← Book details Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 27

Sashe 3

Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na shigo aji a makare ainin domin sai da muka biya muka ajiye Yaya Rabi a asibitin Malam wajen awon tsohon cikin da take dauke da shi, muka kuma mai da ita gida sannan Yaya Mufty (sunan da Yaya Rabi ke kiran mijinta Muftahu) ya kawo mu ya ajiye ya koma (office).

Jikina har bari yake domin na ji jiya
yan ajinmu na fadin anyi sabon lecturer mara daukar wargi, madadin Farfesan dake daukarmu darasin.

Sanye nake da shudiyar danyar atamfa (exculusive) mai ratsin ruwan hoda da mayafi launin sararin sama mai haske.

Bayan wannan babu komai a fuskata sai farar powder da na muttsika da vaseline (lip balm) a siraran labbana wanda ya kara musu taushi da kyalli.

A rayuwata bana rabo da zizara kwalli a idanuna, kwallin (kajal) baki yana kara lafiyar ido, yana kuma kara fiddo min da gazar-gazar din gashin idona.

Ina kokarin zama a kujera ya ce,
Get out please..... (fita waje don Allah)
Wata kunya ta taso ta lullube ni ganin yadda idanuwan maza da matan ajin ya dawo kaina.

Malam ya sake daga murya ganin na yi kasake!

Na kasa zama na kuma kasa fita.

Ya ce,
Get out I said (fita na ce)
Na daga ido cike da kwalla a hankali na dube shi.

Baki ne mai kyau na a buga a kalanda ko ayi tallan advertisement board da fuskarsa.

Bai da tsayi can-can, yana tsaka-tsaki.

Fatarshi goge da zuzzurfan ilimi a kananan shekaru.

Gwiwoyina suka sage tamkar an rarrade su da murfin kwano haka na cira kafa kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki na yi tattaki a hankali na bar ajin.

Wani abin mamaki sai ya kasance ban ji haushin mutumin nan ba a bisa korar karen da ya yi min a kan lattin awa daya.

Sai ma haushin kaina mai tsanani da na bar Yaya Muftahu ya fara kai Yaya Rabi awo maimakon ya fara kawo ni.

Haka nan na samu kaina da gwada yadda yake magana a sarke
get out.... get out I said!

Na yi murmushi na kwashi takarduna na yi (main library) don in yi assigment maimakon in zauna zaman tunanin malami mara daukar wargi, mai magana a sarke da in
ina.
****
A gida nake bai ma Yaya Rabi labarin karonmu da sabon laccara mai tangardar harshe.

Ummi ta ce,
Na ko so in ganshi, baki dan kakkaura mai yanayi irin na Yaya Bash yana driving wata (vauxhall) shudiya.

Gaskiya gayen ya yi a rayuwa Aunty Rabi.

Sai dai na yi mamakin yadda karamin yaro kamar wannan ya kai ga matsayin senior lecturer?

Rabi ta ce,
Meye abin mamakin a ciki?

Mai first class ko 2.1 zai iya zama lecturer komai kankantar shekarunsa.

In kuma a waje ya yi karatun speed din ba daya bane.

Mufty shekara daya kacal ya yi masters a Aston University
Ummi ta zaro ido ta ce,
One year Aunty Rabi?

Ta ce,
Baki bina bashin rantsuwa ki shafa ki ji wai shafa-labari shuni
A washe gari ma cikin ikon rabbi na yi latti.

Malamin jiya shine a ciki, sai na ji hantar cikina na rawa, kafafuna suka fara hardewa.

Tun ganina na farko jiya da mutumin nan wani sabon al
amari ya bakunci ruhi da zuciyata, ba zan ce so bane, zan iya cewa kwarjini yake mun, kuma yana razana ni da kwarjinin.

Yadda zuciyata da hantar cikina basu bar karkarwa ba, haka kafafuna basu bari ba.

Yau ma dai ta jiyan aka kwata, wato ya koroni waje.

