← Book details Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 27

Sashe 2

Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka nan bayan haihuwar Nazir sai da suka kwashe shekaru takwas zuwa tara kafin su samu haihuwar Haulatu.

Daga Haulatu yara ne maza uku daya na bin daya duk bayan shekaru uku.

Duk da jin dadi da sakewar da Nazir ke samu bai sa shi yin wasa da karatu ba, domin ya ga amfanin ilimin wurin mahaifinshi.

Ya so ya tafi soja don ya gaji ubansa amma Baban ya dage kan harshen Larabci yake son ya karanta, baya son shi da aikin soja, babu kwanciyar hankali a cikinsa.

Su shan sigari wannan duk a wurin Larabawa ya koya, sai dai sam in ya zo hutu baya sha a gida sai ya koma.

Bai fara neman mata ba sai da ya kammala degree ya fara masters a zuwan shi bautar kasa garin Lagos, inda ya yi wani aboki Tim ya koyar da shi mu
amala da mata, don haka da ya koma Taiwan sai idonshi ya bude da hakan.

A can ya kammala PHD ya dawo Kano ya fara aikin da yake yi a Bayero.

Rasuwar Tim ta hanyar muguwar cutar (SIDA) Aids bai sanya Nazir Sani kintsuwa ba sai haduwar shi da Fa
izah A.A Giwa.

Bai taba neman kowacce diya mace da niyar aure ba sai a kan Fa
iza, kamar yadda bai taba son wata diya mace tsakani da Allah ba baya ga Fa
izah.

Bai taba tunanin zai bar yaudarar mata ba sai a kan Fa
izah.

Daga ranar da ya dora ido a kanta, bai kara kula wata yarinya da sunan iskanci ko yaudara ba, domin yana ganin kintsattsiyar yarinya kamar Fa
izah ba ta dace da watsattsen miji kamar shi ba.

Don haka ya kimtsa kansa, tun hakan bai zamo dalilin da za a hanashi Fa
izah ba.

Tunda ya tabbatarwa kansa aurenta zai yi domin Allah da soyayya.

Ya yarda ya amince da duk zargin da ake masa na cewa shi din dan iska ne, ya yarda ya kuma amince bai taba musantawa ba, kamar yadda bai taba cewa yana da wani hali na kirki ba.

To amma wanda duk yake tarayya ta jiki da Naziru Sani, zai yi shaidar cewa mutum ne wanda baya wasa da sallah, kuma zuciyarsa daya ce da ita yake zaune da kowa, sannan ba shi da tsoro.

Baya tsoron uban kowa, sannan abin hannunshi bai rufe mishi ido ba sam.

Daga ranar da suka yi magana da Abdullahin Haulatu, ranar ba ta zagayo ba sai da Dr.

Nazir ya gabatar da maganar Fa
izah ga iyayenshi, ya kuma roke su da aje mishi neman auren ta sati mai kamawa.

Hajiyar su Haulatu ta yi matukar farin ciki da Allah ya nuna mata ranar da Nazir ya kawo mata zancen aure da bakinsa da ranta kafin mutuwar ta.

Yammata iri-iri ta sha nemawa Naziru yana fitittikewa, shi aure ba yanzu ba sai ya ci lokacinsa matarshi ma ba a haife ta ba.

Da farin cikinta da rawar jikinta ta isar da sakon Nazir ga General, shima ya yi farin ciki sosai, suka yi ta yiwa Allah godiya.

Tabbas addu
ar iyaye ba ta faduwa kasa banza a kan
yansu, ko ba jima ko ba dade.

A washegari ya tura kanin mahaifinsa da kanensa biyu da wan Hajiyarsu wurin iyayen Fa
izah.

Haulatu ce ta ce dasu Kaduna za su wurin Alh.

Muntari don shine madaurin auren su, ta karbi address wurin Aunty Rabi.

Tarba ta girma da mutunci Mama ta yiwa iyayen Nazir ita da Baban Kaduna da suka ce daga Kano suke neman auren Fa
iza wa dansu Naziru, malami a inda Fa
izar take karatu.

Sai mama ta kalli Baban Kaduna shima ya kalle ta aka rasa mai yin magana.

Tun daga nan jikin dattijan ya fara sanyi.

Da kyar Baban Kaduna ya ce,
Na yi mamaki da kuka zo neman aure ba tare da kun yi bincike a kan gidan su yarinyar ba.

Ban da haka duk wanda ya san zuri
ar Abubakar Giwa, ya san basa auren bare.

Ban fadi haka don yaron wajena ne mijin Fa
izah ba, sai don cewa ka
idar gidanmu kenan da muke bi tun iyaye da kakanni.

Ina mai bai ma Naziru hakuri, ya yi hakuri, ya yi hakuri Fa
izah TA YI AURE!!!

Da wannan bakin labari Hajiyar Dr.

N ta tare shi a dawowarsa daga wajen aiki.

Labarin da ya yi masa bugun da wani labari bai taba yi masa ba.

Ya dauki mukullin motarshi ya nufi kofa Hajiyarsa na kira, bai juyo ba yake fadin
Barni in je Hajiya, Giwan za ni in tambayi Fa
izah dalilin da yasa ni ban yaudareta ba ita ta yaudare ni...... ta san auren gida ake musu amma ta yi min haka.... me na yiwa Fa
izah da za ta zabi ta yi min wannan yankan kaunar ta yi dai-dai da zuciya da farin ciki na?

Gudun da yake shararawa a kan titin da zai kai shi garin Giwa ya fi kama da na
yan sumogal.

Zagin duniya ya sha shi daga motocin gaban shi da bayanshi.

