Sashe 25
Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ki sani, ranar da duk Fa'izu ya yi gigin sake sako kafarshi cikin gidanmu kamar yadda na dauke kafata daga nasu gidan, wallahi sai buzunsa Ya Rabi!".
Ta ce, "Ko?
Lallai kin fitsare, inama ina nan za'ayi wannan (BOXING)?
Kai da na kadawa (Winner) tuta.
In kuma kanwar ta kar tsamin ne sai kiyo min waya inzo jinyarki".
Zaman Zaria fa yayi min zafi, Walida, Abdallah duk suna makarantar kwana.
Kausar da Walid makaranta suke zuwa safe da yamma.
Babu Ummi babu Zanirah balle tsohuwa Hajjah mai samu farin ciki.
Ko da yake Hajjah ni na gujeta don a ganina ita ce ummul-haba'isin sanya rayuwata cikin halin kuncin da take ciki bayan shafa min bakin jini da hakan ya yi a idanun iyaye da 'yan uwana.
Daga uwata har ubana kowa fushi yake dani, Walida kadai ke kula ni a gidan, haka nan kullum Baba zai fita sai ya ce.
"Tunda haka kike so, wato ga dakin uwarki ga naki, inta wuce dakina ki bita da ido kina kissime-kissime ai sai kiyi ta zama".
Wannan magana ba karamin kona min rai take yi ba, tun ina kuka har na saba.
A zuciyata kuwa Allah Ya isa ga Fa'iz tafi dubu biyar.
Na rame, na fige, na zama 'yar firit dama jikin ba wani jiki ba.
Nayi niyyar komawa Giwa amma na kasa saboda kurarin da nayi a baya cewa ba zan sake zuwa gidan Hajjah ba.
Wuri daya ne nake tunanin idan naje zanji sanyi, wato wurin Maman Kaduna, to amma in ina da kunya ai bana dosheta ba alhalin kiyayyar danta na neman zauta ni.
Ko babu komi ranar da Fa'izun ya ga damar dawowa me na isa nayi mishi akan idon uwarsa?
Gara dai ya kwaso jiki ya kawo namu gidan.
Haka Zanirah da Aliyu suka yo min waya wai hakuri suke bani abinda suka yi min ranar bikinmu a Giwa su wasa ne suke min.
Tsaki nayi na kife wayar nayi tagumi da hannu bibbiyu.
Bayan kwana biyu kuma, sai Ummi da Bashir suma suka bugo, amma su ba hakurin suke bani ba, korafi suke wai naki inje inga gidansu, to inzo in raka Ummi awo tana da ciki dan sati biyu.
Na ce, "Sai ku bari ya cika wata daya tukunna mu fara zuwa awo, kunji ko 'yan abu kazan uba marassa kunya".
Ummi ta ce, "Da fatan (this very big) ashar (is for me alone not with my husband) don mu albarkar miji muke nema ba ma zaginsa".
Watanni biyu suka shude tun ana zuba ido har kowa ya gaji babu Fa'iz babu duriyarshi, babu ko wayarsa.
Don haka na yanke shawarar tunkarar Baba da shawarar da na yanke, wato komawa karatuna a Kano.
Da farko baban ya fara ne da zunduma min zagi bayan ya gama saurarona, kana ya ce.
"Sai dai in karuwanci kuma za ki sannan in barki, tunda kin ki zaman aure.
Sannan ina mai tabbatar miki muddin ya kasance wani mummunan abu ne ya samu Fa'iz sakamakon raunin da kika yi mishi da kwalba, to ki tabbata sai na rotsa miki kwalbar 7up a wannan kodaddiyar fuskar da kike tinkaho da ita.
Kazalika in Fa'iz yayi zuciya ne yaga cewa gara ya fasa auren, sai na dauke ki ke da kayanki na kai mishi sadaka, ko aikace-aikacen gida ne kiyi masa.
****
A WALES (UK)
A bakin wani (swimming pool) dake cikin hotel din da suke ciki cikin birnin Wales din kasar Ingila, bisa fararen kujeru da
yar jar lema da tayiwa kujerun inuwa ta rage hasken hantsi daga idanuwan wadanda ke zaune cikinta.
