← Book details Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 27

Sashe 22

Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fa'izah ta takura min in saketa alhalin ban iya hakan ko giyar wake na sha.

Igiyar aure dai kowa ya sani uku ce, to ni Fa'izu Mukhtar Abubakar na ninka (ribanya) igiyoyin aurenmu da matata Fa'izah Ahmad Abubakar ukku sau uku =(9) kenan.

A kara tausar Fa'izah don Allah kada wanda ya kara dukanta indai akaina ne, domin nayi mata laifin da na cancanci horo daga gareta fiye da wannan da take mani.

Ko kun manta baya?

Na tafi kasar Ingila saina dawo a san abin yi.

Danku, mai neman albarkar ku.

Fa'eez Giwa.

Nan da nan Baba ya washe baki yana dariya, ya kuma mikawa Rabi takarda.

Cikin zumudi ta karbi takardar tun kan ta gama taya yayanta dariyar farin-cikin da yake yi, tun kafin ta kare karantawa take dariya har ta gama.

Kana ta mikawa Momina itama ta karanta duk suka sa dariya.

Rabi ta ce, "Aje a hakan, kada wanda ya ce mata ba haka ba.

In ya dawo ya fada mata da kansa ".

Baba ya yi dariya a zuciyarsa hamdala kawai yake yi.

Ya dauki ruwansa da Momi ta aje masa wanda ya kasa sha ya shanye tas, ya dau mukullin motarsa ya fice zuwa masallaci.

Ya Rabi ta kalmashe takarda cikin jakarta ta shigo dakin da nake tana yatsina fuska.

"To Gimbiyar bala'i, in kin ga dama ki taso mu wuce Giwa tare ko hankalin gyatumar bayin Allah Ya kwanta, jininta da ya hau ya sauka saboda kaunar ki alhalin ke din ba kya son kowa sai kanki, har kuwa da iyayen da suka yi nakudar ki suka haife ki.

Gobe ake yinin Ummi bai kamata ace babu ke ake yi ba koda yake ke zakka ce".

Na yunkura ina fadin, "Zuwa kai kamar da kasa, sai dai wallahi ba zan kwana gidan Hajjah ba sai dai gidan Baba Na'ibi?".

Ta ce, "Yanda kike so ai haka za'ayi miki don kam kinfi karfin kowa".

A GIWA
Washegarin ranar ya kama yinin bikin Ummi.

Ni, amaryar kanta da Zanirah da sauran kawayen amarya duka gidan Baba Na'ibi muka kwana.

Babu wanda ya nuna min wani canji ko a fuska ko a mu'amala kamar komi bai faru ba, ashe Ya Rabi ta bi ta bayan gida ne ta yiwa kowa bayanin yadda abin yake.

Duk da babu wanda ya nuna min wani abu ko alamar jin haushi ko ta da abinda ya gabata ni din akan kaina jina nake wani irin sukuku!

Duk jina nake kamar bare a cikinsu, kuma kenan ashe abinda nayi din ban kyauta ba kenan tunda nake jin kaina matsayin mai laifi a garesu da babu wanda ya budi baki ya ce nayi laifin.

Gani nake kamar dukkansu A.B kallon tsana da kyama suke min tunda na ki dan uwansu na kawo sauyin al'amari cikin zuri'ar su wanda tun Ahmadu A.B shekaru ashirin da uku a baya ba'a samu kwatankwacin sa ba.

Ummi sai faman ja na take a jiki, dinkuna ma duk iri daya tayi mana, wanda duk tasa nima shi take takura min in sanya, dai-dai da kalar agogo bata bambanta ba.

Zanirah kam wani baya-baya take dani tare da yi min wani gani-gani, ni dai naki yarda in biye mata tunda ta samu labarin cin zarafin da na yiwa Yayanta ta koma min haka.

Ba na yarda in nuna nasan tana yi ma duk da raina baya yi min dadi.

Allah wadaran surutun Ya Rabi.

