← Book details Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 27

Sashe 26

Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zauna hira za muyi kafin su Momi su dawo".

Walida a daburce take, ya jata suka isa har gefen gadon da nake kwance suka zauna har rigarshi ta rufe min kafa kadan.

In banda kamshin sassanyan turaren shi ba abinda ke tashi a dakin.

Ya bige da tambayar Walida sha'anin makaranta tana bashi amsa a darare, kokarin zamewa take ta barmu yana kara shimfido mata tambayoyi akanta da kannenta su Waild, Kausar da yayanta Abdallah da nasu karatun.

Ganin ba zai barta ta tafi ba ta ce, "Yaya Fa'iz bari in kawo maka ruwa da lemo in kaiwa yaya Shu'aib abinci falo".

Ya ce, "Kada ki damu Walida, na cika cikina a Kaduna, haka shima Shu'aib.

Yaushe Momi za ta dawo?"
Walida ta kalli inda nake bamu hada ido ba, amma taga yadda kwayar idanuna suka kada suka yi jajawur, numfashina ke sauka da sauri-da-sauri har wani irin huci nake kamar mesa babu rahma cikin su dai-dai da kwayar zarrah.

Walida ta kara rudewa ta ce, "Na jona ruwa a (heater) Yaya Fa'iz ka barni inje in kashe kada ya kone fada Momi zata yi min".

Ya ce, "To kiyi sauri nima ba zama zanyi ba, sako zan baki wurin Momi sai mu wuce".

Ta ce, "Toh".

Da saurinta ta fice har tana sake tuntube da dokin kofa.

Ya girgiza kai ya mike ya sauke ido a kaina, tsayin mintuna biyu yana kallona kawai babu ko kiftawa.

Nima kallonsa nake, wani irin kallo da ni kaina na kasa fassara shi, na takaici ne ko na kiyayya koko na gara da Allah Ya kawo ka?

Ni kaina ban sani ba.

Daga ni har shi babu mai niyyar daina kallon, duk da shima na kasa fassara nashi kallon.

Shi ba kallon so ba, ba na kiyayya ba, ba na jin haushi ba.

Yafi kama da kallon iko da raini.

Ta wani fannin tamkar kallon, "Baki da yadda za kiyi dani" koko kallon "Nafi karfinki da ke da duk abinda kike takama da shi.
(In another notion) kallo ne na "Yarinya na ci dubu sai ceto, kiyi duk abinda za kiyi" Sai da ya mula don kansa ya ce.

"To ni Aunty Fa'izah zan wuce Giwa, tunda na iso Hajjah bata ganni ba, lefenki na kawo miki, wanda kowa ya kasa kawo miki tunda kin zama Faskari, mai faskarawa mutane kai.

Sai tsarabar da nayo miki a tafiyar da nayi, tunda babu gaisuwa ko ta Musulunci a tsakaninmu.

Daman nazo ne in shaida miki zaman nan ya isa haka!

Ranar (monday) kwana ki shidda kenan masu zuwa ki kimtsa kayanki da duk abinda kike bukata za ki tare a gidanki kamar sauran 'yan uwanki, don gaskiya fisabilillahi kin takurawa su Momi da alama har su Walida kin takura musu, nima kuma kin takura min.

Haka kawai ina da mata amma bani da maraba da gwauro.

Gara mu kauce haka muma mu manta komi, da duk abinda ya faru a baya, mu fuskanci sabuwar rayuwar dake tunkaro mu, muka kuma bude ido rana daya muka ganmu cikinta.

Wato rayuwar aure.

Sai mu rungumeta, mu kasance cikin godiyar Ubangiji da neman dacewa duniya da lahira".

Da ace Fa'iz yasan tashin hankali da bala'in da kalaman dake fita daga bakinsa suke kara jefani da ko da wuka a makoshi bai yi gigin furta su ba.

Domin kalamai ne da ban taba jin mafi muninsu a duniya ta ba. (Hada rayuwa ta har abada da shi FA'iZ-ABUBAKAR) koko ince makiyina.

