← Book details Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 27

Sashe 4

Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuciya da gangar jiki duka sunyi amanna, sun karbi shisshigin sun dora a kan kujera mai matsayin da baya kwatantuwa.

Watakila da zai iya lashe ni zai yi saboda kulawa.

Hakan yasa duk na bi na takura na kasa sakin jikina daga sanya baki cikin hirar shi da Ummi, wanda duka tambayoyi ne a kan abin da ya kawo mu Kano.

Haulatu ta ce,
izah fa ta bi ta takurawa kanta saboda malaminta
Gaba daya suka maido hankalinsu gareni suna murmushi.

Ta ce,
Dama kin saki ranki, kin saki jikinki wannan malamin....

Ya yi hanzarin cewa,
Abdullahi killace bakin matarka kafin in bubbuge shi
Abdullahi ya miko hannu ya rungumo kwibin matar shi yana fadin
Kada ki kara magana Honey.

A yiwa Yaya Malam biyayya don tare zan tafi in barku.

Sai dai ban goyi da bayan a buge min bakin amarya ba tun ban biya farashinsa ba (siyen baki)
Ban san sanda na yi dariya ba, ni dai haka nan soyayyar Haulatu da Abdullahi ta ke burge ni.

A gaban kowa basa iya boye su masu begen junansu ne, sai dai in ba za ka iya gani ba ka kau da kanka.

Haka yake yi in ya je wajenta a makaranta ya yi ta bamu kunya, wani zubin su bamu sha
awa, wani zubin su bamu dariya.

Tattalin Haulatu yake kamar kwan da aka nasa yanzu-yanzu.

Haka ita ma.

Ganin dariyata sai Abdullahi ya ce,
Ko ke fa?

In ya sake ce miki
get out
ki zo nan ki gaya mun ni dashi ne kin ji Fa
izarmu
Cikin dariya na ce,
Ai ban ga laifin shi ba Yaya Abdullahi.

Ni ya dace in nemi afuwar shi a bisa lattin da nake mishi, wallahi ba halina bane yin latti akasi da uzuri aka samu.

I
m sorry Malam
Wani irin lumshe ido ya yi bai ce komai ba.

Ya kara kwanciya a cikin kujerarsa.

Wannan karon wayar hannunshi yake latsawa kamar bai san bikin da muke yi ba.

Haulatu ta cika baki da shawarma cikin tsokana,
Wallahi Ummi wulakancin dan iskan malamin nan fa ya soma isata?

Ko kin san asarar lecture biyu ya yi min?

Oho!

Ina na san shi?

Yana nan wani baki dan kakkaura mai in-ina
Na kai tafukana da suka sha adon jan lalle na rufe fuskata suna ta dariya.

Shi kuwa murmushi kawai ya yi.

Ya ce,
Haulatu ba a sirri dake?

Na ce,
Daman kin san shi ai kika rufemu a bai-bai?

Ta ce,
Ah toh!

Ba ga shi yanzu na baku mamaki ba
Abdullahi ya ce,
Lallai dan iska, yau kuma
yan iskan idanun bisa aminiyata suka fada?

Ya dago kai daga kan wayarshi ya ce,
Ya ishe ka haka nan Abdullahi!

Kai ka tashi ma ka tafi lokacin tafiyar ya yi ko a nan za ka kwana yau?

Ya ce,
In na kwana na yi laifi ne?

Bai kula shi ba, suka ci gaba da kwasar girkin Haulatu sai da kowa ya yi kat.

Shi da kansa ya yi serving dina.

A yadda yake sarrafa hannayensa wajen serving din za ka fahimci lallai namiji ne wanda zai tattala matarshi matuka, wanda zai lallaba matarshi fiye da Abdullahin Haulatu.

Abdullahi ya mike yana fadin
Haulatu zan wuce, zo ki ji mana
Ummi ma ta mike ta ce,
Ni toilet za ki nuna mani a cikin gida
Gaba daya suka fice.

Daga ni sai malamina Mr. no name.

A sannan ne na fahimci sun fita ne duka don su barmu mu biyu.

Ya dan motsa a cikin kujerarshi sannan ya ce,
izah!

Wannan kira ya dade yana amsa kuwwa a sassan jikina.

Ban iya na amsa ba sai kara dukar da kai ina murza zoben hannuna.

Har yanzu ban yi abin da zai sa a sake dani ba?

Ko sai na kai ga durkuso bisa gwiwoyi na?

Domin wannan afuwar Fa
izah?

Na dan fiddo ido,
Ta ya ya malami zai durkusawa dalibinsa?

Ta dalilin yana SON dalibar soyayya mai yawa.....

Ya fadi cikin kwaikwayar muryata.

Da a ce ban ga yadda yake ciccijewa yana cin magani a aji ba, sai na rantse cewa ba shi bane.

Lallai so ba dama ne.

Jin na yi shiru ina tauna maganarsa sai ya katseni da cewa,
Shin Fa
izah ta tsai da gwani ne tsakanin Giwa, Zaria, ko Kaduna?

Sai na yi dariya cikin jin kunya,
Don me ka yi tunanin wannan?

Mu
yan Giwa bama hada taura biyu a baka
Murmushi ya yi tare da girgiza kai,
yan Kano muna hadawa, kenan rabon kanawa ne ya hana?

Murmushi na yi cikin jin shauki.
izah I
m serious.

I
ve interest on you.

Shin za ki iya auren malamin makaranta?

Dagowa na yi na dube shi da dukkan idanu,
Babana ma malamin makaranta ne
But you are born with a silver spoon in your mouth (kin fito daga gidan masu hannu da shuni), kaman hakan zai zama takura
.

