← Book details Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 27

Sashe 13

Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki rufa min asiri Walida, shin Baba na gida?"
Ta girgiza kai.

"Momi fa?"
Ta nuna min (kitchen).

Na ce, "To don Allah Walida kar ki gayawa kowa ina cikin gidan nan, zan zauna xakin Abdallah, ai yana makarantar kwana ko?"
Ta gyada kai tare da leqawa ciki ta tabbatar momi firar doya take, tayi min alamar in shiga.

A hankali ta murda qofar dakin Abdallah na shige wanda ke daga can gefen tafkeken falon, ta mayar ta rufe kenan Momi ta qwala mata kira.

"Walidaa!".

Ta ruga a guje tana faxin.

"Yes Momi".

Momi ta ce, "Ke da wane a waje ku ke magana?"
Ta dan diririce na rashin sabo da yin qarya, kafin ta ce.

"Joseph ne yake neman Cinyere na ce bata zo ba".

Ba tare da ta juyo ta dubeta ba ta ce.

"Ga abincin ku can kan leda ki ta da Walid ku ci, ya yi bacci ko?"
Ta ce, "Kai Momi, ki qyale shi ya fa sha kunun tsamiya mai yawa kafin ya yi baccin".

Ta juya don ta kira Kausar ta tarar tayi bacci akan litattafanta itama, ta gayawa Momi kana ta dauki plate din ta bude qofar a hankali ta shigo.

Nayi tagumi ne a gefen gadon Abdallah na zubawa kayana ido, da 'yar muryarta mai sanyi ta ce.

"Yaya Fa'izah".

Tare da zama a kusa dani, ta dora hannunta bisa cinyoyina.

"Wai shin me ke faruwa ne?

Duk akan auren ki da Ya Fa'iz ne?"
Na share hawayen da suka cika mini ido, na ce.

"Shin Walida kin mance sanda Fa'iz ke azabtar dani ne?

Sharri kala-kala da azabobi iri-iri wanne ne Fa'iz bai min ba, bai kuma gana min ba?

Qiyayyar duniya wacce iri ce Fa'iz bai min ba?

Amma ki ga don zalinci ya zo ya kalallame Hajja da su Baba suka xaura mana aure...".

Wasu azababbun hawaye suka mirgino akan kundukukina.

"Don haka ni kam Walida anan zan ci gaba da voyewa har zuwa sanda suka gaji da nemana suka warware auren nan, ko kuma su kai gawata idan baqin ciki ya qarasa ni, da dai in zauna ayi bikin nan jibi...".

Na ci gaba da share hawaye ina fyace majinar dake ambaliya daga hanci na.

Walida tayi zuru tana kallona.

Da alamun tayi nisa a tunani.

Ni na san Walida yarinya ce mai kaifin basira duk da kasancewarta mai qarancin shekaru, kwata-kwata bana ji ta cika shekaru goma sha huxu.

Wala'Allah abinda take saqawa ya zam mai amfani a gareni.

Ta ce, "Yaya Fa'izah, ban zauna a Giwa ba ko kaxan balle in san halin Ya Fa'iz a da can, ko rayuwar da ku ka yi tare, bana ma kuma marmarin zaman, sai dai nakan ji ana labarin a cikin 'yan uwa ko in munje gidan Baban Kaduna ko yaro ne ya takurawa xaya sai kiji manya na faxin, "Kada ku zama Fa'iz da Fa'izah mana, kuyi riqo da ZUMUNTAR ku".

Sai dai wallahi a yadda Baba ke son auren nan naku ya kuma dage ya tsaya wajen ganin wanzuwar sa na rantse duk inda ki ke sai ya nemo ki, balle cikin gidansa.

Ni kam banga abin ta da hankali da qin Ya Fa'iz ba, da kin xora idonki bisan Pilot Fa'iz Giwa a akwatin talabijin sanda aka nuno shi a tashar CNN, ranar da wani jirgi ya faxi a Mozambique da kinyi alfahari da kasancewar shi miji a gare ki.

Wanda ba isarki ko cancantar ki ce ta baki shi ba, face darajar Zumuncin da kasancewar ku JINI XAYA.

