Sashe 23
Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kokari nake in danne tasirin maganganun Aunty Zainab a zuciyata ta hanyar turawa gidan Hajjah a dauko min wani tsalelen leshi na (pitch colour) asalin shi marigayi N.S ya dinka mani kudinshi sun kai Naira dubu tamanin da biyar, ya dinka min shi ne wai inyi fitar fatin bikin shekarar haihuwar wani abokinsa da aka yi a Kano mai suna Dr.
Gadanya.
To a lokacin a ranar sai na tashi da zazzabi, dalilin rashin zuwana kenan na linke na goge leshin na boye can kasan kayana.
Ina da takalmi da jaka 'yan (Thailand) suma mahadin leshin duk ban taba sanyawa ba.
Abinda yayi mani cikas inda zan samu goggoro ba tare da na kula wadanda muka yi amfani dasu a yau ba.
A take na dau mayafi na fita, naje saloon aka gyara min kai da (setting) na burgewa na kuma je aka nado min goggoron yadda nake son shi (light pitch) aka yi min gyaran akaifa da wankin kafa nayi sumul da ni.
Na dawo gida na kulle kaina cikin kallabi kai ba zaka ce an taba shi ba na hada kayan da goggoron na boye a sif din Aunty Zainab.
Wurin sha biyun dare barci ya soma fizgata sannan su Ummi suka shigo ina kwance a gado, ta cire goggoronta ta kwado min, shi kansa goggoron kamshin turaren Bashir yake yi.
Na ja wani wawan tsaki na ture goggoron daga kusa dani, ko me zan jiwa haushin oho!
Tana so ta gaya min ne ta hada jiki da namiji, ko me zan jiwa haushin oho!
Banza an bata sidin turawa shi ne zata zo ta yiwa mutane fiffika, har warin tabar da aka ce yaya Bashir yana sha take yi.
"Banza mahaukaciya".
Ban san sanda furucin ya amayo daga cikina ba.
Tayi dariya ta ce, "Duk haukana ai ban kai ki ba.
Yaya Bash ya ce a gaya miki kada ki samu damuwar rashin (partner) gobe don 'couple evening' ne za'ayi miki mijin roba da yaya Sa'id Ibrahim Bamalli".
Ashariya naso danno mata, amma sai na fasa.
Ta cancanci bakar magana itama, don haka nayi gyaran murya daga kwance.
"Babban hauka ya wuce ka kaiwa miji kanka a soron gidan iyaye?
Don haka ban fiki hauka ba, ke naki salon na zamani ne, nawa kuwa (old-fashioned) ne.
Ni kam ku bar mijin robar ku na yafe ba a matse nake da namiji ba da har sai nayi riga malam masallaci.
Party ba don kowa zani ba, sai don kar ku dauka wulakancin ku da cin fuskar ku ya hana ni sakewa ne ko ina bakin cikin rashin miji har hakan ya hana ni shiga mutane, ina fatan kin g
ane?"
Ummi ta tafa hannu tayi dan fitoo, ta ce.
"Yeho!
Yarinya wallahi kinci a baki kyautar amsarki.
Indai wannan shi ne hauka, don Allah a nada min sarautar mahaukatan duniya akan umarnin iyayena nake ba kuma zan taba ganin ba dai-dai ba, tunda na bisu, su nakewa biyayya.
Ke kuma mai hankalin da yafi na kowa da kika tasarma kisan kai fa?
Waima tukunna ina hankali ga matar da ta titsiye mijinta da duka da zagi ya saketa?
Matar da ta dauki kwalba ta rotsawa mijinta ai ta tabbata tsinanniya".
(Baki kasan me zaka fada baka san me za'a mayar maka ba-TAKORI).
Zaneerah ma aka cire mayafi aka jefo min.
Eh naji kamshin (212) din yaya Aliyu kam babu shakka amma itama ta cancanci a tanka ta duk dai da ban san ita din dame zata mayar min ba.
