Sashe 16
Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Babu mamaki in ya tuka jirgi a wannan lokacin ya saito shi cikina garin Giwa wanda hakan babu makawa zai murkushe musu dan garin na iyaye da kakanninsu da bai taka kara ya ba balle ya karye.
Mama ta tabbatar nutsuwar Fa'iz kawai samun zuciyar Fa'izah, ko da bai furta ba bai kuma nuna (weakness) dinsa ba, har gobe Fa'iz Abubakar, namiji ne mai amsa sunan namiji ko a cikin daruruwan maza baka fiya gane (weakness) dinsa ba, balle akan mace.
Ita din ma don ta sa mai ido ne, amma da fatar bakinsa bai furta mata ba.
Wanda hakan kuma (samun zuciyar Fa'iza) ba shakka ba karamin aiki bane ga duk wanda yasan Fa'izah da Fa'izun wurin kafiya da taurin kai.
Wadannan sune halayen da Hajja ke hange har take ganin hada masu irin halayyar gamayyar aure shi ne dai-dai.
A yau kam Mama ta qalubalanci tunanin Hajjah akan-kanta.
Hada masu halayya daya aure cikin A.B ba dabara bace so-karvau.
Zanira da Aliyu kam hadi ne na Allah, laushi na dukan taushi.
Amma masu taurin zuciya da kafiya ba dai-dai bane hadasu aure, in daya ya taso daya ba zai sauka ba, haka in daya ya hau daya ba zai yarda ya fado kasa ba yayi lallami ya kaskantar da kai ba ga dan uwansa.
Yadda Fa'izah ke ganin ta watsar da kanta inta kwantar da murya ta roki Fa'iz SAKI, haka Fa'eez Giwa ke ganin zub da kima ne da aji, muddin ya kwantar da kai ya baima Fa'izah haqurin abinda ya yi mata a baya.
Duk da abin ya zo ya zame masa jidali, ya hana shi ci, sha da sukuni da jin dadin komai dake cikin rayuwar duniyar baki daya.
Ya hana shi barci da walwala balle komawa bakin aikin shi.
Don haka Mama ke addu'ar Allah Ya sauke na Fa'izah, domin muddin Fa'izah ta sauke dole ne shima Pilot din ya sauka.
To a washegari ne kuma Aliyu ya kada mata 'ya'yan hanji da albishirin gudun Fa'izah.
Bata iya ta fadiwa Fa'iz ba sai dai shi a lokacin ya damu da ya ga Fa'izah ko da gani da ido ne a kalla zai samu sauki daga azabtuwar da zuciyarshi ke yi a dalilin rashin ganin nata, inyaso ko ganinta ya yi kawai daga nesa ya haura takalmansa ya bar mata garin da kasar baki daya, in ta rage bala'in ta bishi Amsterdam su zauna.
Indai sun kasance gida daya ai maganar kafiya da kiyayya sai ayi ta yin mai dalili, ba yanzu da ko harararta baya hange ba.
Ya kurawa jerin jakunkunan da ya danqara dalolin shi ya sayo da sunan lefe ido.
Shin wacce Fa'izah yake tunanin za ta daura zaninshi?
Ko da yake a lokacin yana kan aiki a Istanbul ne, giyar son ta buge shi, ya shiga hada su a kasuwar (AKMERKEZ Shopping Mall) ba tare da ya yi shawara da kowa ba ko yasan 'size' da take amfani da shi a yanzu.
Ya dubi shekaru ne kawai ya kintata, kuma da ya ganta bata zarce yadda ya kintatan ba.
Ya bude yana duba su a hankali har da (underclothes).
Fadin abinda ya kashe akai bata baki ne, amma ta wace hanya zai bata ta karba tunda a zuri'ar su ba'a lefe?
Shi ne abinda ke damunsa.
Ya mayar ya zuge ya koma ya jingina da filo ya lumshe idonsa, abin duniya ya bi ya dame shi, ya rasa ta hanyar da zai bullowa matsalar aurensa.
Hausawa kan ce, "Tun ran gini ran zane".