Miji ne na liqawa a goshi, kuma abin tinqahon kowacce xiya macen da ta san ciwon kanta.

Da kinyi nadamar wannan azabtar da kankin da tada haqarqarin da kike yi kan wai ba kya son sa.

Ko kin san Ya Fa'iz na yanzu bai yi kama da Fa'izun gidan Baban Kaduna ba na da can da kika sani a baya?

Wallahi in banda Fa'iz ke son ki, da na ce yafi qarfinki a halin yanzu kam!

Umm!!

Ni dai ina baki shawarar ki haqura ki fauwalawa Allah al'amarinsa da yinsa, kada ki zamo mai shisshigi cikin iyakar Ubangiji, wato yarda da qaddara mai daxi ko mara daxi.

Wallahi Yaya Fa'izah ni shaqiqiyar ki ce, don haka ba fata nake miki ba, muddin yaya Fa'iz ya barki ba za ki samu ko da wanda ya kama qafarsa ba...".

"Ni kam na shiga uku!!!".

Abinda na faxi kenan a fili kamar in xora hannuwa aka in fasa kururuwa.

Me yasa kowa ba ya ganin hujjata da qima, girma da muhimmanci?

Me yasa kowa ke son Fa'iz?

Me yasa kowa ya buxe baki yabon Fa'iz yake yi?

Sun manta cewa maqiyinka baya tava dawowa ya zama masoyinka?

Wanda ya ce bai son ka jiya, gobe ya ce yana sonka to tabbata wani abin ya hango.

Na dubi Walida cikin matsanancin vacin rai a ido da zuciyata, na ce.

"Yau na amince kina daga cikin maqiyana Walida!

Kin nuna min ba ki qaunata Fa'iz kike so kamar sauran dangi, kema kina cikin sahun su Ummi, Hajja da Zaneera...

Yaya Aliyu kaxai ke sona har gobe cikin A.B, kin kuma nuna min kema......".

"...Walidaaa!".

Momi ke qwala kira.

Walida ta miqe a razane, a kixime muryarta na rawa ta ce.

"Wallahi-wallahi daga yau ina bayanki Yaya Fa'iza... tunda har baki son Yaya Fa'iz har haka, nima daga yau na tsane shi... na tsane shi!!!".

Wani irin murmushin qaunar 'yar uwata ya suvuce a fuskata irin wanda ke fitowa tun daga qarqashin zuciya, itama murmushin tayi mini.

"Daure ki ci abinci Ya Fa'iza, zan ke kawo miki abinci ko yaushe.

Don Allah ki daina kuka.

In kinga ban shigo ba to ina makaranta ne boko ko Islamiyya. (Toilet) xin Abdallah a buxe yake, kuma famfo yana zuwa".

Ta fice da sauri ta ja qofar ta tadda Momi, ina jiyo Momi na faxin.

"Me kike a xakin Abdallah tun xazu ina ta kira?"
Ta ce, "Momi littafina da ya ara nake nema "An African Night Entertaiment" nake jin ma ya tafi da shi".

Shigowar Baba ya katse su.

Na xauki kwanon abincin da Walida ta kawo mini nayi loma guda na sakwara da miyar Ugu.

Tamkar nayi loma da curarren maxaci duk da zaqin nama da na mai tauraro da miyar tayi cau.

Yadda zuciyata take baqiqqirin haka bakina yake xaci xau.

Na runtse ido na a hankali na kishingixa bisa gadon Abdallah tare da jan bargo har kaina, sakamakon wani irin sanyi da naji yana ratsa qasusuwana, yana son shiga har cikin bargo na alamar shigar zazzavi.

Zuciyata na wani irin tuquqi, maqaqi da azalzalar baqin-cikin da ba zan iya kwatantawa ba.
*****
A GIWA
Acan Gida babu wanda ya farga da rashina a gidan har garin Allah Ya waye, duk jama'ar gidan baqi da 'yan gidan kowa harkar gabansa yake yi, ana ta shirye-shirye.

Musamman kasancewar ranar ta Alhamis a matsayin ranar buxar kai.