Ya fadi cikin murmushi.
a, ban fito daga (silver spoon) ba, na fito daga BABBAN GIDA (point of correction) mai babban suna
Tafi ya yi min sau uku,
Mene ne bambancin guda biyun?

Akwai bambanci da yawa.

Babban gida kudi bai yi yawa ba, amma babu yunwa babu rashin suttura a cikinsa.

Sannan masu shi dattijan kwarai ne masu magana daya.

Idan kuma ka ce tajirin gida kana nufin gidan hutu
Wannan karon dariya yake yi sosai wadda ta sanya ni shagaltuwa a kallon sa, kyawunsa na kara kayatar da zuciyata.

Na yarda dake Fa
izah, to amma fa sai kin ki ji kin ki
gani a tafiyarmu.

Abin da na gani ina so da zuciya guda ba zan iya munafuntar shi ba, ina da tabo Fa
izah, wanda na san as soon as an fara ganinmu tare za a kawo sukar sa.

Duk da an ce waka a bakin mai ita ta fi daxi, ina jin kunyar kaifin idanunki....

Ya yi dan murmushi....

Ina son mata Fa
izah, ina son su da yawa..... na yi amanna da cewa har gida za a biyo ki a gaya miki wannan, sai in ba a ganmu tare ba.

Amma na yi miki alkawari Fa
izah tsakanina da mahaliccina from you it will cease to exist (son matan) na yi miki alkawarin bari har abada in har kin amince ki zamo uwar iyalina.

Daga ganina dake na farko zuciyata ta gaya min ke ce (life-companion) dina mafi cancanta.

Kaunarki ta fara ne daga ganina dake na farko (love at first sight) na rasa nutsuwar zuciyata a tsayin wunin ranar da daren baki daya.

Da nake kwatantawa Haulatu kamanninki da level din karatunki take ce min ke best friend dinta ce tun a secondary, da take yawan bani labari.

Shine ta hada mana wannan dabarar ta dinner (to dine here together) ta kuma turani in dauko ku.

Gaba daya tarihinki na jishi wurin Haulatu, na kuma kara tabbatarwa kaina INA SON FA
IZAH!

Shin Am I accepted Fa
izah?

Kaina na sunkuyar ina murmushi.

Abin nan da masu iya magana ke cewa, labarin zuciya a tambayi fuska, don zuciyata ta yi na
am tun ma kafin ya furta.

Har nake jin cewa, ba son mata ba ko mata dari gare shi zan iya zama ta casa
in da tara in har nice uwar
yanshi.

Domin yanada duk abubuwan da za a so shin a kansu.

Ga dai ilimi, ga kuruciya, ga kyau na a manna a jarida, ban ga makusarsa ba.

Ko da ban furta ba, kallo daya za a yi min a tabbatar da na fada a matsananciyar kaunar ka.

Daga lokacin da idanuwana suka fada a kanka Malam
Magana nake a zuci, ban san cewa a fili nake yi ba.

Ganin ya lumshe idonsa ya bude ya ce,
Na gode
.

Ya tabbatar min ya ji abin da na ce.

Wannan sai ya tuna min da lokacin da na karbi tayin soyayyar Yaya Aliyu a Zaria, ga shi ban ci ribar waccan ba, na amsa ta biyu, kada Allah ya kara dandana min dacin ta.

Cikin dan lokacin nan mun tattauna abubuwa da dama mun kara fahimtar juna.

Har zuwa lokacin na kasa tambayar shi sunan shi.

Sai wurin karfe goma Haulatu ta fargar damu, da kyar muka katse hirar muka fito zuwa mota.

Ina ganin Ummi da Haulatu na gulma suna rada da dariyar shegantaka ko kula su ban yi ba.

Don na san da ni suke.

A kan hanya ma hirar muke yi.

Ya gaya min ya yi dukkan karatunshi ne a Taiwan inda ya karanta harshen Larabci ziryan.

Shi da Abdullahi
yan family friends ne, haifaffun garin Dambatta.

Da kyar muka iya yin sallama don sai da Ummi ta shige ta barmu.

Sai shigowar hancin motar Yaya Mufty ne yasa muka yi sallama ya jira fitowar shi da yin parking din shi suka yi hannu, sannan ya shiga motarsa ya tafi.

Har zai fita get ya dawo ya yi min horn na juyo
Phone no na manta Fa
izah
Ni da Ummi bamu da waya
Saboda me?

An hana mu rikewa ne
Hannu yasa ya dauko tashi a gefe,
Ki rike wannan saboda ni Fa
izah.

Na yi alkawari ba zan zamo mai hana ki karatu ba!

Ya cire layin ya miko min (Sony experia) sabuwa dal.

Na rasa abin da ya hanani kin karba, na kuma rasa wanda ya sani yin godiya.

Wala
alla soyayyar kenan?
****
Fada na duniya babu irin wanda Aunty Rabi ba ta yi min ba a wannan daren.

Ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, har sai da na saka kuka.

Na farko daren da muka yi, na biyu tsayawa a waje da namiji tsayin karfe sha dayan dare.

Na uku wayar da ta ganni da ita, da izinin wa na karbo ta?

Don bakwa gaban iyayenmu ba zan ci amanarsu ba.

Abin da ya zaunar daku gidana shine karatu ba (flirting) ba.

Wannan wayar dole ki mai da masa abarsa gobe.

Gaskiya ba dani ba, ba a gidana za a karya dokar A.B House ba, gara ma ku sake tsari.

Gobe abu na farko da za ki fara da zarar kun shiga makaranta shine mayar da wannan wayar.

Yaya Muftahu bai ce komai ba.

Haka na kwanta zuciyata ba dadi da haushin Aunty Rabi.
Chapter 4 · 0% Book details