Mugun dan uwa da kullum ketowar alfijir da faduwar rana sai nayi dakacen INAMA ban hada jini da shi ba.

Wani kwayan mutum guda daya da ya maida mahaifiyata marainiyar wayonsa, ya maida ni kwallon takawarsa a duk sanda ya so, ko gare-gare abin wasan yara.

Mikewa nayi gaba daya na littafin KWANA SITTIN ya fado daga ruwan cikina, na ce.

"Da uwar wa zaka tafi wurin direbancin?"
Tsalle daya nayi sai gani a bakin kofar dakin nayi maza na rufe na murza 'key' na zare shi na cilla shi waje ta taga cikin wani irin zafin nama da ni kaina ban san inada shi ba.

Ya yi maza shima ya cafe mukullin cikin irin nashi (exceptional) zafin naman wanda yafi nawa kafin ya kai ga ficewa ta tagar.

Ya shiga sosa keya da (key) din ya daure fuska sosai kamar ba shi ne ya gama maganar da yayi cikin raha ba.

"Meye haka?

Gafara ki bani hanya na wuce".

Na ce, "Wucewa kam zaka yi ta, tunda har ka yi nasarar amsar mukulli.

Amman fa bayan rubutun saki uku ris a gareni FA'IZA A.A GIWA".

Murmushi ya yi, "Wannan ne kuma ba zaki samu ba har abada Fa'izah, har kuma yaumil-ardhi.

Domin ban aureki don in saki ba.

In haka ne tun farko ba zan fara ba.

Karewa ma, ni ba lallaminki nazo yi ba kamar wancan karon, UMARNI ne ki hada kayanki ranar litinin za ki tare a gidanki kamar kowacce mace mai aure.

Ba kuma neman afuwarki ko kiyi min uziri nazo ba tunda ke abu ba ya karewa a wajenki kamar cin kwan makauniya.

Ki matsa na ce, tun hannuna bai kai fuskarki ya yi mata tabon da bata da shi ba...".

Sunkuyawa nayi kafin ya kai karshen maganarsa na dauko littafin da Walida ta kammala rubutu dasu, na yago takarda a ciki na mika mishi.

"Ko da can babu wani wasa makamancin 'game' ko 'April-fool' da ya taba shiga tsakaninmu balle yanzu da kowannen mu ya mallaki hankalin kansa.

Za ka wuce din babu haufi, kuma babu makawa, amma fa bayan ka yi rubutun nan".

Na sake mika masa takarda.

Fa'iz ya sanya (key) cikin aljihun kaftanin shaddar dake jikinsa.

"Kenan har wani hankali kika mallaka yanzun?

Ko daya!

Kina nan yadda kike; Jiya 'i yau, kazama, dakikiya, 'yar kauye, mummuna.

Don haka daina cewa wani wai kin mallaki hankali, ina hankalin yake nan kana tura kanka cikin jahannama kana ji kana gani?"
Na ce "In shiga wutar mana, tunda ba tare za'a sanya mu ba ina ruwanka?"
Ya ce, "Naga alama abin naki nema yake ya wuce na rannan, to ba zan rubuta ba kiyi duk abinda za kiyi".

Anan kam dankwalina na janyo nayi dammara dashi a kuguna kamar wata sabon hauka, na doshi Fa'iz da takarda har na iso gabansa.

Sai dai kuma zuciyata cike da taraddadin murdaddun damatsan Fa'iz da na hango ta cikin kayan jikinsa.

Ina tunanin idan ya cafke ni da su wa zai kwace ni?

Babu kowa a gidan sai yara na kuma kama kofa na kulle?

Da alama shima ya shirya yau.

Idona ya kyallo min biro a aljihun gaban rigarsa, na cizgo shi, na matsa gabanshi sosai har muna iya jin hucin numfashin juna.

Kallon zakaru masu shirin dambacewa muka tsaya muna yiwa juna.

Sai na samu kaina da ganin wautata anan, shin in nayi duka ta ina zai shigi wannan 'giant' din?