Aliyu ne ya shigo falon Hajjah tare da xan uwanshi kuma babban abokinshi, wato Muftahun Yaya Rabi da ya zo a lokacin don su gaisa da Hajja, isowar shi Giwa kenan.

A babban falon dake shaqe da A.B family maza da mata, Muftahu ya zo ne da labarin rasuwar Dr.

Nazir Sani Galadanci, manemin auren Fa'izah.

In banda Salati babu abinda Yaya Aliyu keyi yana mai qara jinjina wannan mummunan labarin, tare da qara tsinkewa da al'amarin Ubangiji.

Muftahu ya nemi ganina don yi min bayani, Ummi dake kokawa mutuwar Naziru haiqan har kamar ta shixe ta yarfe hawaye da majina, ta ce.

"A wannan halin da Fa'iza ke ciki ne zaka ba ta labarin rasuwar Dr.

Nazir Yaya Muftahu?

Ka rufawa kanka asiri, idan Fa'izah bata ce kai ka kashe mata Nazir ba, la-shakka zata ce haxa baki ku kayi aka kashe Naziru don ta yarda da auren Ya Fa'iz".

Muftahu ya ce, " amman dole ne ta ji?"
Ummi ta ce, "Ji kam ya zama dole ko ba jima ko ba daxe, amma ba yanzu ba, kuma ba daga bakin kowa ba sai na wanda zai iya ma haukar Fa'izah tamkar Yaya Aliyu ko Ya Rabi, amma ba kai ba".

Da sauri Aliyu Na'ibi ya ce, "Wallahi babu ruwana, ba a bakina ba nima, indai har ka dage sai ka faxan Muftahu ga hanya, tana uwar xakinsu tana neman kashe kanta don bala'i da qin auren Fa'iz ko falo ba ta fitowa".

Muftahu ya ce, "Bari inje, inji dai ba zata bugeni ko ta zage ni ba?" Suka ce a tare, "Uhm!".

Hajja ta ce, "Muftahu ka qyale Fa'izah don Allah, shin Fa'izar da ta rufe ido ta zageni tas kan Naziru kai waye da bazata zage ka ba, zaka je mata da labarin mutuwar Nazirun?"
Muftahu bai tsaya ba a yayin da ya danna kanshi a xakin bakinsa xauke da qatuwar sallama.

Ya yi dube-dubenshi ya fito, ya ce.

"Au, ai ma bata nan".

Ummi ta ce, "Ko dai ta shiga bayan gida?"
Ya ce, "Ga bayan gidan nan a hangame, ai babu kowa a ciki".

Ta ce, "Duba sosai dai can qarshen gado ko ta naxe cikin bargo".

Muftahu ya yi dube-dubensa har da duba qasan gado ya kuma haxa da kira.

"'Yar Zaria a Kano!!!".

Shiru ta ziyarce su, sai ma amsa kuwwar muryarsa da ta dawo cikin kunnensa.

Ya ce, "To wataqila dai idona ne, Aliyu zo ka duba".

Baki xayansu suka miqe suka shiga xakin inda Fa'izah ta ce xaukar ni inda ku ka ajeni.

Zaneera sai da ta qara shiga (toilet) ta duba bayan qyaure da cikin baho, ta ce.

"Kai!

Tikisa!!

Da qyar fa idan Fa'izah na cikin xakin nan".

Leqa nan leqa can cikin A.

B Estate baki xaya babu Fa'izah.

Hajja ta tuna kalaman Fa'izah.

"Daga yau ba za ki sake ganina cikin gidanki ba balle ki yi iko da ni...".

Hajja ta fashe da kuka tana faxin.

"Ni Dijah na shiga uku, wace irin zuciya ke da yarinyar nan wadda babu ahuwa da rangwame a cikinta?

Tabbas Fa'izah ta gudu ne, ba ta gidan nan, ba ta garin nan".

Zaneerah ta ce, "Ina!

Babu inda Fa'izah za ta iya zuwa da ya wuce Kaduna, Kano ko Zaria.
Chapter 13 · 0% Book details