Pilot Fa'iz Giwa ne da Maajid da Johari tare da wasu abokan su wadanda duka matuka jirgin sama ne ke zaune suna karya kumallo bayan sun fito daga (interview) din da ta kawo su kasar Ingila da British Airlines.
Maajid na shan (tea) cikin wani kankanin kofi, amma hankalin shi naga Fa'iz dake faman juya cokali cikin (coffee) mai zafi idon shi na kan wata siririyar baturiya dake sanye cikin dan kamfe da 'bra' kadai, tana tafiya lange-lange kamar zata karye saboda rashin kauri da kumari ko kuwa kamar da an busheta da baki zata fadi don sirinta.
Amma a zahiri, idan ka dubi cikin kwayar idanunsa ba ita yake kallo ba, idanunshi ne kawai a saitin da take, tsabar tunani ke jagwalgwala kwakwalwarshi wanda kuma ke neman fitar da shi daga duk wani jin dadi da yake ciki ya kuma zamo barazana kuma ga walwala da farin-cikin sa, harma da nutsuwarsa da hayyacinsa cikin duk al'amuran da yake gabatarwa tun barowarshi gida wanda ba wani abu bane face kanwarsa/matarsa FA'IZAH A.A GIWA.
Wadda damuwa da al'amarinta da neman sanin hanyar warwarewar damuwar al'amarinta da shi ya zamo wani abu kadai da ya tsaya ya yi karantsaye ya addabi rayuwarsa.
Har yake neman zautashi ba don ya kasance jarumi akan komai ba musamman wajen shanye damuwa komin girmanta.
(Still) idanunshi na kan Ba'ireshiyar cikin rashin sanin abinda yake yi ya dauki attaruhun kwalba ba tare da ya ankara ba ya zuba cikin kofin Gahwarsa ga zatonsa sukari ne yake zubawa.
Maajid na kallon shi bai hana shi ba sai ido da ya gwalo kamar za su fada cikin kofin shayinsa.
Pilot Javed Saddyqy ya dubi Maajid cikin yamutsa fuska tare da nuna Fa'iz din da abinda yake yi da baki.
Maajid ya kada masa ido alamar ya kyale shi.
Idon shi daina kan Baturiya wadda ke ta faman yi mishi gizo da Fa'izah surarta na rikidewa tana zama Fa'izah.
Ya sake daukar cokali ya motsa shayin yana shirin kaiwa bakinsa.
Anan ne Suhayl Khan mutumin India ya ce da Saddiqy wanda shima Ba'indiyen ne cikin harshen Tamil.
"Fa'iz ya samu makuwa ne halan?"
Alama Saddyqy yayi mishi ta yayi shiru ta hanyar daura dan yatsarsa bisa lebensa, a lokacin yana rike da kofin ne a hannunsa amma tsayin mintuna uku bai kurba ba idanunshi akan Baturiya.
Anan sai Javed ya sanya kafa ya dan take mishi yatsun kafarshi dake kusa da tasa, ya ce.
"Ba zaka sha bane?"
Fa'iz ya kai kofi da azama bakinshi ya yi mishi kyakkyawar zuka.
Ba shiri ya saki kofin a kan tebirin ya ce.
"Aaah!".
Suka kwashe da dariya gaba daya, wadda zafin gahwah da zafin attaruhu suka hadu suka hana Fa'iz jinta duk da karfinta (dariyar tasu).
Maajid ya samu abinda yake so, ya buga tebirin da hannunsa da karfi yana fadin.
" Woman na nufin WO!
MAN, ka shiga uku kenan.
In har baka dauko Fa'izah ba kun zauna a garin nan tare Fa'iz kai ba namiji bane ungulu ne da kan zabo, duk wannan cika da batsewar naka
[6/3, 4:13 pm] Takori: ****
A ZARIA
A wannan rana wadda ta kasances asabar din karshen watan Agusta cikin 'Area One', Walida da Abdallah duka suna gida sunzo hutun karshen zangon karatu na biyu daga makarantun su daban-daban.