Wannan karon kam raina ya baci, domin karkarin lattin nawa na mintuna goma ne kacal.

Muna cin abinci a (Al-Amir) na aje cokali na ce,
Wallahi Ummi wulakancin dan iskan malamin nan fa ya soma isata, asarar lacca biyu kenan ya yi mani
Haulatu ta ce,
Wai wane ne?

Oho!

Na san sunan shi?

Yana nan wani dan kakkaura
Ummi ta ce,
To mu ji alkhairi tunda tsiwar taki ta iso kan malamai.

Wani ya ce ki makaran?

Wannan ta wuce.

Haulatu ta gayyace mu cin abincin dare a gidansu a washe gari ta taya Abdullahinta murnar kammala (Law-School) lafiya.

Muka shirya tsaf muka cakare muka cancare cikin swiss lace ruwan kwaiduwar kwai (beig) da ratsin silver.

Haulatu ta riga ta gaya mana za ta turo direban gidansu ne ya tafi damu, don ya Mufty ya je Giwa, matar gidan kuma tana fama da kanta ba ta (driving).

Don haka da Abdoul ya shigo ya ce,
Wai wadanda Haulatu ta turo a dauka su fito
Sai na zuba mishi rankwashi aka, muka zari mayafi muka yiwa Aunty Rabi sallama muka fita.

Ni dai na ga mota
Vauxhall
(one door) ba Honda din gidan su Haulatu ba.

Kofar direba a bude ya zuro kafafunshi waje, sautin Abdurrahaman Sudaith na tashi a hankali a motar, ya sanya (ear piece) yana bi idanunshi a rufe ya jingina bayansa da kujerar kamar mai barci.

Kamshin turaren
na mota na tashi kadan-kadan.

Ganin bai da niyyar bude idon, bai kuma san da tsayuwar mu a wurin ba sai na yi masa sallama a hankali.

Tare da cewa,
Mun fito
Duk idanun ya bude wal!

A kanmu.

Hasken lantarkin farin bulb din da ya haskake harabar gidan ya haska mishi fuskokinmu.

A sannu a hankali ya dauke ido a kanmu ya yi dan murmushi yana yiwa motar key yana fadin
Bismillah ku shiga muje, kamar ma na taba ganin daya daga cikinku
Tuni zuciya da ruhi suka shiga aikin da suka saba a duk lokacin da suka yi arba da wannan bawan Allah.

Lecturer dinmu ne (Mr.

No name), don ban san sunan shi ba, mai kora ta a bainar jama
a in na yi latti.

Meye hadin sa da Khaulatu?

Ganin na tsaya na kasa shiga motar saboda mamaki sai ya dago ya dube ni muka hada ido na yi hanzarin russunar da nawa domin sun zama masu rauni kwarai a cikin nasa.

Ya ce,
Ki shigo mu tafi, tana jiranku, o.k?

Na bude bayan mota na zube.

Ummi ta shiga gaba.

Ya rufo kofar side dinsa cikin taushin murya ya ce,
IZAH NAKE SO TA DAWO GABA BA UMMIN AUNTY RABI BA!

Wani sauti kululuuuu!

Da cikina ya bayar kenan na mamaki, tsoro da tu
ajjabi.

Ummi na dariya ta bude kofar gaba ta fito ta dawo baya ta zauna tana min alamar in fita ina girgiza mata kai alamar a
Ya ce,
Bana sayar da kai Fa
izah, ni aminin Barister Abdullahi Turaki ne.

Shi ya turoni in taho daku an aiki Malam Saleh, ina fatan Fa
izah ta gamsu?

Ni da Ummi duka sai da muka murmusa.

Na bude mota na fito na koma gaban.

Ya ja motar a hankali muka bar harabar gidan, ya hau titi dodar.

Daga ni har Ummi mun yi tsit kamar a ce kyat!

Mu bude murfin mota mu arce.