Fa'iz kato ne sosai mai tsayi da kauri, kaurin da ba kiba ke haifar dashi ba 'diet' ne da hutu na yanayin rayuwa mai nagarta.

Don haka na fashe da kuka tabbacin Fa'izun yafi karfina kamar yadda ya ce, babu yadda zanyi dashi.

Sai na ce a raina.

"bari kawai kaifin harshe na ya zama makamaina".

Cikin kuka na ci kwalarshi amma fa kada ki so ki tona bugun da zuciyata ke yi, na ce.

"Idan har ka haifu cikin uwa da ubanka ka rubuta min takardar nan Fa'iz...".

Ban kai karshen kalamina ba ya fidda hannu ya shimfida min wasu irin gigitattun mari hagu da dama.

Na nemi ji na da ganina na wucin-gadi na rasa.

Naga giftawar wasu taurari masu hasken dake tafiyar da ganin dan-Adam na lokaci mai tsawo, ji kake fauuu! fauu!! fau!!!

Yasa tsayayyun kafadunshi ya ingije ni gefe guda na fadi warwas akan dandagaryar kafet.

Ya nufi kofa ya zaro dan mukullin a aljuihunshi yana kokarin sanyawa jikin kofar, nayi kukan kura na wawuri abin zaman kwalliya (stool) na jefe shi dashi, ya same shi a baya.

Yasa hannu ya rike kafadarshi ya kuma juyo cikin dan bude ido ya ce.

"Kin gama?"
Na tsala ihu na taso nayi kanshi da duka da duk iyakacin karfina da hannayena hagu da dama.

Ganin duka wannan bai min ba, domin kamar ba jikinsa nake duka ba, sai na kai kaifafan hakorana damtsenshi shi, cewa yake.

"Fa'izah baki da hankali ko?"
Irin bude kofar da aka yi ba zato ya sanya Fa'iz hankadani tsakiyar gado wanda ke nufin da can dukan nawa da cizon nawa bai dameshi ba sai gudun kada a shigo a ga ina dukanshi.

Gaba dayanmu muka bi kofar da kallo cikin firgita.

BABA NE!

Ya ce, "Kai amma Fa'izu anyi sullutun banza!

Ka tsaya kanwar bayan ka na lallasa ka kana tsaye sororo, shashasha, sahorami".

Cikin kuka na ce, "Baba shi fa ya mareni, yayi min dukan tsiya har da rufe kofa don ma kada wani yazo ya taimakeni, dubi yadda ya dauki tebirin nan ya kwada mini a baya...".

Baba kam bai tsaya saurarona ba ni da karerayi na ya dauko dorinar da yakewa su Walida barazana da ita in sunyi laifi yayo kaina.

Fa'iz ya kama bulalar da karfi ya rike, ya ce.

"Haba Baba!

In Fa'izah na haukan shirmenta bai dace kowa ya biye mata ba".

Na ce cikin gunjin kuka, "Kai ne shirmammen, mahaukacin,
amma ni lafiyata kalau".

Baba ya yi salati, ya fisge bulalar daga hannun Fa'iz ya shiga tsula mini ta ko'ina ina ihu ina zagin Fa'iz ban fasa ba.

Fa'iz ya sake damke bulalar ya ce, "Baba ya isa haka nan.

Ka yiwa Allah da darajar marigayi kayi hakuri".

Idanun Baba sun rine da bakin ciki da takaici, ya ce.

"Fa'iz ko ka cikani ko in kakkarya Fa'izah da hannuna, ina amfanin wannan jarababbiyar yarinya cikin A.B?"
Ya fisge bulalar daga hannunshi, ya ci gaba da shimfida mini da iyakacin karfinshi.

Da Fa'iz yaga Baba na shirin illata ni (and he has no regret for it) Sai ya fado kaina gaba daya yayi min rumfa da faffadan kafadunshi, ya zagaye ni da hannayenshi ya rungume ya ce.

"Sai dai ka nakasta mu tare Baba!

Amma ba zan zuba ido a kashe Fa'izah akan gaskiyarta ba!!".
Chapter 26 · 0% Book details