A dai-dai kwanar da zai karya ya shiga Giwa suka yi arangama da motar shanu ta bi ta kan motarsa ta murkusheta irin murjewar da sai wani babban ikon Allah za a fidda mai rai a cikinta.
****
GIWA
Ban motsa daga inda nake ba, tun daga lokacin da na fadi na suma.

Karar da na yi ya janyo hankalin Hajjah da sauran mazan dake zarya a tsakar gidan.

A guje Hajjah ta shigo har tana tuntube da kofar daki tare da su Baba Barau da suka shigo a lokacin da
yan kanzaginta su Inna Kubra.

Hajjah ta tsugunna da hannuwanta biyu ta girgiza ni tana kirana
izah......

Fa
izah!!

Baban Giwa (Barau) shi ya fita ya zo da ruwa a kofi ya shiga yayyafa min amma ban motsa ba, ga idanuna a bude ina kallon su tarrr!

Hajjah ta shafi fuskata zuwa idanuna shima ban motsa ba, ta kama hannuna ta ji shi sanyi kalau, jijiyar ta saki.

Ta dubi fuskata babu alamun rai a tare dani sai ta rushe da kuka.

Inna Kubra ta soma karanto addu
a tana tofa min a fuska.

Ya yin da Baban Giwa ke tofawa cikin kofi, ya kammala ya shara mini duka a kaina, sai na kwanto sharaf jikin Hajjah kamar matacciya.

Ko dan yatsana na kasa dagawa, babu wata gaba dake motsi a jikina.

Wannan ya tabbatar musu da cewa dogon suma na yi, irin wanda shock ke sanyawa, mai wuyar farfadowa.

Hajjah ta rungume ni tana kuka ta ce,
Na shiga uku ni Hadiza, me ya yi zafi Fa
izah?

Muddin kika mike Hafizi na isowa za a warware auren nan, ba zai yiwu garin neman gira a rasa ido ba.

Wayyo ni Hadiza, wallahi na manta shaf da kiyayyar Fa
izah da Fa
izu da ba a yi auren nan ba
Baban Giwa ya zauna gefe ya zuba min ido duk sunyi tsuru-tsuru, ya ce,
Uhm!

Ai na fada Hajjah babu wanda ya saurare ni, yanzu in ta mace ai shi kenan hankalinki ya kwanta.

Tun lokacin na Aliyu na gaya miki kada a kara aurarrakin nan kin ki ji.

Yanzu ai an dau darasi ko?

Baban ABU wato mahaifina ya daga labule ya shigo yana cewa,
Zancen banza kake Barau, ba suma ba, ko mutuwa Fa
izah ta yi babu mai karya dokar Abubakar Giwa ko bayan ran Hajjah, mu zamu tsaya a kan wannan principle har karshen rayuwarmu.

Tashi ka fita ka baiwa mutane wuri sakarai matsoraci girman wofi tun ranka bai baci ba wallahi
Baba Barau ya kwantar da murya ya ce,
Nima ban ki hakan ba, amma a dinga duba soyayya tsakanin yaran nan kafin a kara kulla kowanne aure tsakaninsu.

Fa
izah da Fa
izu basa ga amciji tun tali-tali har zuwa girmansu.

Baban ABU rai!

Yana gaba da komai, sai da shi ake komai
izun ne ya bankado labulen dakin ya shigo a sukwane kamar an jefo shi tare da Yaya Aliyu, don tun fitowarsu mota Khalid yaron Baban Giwa ya ce dasu wai Fa
izah ta yi kara ta mutu!

Bai iya ya ce komai ba duk da ya ji kadan daga abin da suke tattaunawa, illa bin Fa
izar da ke yashe a kasa mushe ko mai rai da kallo.

Manyan fararen idanuwanshi gaba daya sun fito waje sun yi jawur, har wani brown-brown suka koma.

Jikinsa sai mazari yake bakinshi na motsi, amma ya kasa magana.

Aliyu ya ce
Shin Baba me kuke yi haka dukkanku tun dazu da aka rasa mai kaita asibiti?

Fa
izah ba mutuwa ta yi ba!

Sai ya sunkuya ya ciccibe ta gaba daya, Fa
iz ya hade girar sama da na kasa ya ce,
Ko da ban karanta ba na san maganin wannan suman...

Da sauri Yaya Aliyu ya dire ni gefen gado ya yi baya, ya ce,
To likita mai mata Bismillah
Ya yi waje abinshi.

A ranshi kam dariya ma abin ya ba shi yana ta yin ta ciki-ciki, wai matar dake tsakanin rai da ajali ake ma kishi?

Bai san gara ta dauwama a suman ba da ta farfado ta ganshi.

Ya karbi diyarshi da ke ta tsala ihu hannun Ummi a falo ya yi waje.

A hankali su Baban ma suka shiga ficewa daya bayan daya ba tare da kowannensu ya sake tofawa ba.

Hajjah ta share hawaye ta ce,
Yanzu Hafizi ya za ayi Fa
izan ta farfado?
iz cikin jin haushinsu duka ya ce,
Ban sani ba Hajjah
.

Ita ma a fusace ta ce,
Amma ka hana a kaita asibitin?

Ya fiddo ido ya ce,
Hajjah bakya gani daukarta ya yi ne?

Hajja ta hasala ta ce,
Zancen banza zancen wofi, yau ga sakaran kawai.

Sannu mai mata, hala gawa za ka aura?

To in gaya maka gaskiya auren nan kunce shi za ayi ba zai zama sanadiyyar rasa ran Fa
izah ba.

Da na san haka abin zai zama tun farko da ban saurare ka ba.....
[6/3, 4:13 pm] Takori: Ranar litinin din nan rana ce da ba zan taba mantawa da ita a tarihin rayuwata ba, domin wani dan karamin bangare da ta taka cikin tarihin nawa.
Chapter 2 · 0% Book details