"An dai ji kunya wallahi, tsofai-tsofai ga goyo ga tirtsetsen ciki amma ba'a fasa jaraba ba, shima Yaya Aliyun...".
Daga labulen dakin yayi yana fadin.
"Zaneerah ina wayata da na baki ki sa min caji?"
Dif!
Kake ji na dauke wuta, kamar ba ni ce mai magana ba.
Ya dube mu suna ta sheka dariya kamar sun samu motsatstsiya ya ce.
"Me take cewa ne?"
Na mike gaba-gadi na dauki dankwalina na daura na bar musu dakin.
Ina jinta tana cewa dashi.
"Zaginmu take yi".
Ya ce, "Baya tsiro ai, da tuni jikin nata mijin ba masaka tsinke".
***
Washegari tun safe su Ummi ke shirin wucewa Kaduna liyafa, sai shirya kaya ake ana zuge (troller).
Motocin da za su kwashe su zuwa Jabi Road basu zo ba sai bayan azahar suka shiga suka tafi da kawayenmu duka daga can ne za su shirya zuwa wajen da aka tanada don yin liyafar.
Ina kwance a doguwar kujera ban ko motsa ba ina kallon fitarsu daya bayan daya.
Yaya Aliyu ya shigo yana balle 'links' din hannun rigarshi ya ce da Zanirah.
"Madam, muje ko?"
Ta tashi wata tikisa da ita kamar alkubus, shi kuma aka sakalo hannu kugunta aka tallafeta, a haka suka fice ko kallona basu yi ba, suka fice.
Inda ya bude mata gaban 'Porsche' dinsa ta shiga, ya rufe ya zagaya shima ya shige.
Bashir aka kama hannun amarya mai kama da Princess Diana don kyau da daukar ado suka fice.
Har sun kai kofa ya juyo yana ce da ni.
"Af, gwauruwa, mijin robarki fa yana jiranki a waje Yaya Sa'idu, an baki kaya don kidifiri kin ki amsa.
No worries, na jikinki ma inaga ba laifi, kya samu waje ko tebirin iyaye da su".
Wani gululu yazo ya tokare ni yaki wucewa, ya tsaya min a makoshi, amma Fa'izah (is always) Fa'izah, ina da 'ki-fadi' sai na ce.
"Allah Sarki Yaya Bashir ka sallami mijin robar Fa'izah ko babu shi Fa'izah (can survive), kasan mace Allah Ya yi mata juriyar iya rayuwa ba tare da namiji ba, namijin ne bai iya rayuwa mai dadi sai da mace.
I.e namiji zai saki mace, ta zauna gidan iyayenta ba tare da ta yi wani auren ba kuma ta zauna lafiya.
Amma shi namiji a ranar da yayi sakin ma zai iya kawo wata, ka gane?"
Ya ce, "Ohonki kuma!
Tsoron shan kunya ya hanaki zuwa (party) baki da sauran bakin surutu".
Da haka ya fice.
Na mike tsam bayan fitarsu nayi wanka, na dauko lesi na na sanya, na saki dogon gashina a gadon bayana, na karkata goggoro na tsayar dashi dai dai goshi na.
Na janyo takalmi da jaka na cikin kwalinsu mai tudun dunduniya siririya da siririyar igiyar daurewa na fitar na sanya, na rike 'purse' din mahadinsa wadda kudin mota kawai na zube a ciki.
Nan da nan na hau walkiya kamar wata dan daren goma sha hudu.
Na kawo (fashion earing) kalar adon lesin na daura (shimmering pearls) hannu, wuya, kunne da idon sawu sai walainiya nake duk motsin da nayi.
Ni kaina yau nayi mamakin yadda nake, ban taba tunanin haka Allah Ya kyautata surata ba sai yau.