Haka "Juma'ar da za tayi kyau tun daga Laraba ake ganeta".
Sannan "Kowa ya sayi rariya yasan zata zub da ruwa".
Kuma "Tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka". (So he has to bear the outcome of his wrong doings...)
Ya nisa "Ba abinda lokaci ba ya magani".
Wani sashi na zuciyarsa ya yi (whisphering) wato rada.
Dai-dai lokacin da wayarsa dake kan bed-side take ta tsuwwa.
A fusace ya dauka domin bai son wani abu ya katse tunanin nan da yake yi, tunanin kaxai sassauci yake saukar mishi tunda ba zai iya gayawa kowa halin da yake ciki ko abinda ke damunshi ba, sai dai su tattauna shi da zuciyarsa su baiwa juna shawara, su kuma lallashi juna tunda babu mafita sai jajircewa, ya rike igiyoyin aurensa gam-gam har zuwa lokacin da Allah zai tausasa zuciyarta wadda babu wanda ya san yaushe ne?
Sai Zuljalali wal ikrami.
"Na'am!".
Abinda ya ce kenan ba tare da ya duba fuskar wayar ya ga wane ne mai kiran ba.
"Ka ajiye duk abinda kake yi haka ka taho gobe.
Yanzu na samu sakon ana kiranmu (interview) jibi da British Airlines.
Ka sani wannan dama ce ba ta wasa ba, don Allah Abubakar ajiye komai ka taho don Allah.
Night flight na gobe zamu bi zuwa Great Britain".
Abokinsa ne Ba'indiye Maajid Abduljalal ke magana kamar zai fashe da kuka.
"Amma Maajid za ka cuce ni, ka san abubuwan da suke gabana kuwa?"
"Zan cuce ka ko zan taimake ka? (This is a life-time opportunity) Abubakar, ina shawartarka (don't miss it...) koma mene ne ke a gaban naka ajiye shi, ba Fa'izah bace?
Don Allah kada ka ba da maza (achievements are greater than women).
Ka yarda dani, ka karfafa zuciyarka muyi wannan fafutukar tukunna, sai ka dawo ka ci gaba.
Na yi maka alkawarin (I'll stand by you) inga cewa kun dai daita da matarka idan mun dawo (and I promised to help you to the end of the battle my friend, be a man) Fa'iz, ina jiranka.
Akwai (morning flight tomorrow) daga Abuja, nima shi zan bi daga Berlin zamu hadu a Airport din Wales, ina jiranka".
Ya kashe wayar ba tare da ya bashi damar ya yi korafi ko musu ba.
Ya ajiye wayar cikin matuwar jiki, sai kuma ya daga ya kira British Airlines ya yi 'booking' duk da jikinsa a mace yake.
Wani sashe na zuciyarsa ya yarda da Majid babu tantama zai halacci wannan (interview) to amma wani iri yake jin jikinsa kamar in ya tafi ba zai dawo ya tadda Fa'iza ba.
Halin rai da karfen nasara.
Ya duba agogonshi 'Jovial' mai ruwan kasa-kasa ya tadda karfe uku na yamma.
Dole ne yaga Fa'izah ko daga nesa ne kamin ya tafi Birtaniya.
Domin a yadda yake jin jikinsa da zuciyarsa da kyar ne in zai dawo ya tadda Fa
iza.
Don haka maganar ginshira da jan aji babu su yanzu, zai fuskanci Fa'izah (no matter what!)
Ya mike kamar wanda aka yiwa allurar kuzari ya fito da sauri ya kwalawa kaninsa Shu'aib kira.
"Ka rufe kofar nan ka kwashi jakunkunan nan dake daki na ka zuba min a boot ka aje mukullin, zanyi tafiya sai na dawo".
Ya isa sashen Mama yana yi mata bayani a gurguje, sai ga hawaye a idon Mama.
"Ni dai raina baya son tukin jirgin nan Fa'iz, hankalina ba ya kwanciya, kullum kana kan iska.
Me zai hana ka dawo gida kwata-kwata ka nemi wani aikin mai sauki kayi?"