'Yan uwa da abokan arziki kowa yazo yadda yake kiran Ummi da "Amarya" haka nima suke kirana, amsawa nake da karfin gwiwata tunda nasan ina da 'guarantee'.

Su Walida, Hanifa, Maryam manyan kanne kirazan biki sun kasa zaune sun kasa tsaye, sunyi ankon shadda ruwan zuma da bakin gwaggwaro sunyi kyau matuka.

Walida idan muka hadu da ita ta takarkare tana rabon abinci sai ka rantse da Allah bikinta ne ko nawa, saboda rawar kai da rawar kafa.

Ashe Walida tasan komai, ni ina mata dariya itama a ranta ni take yiwa.

Ummi ce ta gargadeta kada ta sake aji mutuwar sarki a bakinta.

Da yamma can goshin magariba muna sanye da wani (swiss-lace) mara nauyi ni da Ummi (turquise blue).

Jama'a sun fara bajewa don gab ake da kiran sallar magariba a falon Aunty Zainab, Ummi zaune a gefe tare da sauran kawayenmu, hatta Haulatu ta halarci bikin Ummi, Naja'atu da Zubaida duk suna falon ana ta zuba hira.

Ni ina gefe kwance a doguwar kujera, Fa'izah ce akan ruwan cikina diyar Yaya Aliyu ina mata wasa tana ta dariya.

Yayin da Zanirah tana zaune da zungureren cikinta a gaba tana faman zuba (souvenirs) a leda ita da su Haulatu, kowacce da abinda take zubawa a leda wata kek, wata meat pie, wata cincin, wata soyayyen nama suna dai yin kullin nasu cikin tsari mai burgewa.

Walida ta shigo ta ce wai muje inji Yaya Bashir duk mu ukun yana dakinsu na da na gidan Hajjah.

Gaba daya muka mike, Ummi aka sake gyara goggoro aka duba madubi aka dauki (spray) aka feshe jiki, tuni dakin ya dume da kamshi mai dadi.

Aka sa hoda aka fente fuska, nan da nan ta hau sheki.

Nayi dariya na ce, "Iyen ba!

Kaga amaren babban Yaya, haduwar ba sauki".

Ta kyabe baki ta ce, "Ohon miki!

Kece gwauruwa, sai ki zuba mana ido in munyi 'ya'ya kunyi kai daya sai ku ci naku zamanin tare dasu ko?"
Na ce, "Ina!

Ta Allah ba taki ba.

Allah Ya kiyaye insha Allah nima bazan kara shekara gidan iyayena ba Allah Zai kawo min nagari na kowa, kuma zabin zuciyata".

Da hirarrakin da muka karasa dakin su Yaya Bashir kenan.

Ummi ta faki idona tayi min gwalo.

A tare muka yi sallama Yaya Bashir ya amsa, kowaccenmu ta samu kujera ta zauna.

Yaya Bashir na fadin.

"Ummi tawa dawo nan mana".

Yana nuna kusa dashi.

Tayi murmushi tana sunkui da kai, bata amsa tayin nashi ba ta zauna a gefena, shi da Yaya Aliyu ne, wanda tsam ya taso daga inda yake zaune ya zauna a masangalin da Zanirah ke zaune ya zauna cike da kulawa yake tambayarta.

"How is my baby kicking?"
Cikin murmushi ta amsa, "Gashi nan yana ta yi kamar zai kwance min zani".

Murmushi yayi suka ci gaba da hirarsu.

Bashir ya taso daga inda yake ya nuna min kujerar da ya mike.

"Ke gwauruwa, ja jiki ki bani wurin zama kusa da mata ta mana".

Sum-sum-sum na mike na bashi kusa da matarshi, a zuciyata ina da na sanin biyo su don kamar da gayya suke yi, don su ci min fuska.

Sai dai tun can ina girmama Yaya Bashir, saboda yadda baya nuna bambanci tsakaninmu da Zanirah da kowa cikin gidan Hajjah.