Na fito harabar gidan Baba Na'ibi babu kowa don haka na tura wani almajiri yayo min hayar taxi kafin minti goma sai gashi ya dawo cikin motar tare da mai taxin.
Na ce da mai taxin ya yi duk iya gudun da zai iya ya kaini (Indoor-sport hall) na garin Kaduna cikin awa daya, ko nawa ne zan biya shi.
Nan da nan ya ce in shigo mu tafi.
Dakin taron ya cika ya batse babu masaka tsinke da kyawawan iyalin A.B tabbacin a yau mallawan na biki kasurgumi da basu taba yin kwatankwacinsa ba.
A cikin tafiyar nutsuwa na shiga ratsa taron jama'ar suna kallona tabbacin basu tsammaci zuwana ba ma balle wannan shiga ta firgitarwa.
Ashe wajen cike yake da abokan Fa'eez na Kad-Poly irin su Surajo Nuhu wanda a halin yanzu ma'aikaci ne a Central Bank da wasu daga cikin abokan su da yawa suka mike suka tarboni muka jero tare sai tafi suke yi da dariyar farin ciki, yayin da Sa'adu Bori dake cin kasuwarsa a wajen ya karkatar da akalar wakarsa gareni ya kyale su Ummi, cewa yake.
"TAKAWARKI LAFIYA GIMBIYAR ABUBAKAR FA'IZU GIWA...
AMARYA FA'IZA AMANAR FA'IZ GIWA...".
Suraj tunda na tako kafata cikin (hall) din yake min (spraying) da dollers madadin Fa'izun su kenan.
Ni kam ko a jikina, a raina fadi nake wahala ce bata ishe ku ba, ko kallo basu isheni ba.
Wajen ya hautsine da kirarin abokan Fa'iz masu video da masu camera suka juyo da akalarsu kanmu gaba daya abokan Fa'iz daukana suke hotuna wasu vedio da wayoyinsu.
Ina kallon bakin su Yaya Aliyu dake (high-table) yaki rufuwa, haka Mama da tarin hamshakan matan Kaduna da ta gayyato.
Anan Yaya Rabi, Aunty Hauwa da Mama da kanta suka taso suka tarbeni suka hana ni isa ga mazaunin su Ummi.
Girgiza kai nake cikin son kecewa da kuka ina yi musu nuni da ka su barni in wuce, amma sunki hakan.
Mama ta rikeni gam-gam, haka Ummi da Bashir, Zanirah da Yaya Aliyu tasowa suka yi daga mazauninsu ya saura babu kowa a gaban Sa'adu bori cikin filin sai mu 'ya'ya da jikokin Hajjah da kawayen Maman Kaduna sai ko Surajo da ya rufa min asiri suka shiga yi mana "spraying" ni da Surajo sai ka rantse da Allah shi ne angon nawa, kazalika Ummi da Bashir, Zanira da tirtsetsen cikinta da Yaya Aliyu rungume da ita, duk suka bude bakin jaka suka shiga yi mana 'spray' tako'ina.
Dadi ne ko mene ne ya yi min yawa, sai gani kuka ya kece mani.
Tausayin Mama har kokon raina da jinjina kaunar da take mani na kasa jurewa nima ban san dalilin tausayin nata da ya rufeni ba, na zame da gudu na karasa mazaunin su Ummi na zauna na kifa kaina a tebirin na shiga kuka mai yawan gaske wanda ni kaina bansan dalilinsa ba.
Suraj ne yazo ya zauna a kujerar Yaya Bashir ya ce.
"Fa'izah, Fa'iz bai kyauta ba na sani, don me ya yi mana haka?
Rana irin wannan mai dumbin tarihi ka tsallake ka tafi wani aiki kai kafi kowa aiki?"
Haushinsa ya kara kamani da shisshigin da yake ta yi mini tunda na sako kafata a filin wajen nan shi bai yadda ba asiri ya rufawa abokinsa, kuma abin kirki yayi.