Ya yi dariya ya ce, "Kai mama kenan, insha Allah ba abinda zai faru.
Ki bar mutum da zuciyar sa akan abinda suke so, kiyi addu'a Allah Ya tsare, Ya dafa mana, Ya kare miki mu a duk inda muka shiga.
Ki cire duk wata fargaba da tsoro, mutuwa daya ce tak!
Hanyoyinta ne yawa gare su, amma inevitable ce (mara makawa).
Yanzu ina zan ga Fa'izah inje Mama ko da babu gaisuwar arziqi?"
Mama gabanta ya ragargazo ya fadi.
A irin wadannan kalaman masu tsinka zuciya da Fa'izu ke furta mata da halin da yake ciki a fuska da zuci zata iya kara masa damuwa da sabon labarin gudun Fa'izah?
Ko da yake wani sashe na zuciyarta na gaya mata wai Fa'izah na Zaria, amma ya akai tasan hakan?
Ya za'ayi ta tabbatar da hakan?
Yadda Fa'izah taki jinin auren nan ina ne ba zata ba don ta guje masa?
Fa'iz ya sha jinin jikinshi da shirun Mama, ya ce cikin raunanniyar murya.
"Mama Fa'izah ta kashe kanta saboda kiyayyata ne ki ke jin nauyin gaya mini?
Na tabbata Fa'iza in akwai abinda yafi haka zata yiwa kanta, indai akaina ne Mama...".
Ya kasa karasawa, muryarshi na karkarwar da ta baiwa Mama tsoro akan wanda take ciki.
Tayi hanzarin katse shi.
"Lalalala!
Fa'iza ta warke tuntuni.
Hasalima ka samu sauqin tafiya domin tana A.B.U".
Ta hasaso ne kawai ta fada, domin ta rantse ba za'a ji mutuwar sarkin nan daga bakinta ba, ya je wani ya gaya masa.
Tayi saurin dauke kanta daga kansa, saboda hawayen da ke neman fallasa ta sun ciko idanunta, kiris suke jira su malala.
Ya yi dan murmushin tausayawa kansa, amma yafi tausayin Mama da matsalar shi ta zo tayi mata karan tsaye bata ji ba, bata gani ba.
Ya juya ya doshi kofa, a zuciyarsa babu tsoron Fa'izah ko miskala-zarrah.
Babu tunani ko fargabar abinda zata yi masa.
To me zata yi masa da ya wuce zagi na fatar baki tunda dai a doke ba zata doke shi tayi nasara ba, sai dai hannunta ya yi ciwo.
Zagi yana tofo?
Ko yana tsiro a jikin dan Adam?
"Kuskuren Pilot Fa'iz Giwa kenan na farko, da ya sani da ya tafi neman aikinshi salin-alin shi ya fiye mai ALHERI".
Inji Sumayya Abdulkadir (Takori).
[6/3, 4:13 pm] Takori: ***
A ZARIA
Yaya Rabi da suka taso daga Kano ita da direban Ya Muftahu ta yiwa direban umarnin ya tsaya a Zaria zata ajiye tsarabar Momi na ta Gurasa data yo mata daga Kano kamin su wuce Giwa su hadu ita da su Yaya Aliyu su shiga neman Fa'izah.
Malam Garba direban Muftahu yayi (parking) dai-dai kofar shiga falonmu kasancewar gidajen malamai na Jami'ar Ahmadu Bello falo zaka fara taddawa da ka zo gidajen.
A dai-dai wannan lokacin na kammala cin abincin rana da Walida ta lababo ta kawo min ne.
Na daga labulen dakin Abdallah ina kallon daidaikun motocin dake giftawa suna wucewa ta kofar gidanmu da yake titi ne a shimfide wanda in ka bishi zai shigar da kai cikin makaranta don ko kusa nasan ba lokacin dawowar Baba bane, don shi sai wajejen taran dare yake shigowa.
Nikam wannan zaman kadaicin ya fiye mani zaman Giwa ina kallon bakin ciki kala-kala.