Na hada hannuwana biyu na tallabe haba ina kallon su suna barkwancinsu suna dariya, babu wanda ya damu da ni, kamar ma sun manta da ni a dakin.

Takaici ya isheni, na mike zan fita, Aliyu ya ja gefen zani na zan gifta su.

Na juyo amma ban yi magana ba.

"Dama ba wani abu yasa aka yi kiran tare da ke ba, maganar liyafar Kaduna ce ta gobe, mu zamu sa ankon shadda (hilton) da su Ummi, ke kuma tunda kin saki naki auren (don bana ce an sake ki ba) sai kisa wannan".

Ya nuna min leda bacco shake taf da kaya.

"A wajen Maman Kaduna na amso miki cikin kayan da tsohon mijinki yayi niyyar baki tsiya ta hanaki kwantar da kai ki ci arziki, ya tattara ya barki bayan ya dankara miki sakin wulakanci tara rigis!

Wai 3x3 =9.

In basu yi miki ba ki fada aje a buda a canjo miki don babu abinda zai yi da su, in zai yi sabon aure na tabbata sababbi zai yiwa sabuwar matar duk da nasan ko zai yi ba nan kusa ba, don kinsan matuka jirgi mata ba damunsu suka yi ba, kullum a tsaye suke kwana cikin iska, ba lallai ya damu da yin aure nan kusa ba".

Suka kwashe da dariya baki daya.

Kallon Yaya Aliyu kawai nake yi ina lissafa shi cikin sahun boyayyun makiyana wadanda ke sanye da fatar damisa suna (pretending) ta akuya ce.

Yaushe Yaya Aliyu ya koma haka?

Yaushe ya zabi Fa'iz ya barni?

Hawaye suka zubo min wadanda duk kokarina na kasa maida su.

Naso insa kai in wuce ba tare da na ce dasu komai ba, amma zuciyata ta ki amincewa ko da ban iya na rama ba, bazan nuna karaya ba.

"Koda bani da wanda zan aura a halin yanzu, nafi karfin suturar da zan sanya a jikina.

Allah Ya hore min abinda zan dinka ma kaina inyi fitar bikin Ummi ko da bai kai nasu tsada ba a kalla dai ba za'a ce an ganni tsirara ba.

Don haka ba sai na daura na Fa'izun ba, ko a sanda yake mijina bai yi arzikin da zai dinka min sutura ba, ya baro yi min sutura a sanda nake da bukatarta balle yanzu da igiyar ta tsitstsinke, alakar ta bi rariya.

Don haka Yaya Aliyu, ina ganin ku nemo wanda za kuyiwa gorin sutura ba dai ni Fa'izar ba".
[6/3, 4:13 pm] Takori: Suka sake kwashewa da dariya alamar 'game' din nayi masu dadi dukkansu.

"Sai Hajiya Fa'izah!!!".

Suka ajiye jinjina da hannayensu.

Ganin sun mai da ni mahaukaciya na fito na barsu ina matsar hawaye zuwa falon Aunty Zainab.

Fa'izah baby ke ja min zani, ban san sanda na tureta ta fadi gefe tana kuka ba.

Aunty Zainab Maman Yaya Aliyu ta tare ni tana tambayar me ya faru nake kuka?

Ina kuka na zayyane mata wulakancin da suka yi mani dukkansu.

Ta ce, "Fa'izah duk ke kika jawowa kanki.

Da kin kwantar da hankalinki da Fa'izu da duk hakan bata faru ba.

Kin san dai duk cikinsu Fa'iz ya fisu komai har shi yayan kobon (Aliyun).

Amma ki ka rufe ido ki ka badawa idonki toka da bala'i da rashin arziki har ya gaji ya tafi ya barki.

Don haka baki da hujjar jin haushin su Ummi ko mazajensu anan".
Chapter 22 · 0% Book details