi dani a lokacin?
Sai ma cewa da tayi in taso mu tafi bikin Ummi Giwa?
Me ya hana ni karanta takardar da kaina abin kamar tsafi?"
Raina ya yi mugun baci, hankalina ya jirkice, idanuna suka kada suka yi jawur suka wani irin cicciko da kwalla.
Suraj Nuhu, ya yi danasanin karambaninsa, ya tabbatar ya yi babban kwafsi, kuma abinda ba'a aike shi ba don son ya burge.
Ya shiga in-ina yana fadin.
"Fa'izah da gangan nake, na rantse miki bamu yi maganar komi da Fa'iz ba, ni na kawo kaina...".
Ina!
Surajo ya barota domin kuwa mikewa nayi gaba dayana tsam nayi hanyar fita, yayin da ya biyoni yana magiyar in saurare shi, amma kurar da ta debo shi ban kalla ba.
Su Ummi suka dakata da abinda suke yi suka biyo mu da idanu.
Aliyu ya saki hannun matar shi ya biyo bayanmu, ya riqo hannun Suraj ya ce ya rabu dani, kana ya haushi da fadan.
"Don me yasa ka gaya mata Surajo?
Wa ya aike ka yi mata zancen Fa'iz?
Ka san haukar Fa'iza kuwa?
Muna zaman zamanmu lafiya ka sayo mana tashin hankali".
Surajo cikin matsananciyar nadama ya ce.
"Ni ina na sani?
Na gaya mata ne kawai Fa'iz ne ya yi min waya cewar yana Wales inzo in tsaya da ita, shi kenan abinda na fada".
Yaya Aliyu ya dafe kai yana fadin, "Shi kenan Surajo ka baro mana likin, sai gyaran Allah.
Wallahi ko lallashi ba zan je ba ta je can duk inda zata je zata dawo da kafafunta, ai ba yau ta fara ba
Da daren washegari aka raka Ummi gidanta a Kabala Custain.
Washegari Zanirah da Aliyu da
yarsu Fa'izah suka wuce Lagos, na Giwa suka nufi Giwa, na Zaria ma haka, haka na Kaduna.
Miftahu da Ya Rabi suma suka dauki hanyar Kano da yaransu biyu, amma Ya Rabi ta ce da Yaya Mufty su tsaya Zaria su ga halin da nake ciki.
Hajja kam ta ce da su don Allah kowa ya kyale ni inyi kida na da rawata ni kadai, kada wanda yaje inda nake balle ya wani lallasheni in bata masa rai a banza.
Amma Ya Rabi ta kasa jurewa.
Ko cikin 'ya'ya Fa'iza ta daban ce a wurinta, tana da matsayin da babu mai shi cikin tarin 'ya'yan nata.
Da na baro Indoor Sport Hall Zaria na nufa a taxi bana ko ganin abinda yake gabana don tsananin takaici da tashin hankali.
Fatana inga takardar sakin nan nawa da idanuna in karanta abinda ke ciki.
Har aka zo kofar gidanmu ban sani ba ina sharar hawaye da dankwalin leshi na, sai da mai taxi ya ce.
"Hajiya, ba nan ne gidan ba?"
Na bude na fita na fiddo kudin da ban tsaya kirgawa ba na dai tabbatar yafi abinda zai nema na zube mishi a kujerar gaba nayi ciki.
Na danna kararrawa (door bell) Momi ta zo ta bude duka hannuwanta cude da fulawa ina jin alkubus take yi.
Ganina haka hajaran majaran fuska babu alamun rahama ta tabbatar cikin ranta da kyar in ba (bomb) din ne ya tashi ba.
Ta matsa min hanya na shige, ta koma kicin ta ci gaba da aikinta.
Gidan babu kowa sai Walid autan Momi, duk suna Kaduna cin biki.
Na fadi nan bisa carpet na shiga kururuwa kamar na rasa iyayena biyu a lokaci daya.
Momi bata ce min cikanki ba, haka ko lekowa bata yi ba.
Wannan ya kara kunna ni, na mike na shiga tamaula da kayan falon su filillikan kujera, flower rose.
Ganin ina shirin yi mata ta'adi da kayan kallonta ta fito a fusace ta nuna ni da yatsa.
"Wallahi-wallahi ki kiyayeni cikin gidan nan, kinga dai babu kowa, babu mai kwatar ki don haka sai inyi miki dukan tsiyan da zai taimaka ya dawo dake cikin hankalinki, don da alama Fa'izah ke dabba ce, dabbar ma ta daji wadda bata san ciwon kanta ba.
Allah Yasa Fa'izu yankan kai yake yi, ya yanke naki kowa ya huta wannan bala'in".
Na hade kaina cikin gwiwa bayan nayi fatali da goggoron.
"Momi bai kamata kice min haka ba, duk abin nan da nake yi saboda in kare mutunci da martabar ki ne daga idanun wanda bai san kina da su ba, don ni ta tawa mai sauki ce ban dauki kaina a bakin komai ba balle in dauki wulakancin da Fa'iz ya shekara yi mini abinda zai hana ni shakar numfashi a duniya.
