← Book details Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 27

Sashe 11

Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tabbas muddin na yarda na zauna da Fa
iz ko na saurari wata kalma daga gare shi ko da guda daya ce na tabbata wadda ba ta san ciwon kanta ba, ba ta san darajar kanta ba, ba ta san darajar wadda ta dauki cikinta wata tara ta haife ta shayar cikin wahala da kakani-kayi.

Muddin ban auri Dr.

N ba na cika butulu duba da tarin kauna da soyayyar da ya mallaka mani, na zama mayaudariya.

Ya zama dole kenan in kaskantar da kaina ga Fa
izu ya warware igiyar da aka zarga a tsakaninmu?

Juyawar da barin kaina yake yi ya tsananta cikin
yan dakiku, a yayin da zuciyata ta halarto min da cewa, rokon Fa
iz a bisa abin da bani da iko a kansa wannan dole ne!

Kaskantar da kai ya zama dole gare ni, tunda durkusawa wada ba gajiyawa bane.

Amma ba don ni ba illa don farin cikin Dr.

Nazir Sani Galadanci.
****
A washe garin ranar idanuwana na bisa kofa, yinin ranar zungur ban ko leko falo ba, illa kunnuwana da na kasa suna zuko min duk mai shigowa da mai fita a gidan Hajjah ko zan ji muryar Fa
izun?

Shiru!

Har yamma.

Kafin in ji Aliyu na ce da Hajjah
iz ya je Kano dauko Yaya Bashir
Hajja ta shigo dakin da nake kwance hannunta rike da kwano shake da gasasshen nama da ruwa-ruwan shi, an kuma barbade shi da yajin daddawa wanda ya ji kayan kamshin gargajiya mai dadi, ta zauna gefena a hankali da gani a darare take.

Allah sarki Hajjah!

Duk zagin da ta sha bai sa ta yi fushi dani ba don ina ji da safe tana gayawa bakinta
yan taya murna da suka zo mata daga Zaria, kada wanda ya shigo ya ta dani barci nake a barni na huta.

Ita kanta ta fada fiyat!

Kamar wadda ta tashi daga zazzabin kwana biyu.

Ta ce,
izah ki yiwa Allah ki bude ido ki ci naman nan, na san kina jina ba barci kike ba, tun asuba nake aikin gasa miki don na san shi akdai za ki iya ci tunda kin ki cin komi tun jiya, shin baki tsoron irin ciwon Aliyu ne?

Na yi mata banza na kara cusa kaina cikin filo na bude sabon kuka.

Hajjah ta yi zugum da kwano a cinya, daga bisani ta aje shi a kasa ta ce,
In kin kin cin abinci wanka fa Fa
izah?

Rabonki da wanka yau kwana hudu.

Shin Fa
izu ya san wainar da kike toyawa ma, in don shi kike yiwa kanki wannan ukubar?

Ban san sanda na zaro kai daga cikin filo ba na yi kutubal da shi na mike zauna, na ce,
Hajjah don na yi kyau, don na yi haske na daina kazanta na zama abin gani har a so ayi sha
awa Fa
iz ya ce miki yana son aure na ko?

To daga yau duk wani abu da ya shafi gyaran jiki zuwa wanka na barshi har abada!

Na koma Fa
izar da ya sanni a baya, kazama
yar Maimuna!!!

In ce dai in na shiga warin hammata da warin baki ya ce baya so, ya je ya auro
yar Rasha ni kuma a barni da mai sona tsakani da Allah ba don wani abu da na mallaka ba....

Na ci gaba da kuka na gasken-gaske.

Hajjah ta ce,
Ayya Fa
izah, kin yi kuskure babba, zato zunubi ko da ya kasance gaskiya.

Daga ranar da Hafizi ya bar Najeriya bai kara ganinki ba ko a hoto sai ranar da ya dawo bayan an daura muku aure
Da hanzari na tari numfashinta,
Tunda haka ne ki kwance auren mana ko dole ne?

Na ji ko da ban auri Dr.

Nazir ba na yarda na amince ki hada ni aure da Malam Hassan maigadin gidan Baban Kaduna, ko Isa direban gidan nann....

Hajjah kam ta koma yi min dariya, ta ce,
Yo ai shi kenan, wannan abu mai dan karen sauki.

Sai ki je wurin Hafizin ki amso takarda ki kawowa Ahmadu da ya kulla auren ku, ni kuma na yarda ayi aure da Malam Hassan maigadi tunda ai mutumin kirki ne bawan Allah, ko ba jinina bane na san asalinsa da tushensa, na zauna da shi tun ba a haifeku ba, babu cuta ba cutarwa
.

Ta mike ta fice ta bar kwanon naman a wurin yana ta turiri da kamshi.

Na dade ina juya maganar Hajjah bayan fitar ta.

Don me kowa na ce ya rabani aure da FA
IZU ABUBAKAR sai ya bude baki ya ce in amso takarda wurin sa?

Bayan suna da masaniyar cewa ba zan taba iya rokon Fa
iz wani abu ba, ko kalma ta hadani da shi a kafatanin rayuwata?

Ni na kai masa auren da zan je na karbo ba su suka kai ba?

Don me su ba za su je su karbo ba in har da gaske suke suna son gyara kuskure da laifin da suka yi mini wanda ba zan iya taba yafe shi ba ko in amince da shi?

Don me sai na karbo takardar aure zai warware ina ce in an maidawa Fa
iz sadakinshi shi kenan aure ya warware?

Cikin kuka na fitar rai mai soya zuciya na ce da Hajjah, a lokacin da na mike na bita har uwar dakin barcinta tana shirin ta da sallar walha.