Ina kwance cikin dakin Walida wanda yanzu ya zama nawa tunda ita ba zaman gidan take ba, sanye da riga da zani na atamfa mai karshen tsada (Exclusive Sharaton) ruwan ganye mai ratsin hoda, kaina ban daura kallabin atamfar ba yana dai ajje gefen gadon, na hade gashin kaina cikin tafkeken 'hair-bound ina karanta sabon littafin Takori ne mai suna 'KWANA SITTIN'.
Zuciyata ta tafi gaba daya cikin rayuwar (schezophrenic_Safeenah) mai tsananin ban tausayi.
A wani bangaren, ba Safeenar nake tausayawa ba kamar Kabir Danbatta, na rasa shi da Dr.
Dangi wa yafi dacewa da amsar ragamar rayuwar Safeenah?
Kowannen su masoyinta ne na hakika.
Muryar oyoyon da Walida ke yi ya katse min karatun, na bi hadaddun jakunkunan da Shu'aib ke shigowa da su dakin namu yana dora daya kan daya da kallo ina kissimawa cikin raina, wane irin baki ne muka yi masu tafe da jakunkuna 'classic' haka kuma har dozen?
To kwana nawa suke nufin za suyi a gidan namu?
Kamshin sassanyan turaren (212) na maza ya sirnano cikin hancina, wani irin kamshi da ban taba jin mai sanyi da dadinsa a duniya ba.
Wadanne irin baki ne momi tayi haka?
Abinda nake tambayar kaina kenan.
Daga inda nake kwance na jiyo muryar ma'abociyar ginshira, na tambayar Walida ina Momi da Baba?
Walida ta ce, "Momi na gurin aiki, Baba na cikin makaranta.
Amma Yaya Fa'izar tana ciki tana karatu".
Da murmushi fal a fuskarsa ya ce.
"Karatu?
Ko dai kuka Walida?"
Ta ce, "Wallahi karatu take, kullum ma karatu take, ta je kasuwa ta sayo littattafan TAKORI na da dana yanzu, su take karantawa kullum, ta daina kukan tuni...".
Muryar FA'IZ, FA'IZ GIWA, FA'IZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA!
Da kwarin gwiwarsa ya yi sallama a dakin cikin 'husky voice' din da Allah Ya yi musu baiwarta zuri'ar Abubakar Bamalli Giwa bakidaya.
Ya samu wannan kwarin gwiwar ne daga labarin da ya samu a bakin Walida masu nuna na kwantar da hankalina tunda har ina karatu?
Duk da kwakwalwarsa bata fahimci littattafan TAKORIN da Walida take bayani akai ba, ya dai fahimci NOVELS ne wanda ba zai ce na Hausa ne, na Turanci ko na Larabci ba, tunda bai san mene ne ma'anar TAKORIN ba, bai ma taba jin kalmar ba cikin kowanne yaren.
Abinda ya fahimta shi ne TAKORIN 'is an author' tunda yaji ance NOVELS dinta.
Banda wannan kwarin gwiwar da ya samu ya samu karin na Momi da Baba duka basa nan yadda zasu ji dadin babbaka juna a wuta idan ta kama.
Babu mai ceton dayansu.
Yau za ayita ta kare (he can no longer tolerate it anymore!!!
Kamar yadda ya ce da Mama ne ya zo daukar aurensa (dead or alive) haka yake har zuciyarsa.
In har littafin labarin SAFEENAT MAHMOUD ALKALERI wato KWANA SITTIN na Sumayyah Abdulkadir ya amsa, to nima Fa'izar da ake yiwa sallamar na amsa.
Ya shigo kansa tsaye Walida na biye dashi kamar bakinta zai tsage don murnar ganinsa ta iso har gadon da nake kwance, da murnarta take fadin.
"Aunty Fa'izah ga Yaya Fa'iz!".
Wani irin kallo nayi mata wanda nake jin tunda Momi ta haifeta babu mahalukin da ya taba yi mata shigensa, ba shiri ta juya har tana cin karo da (stool) din madubi, saura kadan ta kifa.
Da sauri Fa'iz ya riko hannunta ya rike gam.
"Ina zaki matas?
Ke da nazo muyi zance?