Ba zan taba son shi ba Momi, ba zan taba ganin farinshi ba tunda ya wareki daga cikin iyayensa.
Duk abinda yayi min a baya kin manta Momi...".
"...Na manta don ubanki, sai ki sani in tuna!
Wallahi ki ka sake yi min kururuwa a gida sai na kakkarya ki, kin kuma koma inda ki ka fito kinji na gaya miki".
Sai na tura kai cikin kafafuna nayi ta rasgas kuka a hankali, babu mai lallashi balle wanda zan yiwa in huce.
A kuma yanayin Momi na na tabbata zata aikata abinda ta fadi na sake na sake daga mata sauti.
A haka Babana ya taddani, ya zauna cikin kujera yana fadar.
"Kiyi kukanki mai dalili, yi kukanki da babbar murya Fa'izu bai sake ki ba!
Da yake shi ya haifu cikin uwa da ubanshi ya san darajar iyayenshi da karfin ikon su a kansa.
Allah Ya dawo dashi lafiya kafarki kafarsa, inda duk ya sanya kafa na rantse da wanda raina yake hannunsa".
Kwana biyu aikina kenan ina abinda naga shine rangwame a gareni wato (kuka) duk na koma jemammiyata ta baya a dakin Abdallah.
A haka ne Ya Rabi da Ya Mufty, kan hanyarsu ta komawa Kano sai gasu a Zaria, Aunty Rabi ta shigo ta iskeni dakin Abdallah, ta aje mayafinta da babynta akan gadon Abdallah, ta ce.
"Kai!
Fa'izah bakya gajiya, zuciyarki bata gajiya da kuntatawa kanta a banza a wofi alhalin hakan ba zai sa ba, kuma ba zai hana ba!
Shin duka wannan na kiyayyar ne, ko na haushin Fa'iz dan albarka bai yi saki ba?"
Nayi banza da ita, can kuma na ce.
"Ki bani takardar in gani da idanuna".
Da murmushi fal a fuskarta ta ciro takardar a jakarta ta ce.
"Gata".
"Don haka in zaki hutar da kanki da zuciyarki to ki hutar, in kuma kina ganin kukan ki da tayar da hakarkari da hankalin ki shi zai sa Fa'eez ya yi saki to anan kam kinyi kuskure.
Haka in ma duka da kwalba ne shima aikin banza za kiyi tayi don kuwa Fa'iz jinin Hajjah ne, rabin zuciyarta, magajinta.
Idan ya ce 'eh' baya taba dawowa ya ce, 'a'ah'.
Shin don Allah in tambaye ki, meye abin ki ga Fa'iz?"
Na dago sharkaf da zufa, kashirban da hawaye da majina bayan na karanta takardar.
"Ai ba zaku taba gano aibunshi dani nake hangowa ba tunda danku ne, ba kuma ka taba ganin aibun danka komin muninshi ko munin halinshi.
To tunda ba zaku gani ba da duk hujjar da na kawo to ni na tsane shi ne, bana sonsa, fakat!
Da inyi zaman aure dashi gara min zama a dokar daji da bakin-kumurci.
Allah da Ya halicce ni Shi Ya daura min kiyayyarsa da duk wani mai irin halayyarshi.
Yadda kuma ake ikirarin shi jinin Hajja ne baya magana biyu sai a gaya min in ni tawa uwar shege na tayi ta kawo muku".
Ya Rabi ta jinjina kai cikin kidima tana fadin.
"Babbar magana.
Ni na kawo kaina, dama ba yadda Hajja bata yi dani ba kar nazo ke mahaukaciya ce amma banji maganar uwata ba dole naji wohoho!
Sai ki mutu kuwa!
Muddin Fa'iz ya dawo kafarki-kafarshi zuwa Russia, wallahi nima na daina lallaminki, mu zuba mu dake aga wanda ya haifi wani.
Dabba kawai, shashasha, mara hankali".
Na ce, "Ko uwar Rasha ne ba zani ba, wallahi ba zani ba ko gunduwa-gunduwa za'ayi dani".
Rabi tayi dariya, "Ai har uwar Rashar ma zaki, tunda matukin jirgi kike aure ina ne ba za'a saka ki a jirgi a kaiki ba?"
Na ce, "Koda na rasa bawan Allah Dr.
Nazir, mai ilimin da ya amsa sunan ilimi, banga me zanyi da direba ba Ya Rabi.
Kamar ni in kare a mutumin da bai da ilimin komai sai na tuki?
Direban tasha, wallahi na yi asara!!!".
Rabi ta ce, "Kin kuwa yi asarar.
Yanzu ke ko babur zaki iya tukawa ne balle aje ga mota zuwa jirgi?
Ke kinga shegen bakin ki baya mutuwa, ni na gaji da magana don ba malamar jami'a bace.
Ranar da ki ka bi Fa'iz daga ke sai shi na tabbata murus bakin zai mutu mu don kin raina mu ne ki ka cika mana kunne da babatu.
Don haka sai anjima, mijina yana jirana.
Sai mun zo rakiya filin jirgi...".
Tamkar ta soka min mashi a kirji haka naji.
"Ko kuma an aiko muku da sakon mutuwar danku kunzo zaman makoki ba?