Sunayenmu da ya ambata wai har ma da Aunty Rabi.

Na yi murmushi kadan daga aikin ( talkative ) Haulatu.

Mun yi nisa da Gadon Kaya mun hau titin Audu Bako, jefi-jefi yana karkata mudubin shi don hango motocin dake bayan shi.

Da danja ta tsai damu sai ya juyo sosai ya dube ni ,
Are you o.k?

Daga mishi kai na yi.

Har muka zo
Yankaba bai kara magana ba, sai ni da Ummi kan yi magana na abin da ya shafe mu.

Haulatu da Abdullahi ke zaune a harabar gidan bisa fararen kujerun roba suna hirar su hakora na shining (dariya).

Kai da ganin wadannan ma
aurata ka ga masoyan da ke ji da juna.

Har dai-dai inda suke ya yi parking, ya yin da duk suka mike suka nufo motar suna dariya.

Ya zagaya ya budewa abokinsa, Haulatu ta bude mana ni da Ummi.

Mr. and Mrs
.

In ji lecturer.

Na cika uzurinku, kyawun alkawari cika shi
Abdullahi ya ce,
Wannan lazim ne Sadiqy (aboki)
Haulatu ta ce,
Ni dai ba ruwana, kada ku shafa min kashin kaji, daman ta ce Dan iska ne
Na dafe kirji da hannuwa biyu na ce,
Ke Haulatu!

Yadda na yi din da irin fiddo idon da na yi cikin razana ta gaske ya sa gaba daya har Ummi suka tuntsire da dariya.

Abdullahi ya ce,
Kada ki jawo mata
carry over
Sweetie
Ya ce,
Ko spill over
ba ta karasa a gidan mijinta
Da wadannan hirarrakin muka rankaya dakin saukar bakin su Haulatu.
s a get together dinner of five....

Haulatu ta fada tana wara yatsunta biyar tare da janyo warmers guda biyar Arabian cuisines, kabsa, kebabs, manakees cikin biredin (pita), sai mankees, shawarmah da burger.

Ta bubbude kowanne tana serving a plate, cewa take
I did it to you with my naked hands my dear Abdullahi!

Congratulation on becoming a Lawyer
Gaba dayanmu bamu san sanda muka zuba tafi ba, ni Ummi, da Mr.

Lecturer.

Shi kuwa Abdullahi murmushi yake bakin kamar ya tsage.

Na kasa sakin jiki ko kadan abubuwan duk sun daure min kai.

Sanda Mr.

Lecturer ya bude wata foil paper ya turo gabana saura kadan in saki fitsari don mamaki.

Gasasshen naman saniya ne mai romo da ya ji tumatir da albasa, har da cabeji sai turiri yake.

Ya kuma dakatar da Haulatu daga serving dina shi ya yi serving dina da kansa, wannan gasasshen naman da
kebabs
(tsire) plate dina wato har appetite dina ya sani, wa ya gaya masa ina son gasasshen nama?

A yadda ya saki jiki a gidan na fahimci ba bakon zuwansa bane.

Har wajen su Hajiyar Haulatu tare da shi muka je muka gaishe su muka dawo falon.

Ya dauki tambulan ya cika da lemun matsattsun kayan itatuwa (tropical juice) ya miko min cikin lumshe ido da bude shi duka a lokaci guda.

Ban iya na yi musu ba na karba, amma kurba daya na kasa saukewa saboda gardin lemon, ko ko in ce gardin hannun da ya fito daga gare shi.

Cikin duka (Arabian Dishes) din nan gasasshen naman da
kebabs
kawai na iya ci saboda na zama bakuwar zuciyata.

This is the exact stranger I
m dreaming of.

Sannan actions and emotions dinsa sun nuna abin da ke karkashin zuciyarsa, tun kafin ya furta, he care too much, sai shisshigi yake yi mun.

Shishshigin da ba zan iya tankwabewa ba.
Chapter 3 · 0% Book details