To ki bani sadakin mana ki gani in ban mayar mishi ba?

Tana kokawar sanya hijabin sallarta ta ce cikin alamun nuna gajiyawa da magana daya,
Shin ni Hadiza meye nawa ne cikin lamarin nan Fa
izah?

Sadaki dai Barau ya karba, bayan daurin aure kuma ya dankawa ubanki na Zaria.

Saboda haka su za ki je ki yiwa wannan tijarar da kike yi mini amma ni in kika sa min hawan jini Allah zai saka mini....

Ta soma kokarin fashewa da kuka.

Na juya na fice da gudu na bar mata dakin tun Allah bai jeho wani cikin
yanta ya aika dani lahira ba tare da na kara sanya N.S a idanuna ba.
****
BIKI-BIDIRI
Ga al
adar mutanen Giwa da yammacin Laraba ne muke kamu, washe gari alhamis kuma ayi budar kai.

Don haka ban yi mamakin jin hargowar jama
armu ba daga ko ina cikin garin Giwa, Zaria, Kaduna da makotansu sun cika A.B Estate.

Masu kidan kwarya sun soma wasa korai da gyaran murya cikin lasifaka, masu guda na yi, maroka na ma Hajjah kirari duk inda ta gifta.

Na tabbatar dai al
amarin nan da nake dauka almara nema yake ya tabbata, za su hadani rayuwa da Ya Fa
iz ne ko babbaka su zan yi.

Lallashin ma babu mai lokacin yi min shi, shima Yaya Aliyun tun ranar da yasa kafa ya bar gidan ban kara jin ko tashin muryarsa ba.

Ummi da Zanirah babu wacce ta kara shiga sabgata, na kan ga dai Fa
iza
yar Zanirah ta rarrafo dakin da nake tana wasanta, ta yi ta gaji ta fita ko sanin da halittar dan Adam bana yi a dakin, domin ruhina da kulliyar tunanina baya wannan duniyar tamu, yana cikin wata duniya ta kunci, azaba da tafasar zuciya da zabalbalar kwallah.

A yau na yi amanna da cewa, zan zama matar Fa
iz in na bari tsofaffin nan suka shafa min lalle.

Na yi tunani iyaka tunani bani da mafita, bani da mai mara min baya, babu mai duban hujjata da idanun basira in dai a kan Fa
izu Abubakar ne.

Wani yaro cikin
ya da jikoki da suke matukar so duk da tarin aibobinsa.

Don haka na yakewa kaina mafita ta karshe.

Na janyo (travelling bag) dina na shiga shirya kayana da ba za suyi min wahalar dauka ba a gurguje.

Adda Hanne kanwar Maman Kaduna da tawagarsu suka yane labule suka shigo da guda da sallama, duk suka cika dakin taf!

Tsokanar duniya babu irin wacce basu yi min ba, in gadon dakin ya daga ido ya dube su to nima hakan.

Kaya nake ninkewa daga sif ina dannawa a jaka.

Adda Hannatu ta yi kwafa ta ce,
yar tawaye, mun zo kama ki ne kinyi kamar baki ganmu ba saboda kin isa
A yayin da ta bincire hancin kwalbar turare
intimately beckham
suna ta raha suna darawa cike da unexpressable nishadi da farin ciki bayyananne a zuciyar su da fuskokinsu.

Na dago jajayen kumburarrun idanuna na yi musu wani kallo a kaikace ta kasa-kasan ido a hankali na ce,
Ku kama uwarku dai
.

A yayin da na sunto dankwalin kaina na yi damara a kugu gashina dake daure cikin (bound) ya sunce gaba daya ya cika fuskata da wuyana baki daya, ban damu ba, ban kula ba, jikina har tsuma yake ina jiran mai kwarin kashin da za ta fara matsowa gare ni.

Adda Hannatu ta ce,
Eye!

Dambe za ki yi damu Fa
izah!

Lallai da aka ce kin haukace ashe ba ayi kuskure ba.

To bismillah ma ga mai kwarin kashi tsakanin ni da ke
Zaneerah cikin zafin cewa da na yi su kama uwarsu ta ce,
Eh, uwarmu zamu kama mana, tunda dai babban Yaya uba ne kamar yadda matar babban Yaya ta zama UWA...... wadda za ta cika mana gida da
ya ta sauke tukunya ta dora mana abinci...... ta sa mana kula ta sabe mana babbar riga ta yiwa
yanmu tarbiyyah irin ta gidanmu ba irin tata ta rashin neman albarkar iyaye da son gamawa da duniya lafiya ba.......

Daga haka suka shiga kwararo min turaruka ta ko
ina gaba da bayana har tsakar kaina zuwa yatsan kafata, har kuma cikin idanuna.

Ashe dama kowaccensu da guzurin abinta cikin mayafi, ba Adda Hanne kadai ba.

Azabar turare cikin kwayar idona ta rudani ta gigita ni na soma kara ina murza idanun da dukkan hannuwana, ina fadin
Idona.... idona..... wayyo Hajjah sun fasa min ido
In sun fasa to ke da baki nan kin fasa karatun nan, sai dariyarsu suke.

Kasa na sulale na kwanta ina birgima ina murzar ido dake neman tsiyayewa.

Sai da suka kusa karar da kwalabensu kana na sha duka kitif-kitif-kitif daga hannun kowaccensu, wai ban yi wanka da kwalliyar tarbarsu ba sai zagin da na yi musu guzuri da shi.
Chapter 11 · 0% Book details