← Book details Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 27

Sashe 21

Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fa'iz yayi tsaye kafafunshi harde da juna yana bin (lifter) da ta dauki Maajid zuwa sama da kallo har ya daina hango farar fatar Maajid da fararen kayansa da kwantaccen bakin gashin kansa na Larabawan Syria, yana mai auna maganganun da suka fito daga bakin Maajid din cikin ma'auni na hankali da tunani.

Ya tabbata duk abinda Maajid ya fadi gaskiya ne, to amma ta yaya zai bullowa Fa'izah su kasance tare?

Bama a gida Nigeria ba a duk inda ya sanya kafa?

Barma (bomb) din da ya taho ya barota dashi ya fashe me zai je ya tarar bayan fashewar (bomb) din?

Dole ya bi shawarar Maajid na tilasta kansa kin ganin Fa'izah da dosarta har bayan watanni uku kamar yadda Maajid ya ce.

"Kai to kuma har wata uku!

Wata uku fa ba kwana uku ba!!

Fa'izah zata iya yin saurayi a tsayin lokacin.

Yadda take kin shi din nan zata iya yin saurayin da zai debe mata kewar mataccen nata.

Ya rike kanshi da hannunshi biyu yana girgizawa da sauri...

"No!

Babu mai barinta, iyayensu ba zasu bari wani abu ya taba mishi aure ba tunda tana tsakiyarsu.

To itama bata da hankali ne?

Ai aure yafi gaban wasa".

A wannan karon hawayen kawai yake ganin idan ya yi (shading) zai samu sassaucin kishin da ya tokare shi ya hana shi hadiyar miyau.

In kuma ya sake ya bari suka zubo ya tabbata Fa'izah ta maida shi kamar sauran maza da Maajid yake misali masu yiwa mace kuka don ta so su.

Kada Allah Ya nuna masa wannan ranar.
[6/3, 4:13 pm] Takori: A ZARIYA
Na fito falo fes dani cikin doguwar rigar Momi, baki na kamar gonar auduga, ban zauna a ko daya daga cikin kujerun da suka yiwa falon kawanya ba sai a tsakinin Momi da Ya Rabi, suka dan matsa gefe suka bani fili a darare duk da ita Momi babu alamun jin tsorona a fuskarta, ta bani filin ne kada in dire akan cinyarta.

Duk sai suka bani dariya, ga Aunty Rabi mai yi min kallon hauka sabon kamu.

Na tsugunna gaban Momi da gwiwoyina biyu, na ce.

"Don Allah Momi kiyi hakurdi ki yafe ni, duk bacin ran da na sanya ki da kashin kajin da na shafa miki na zama cikin gidanki ba tare da saninki ba.

Wallahi ni kaina wani abin idan ina yi ban san sanda nake yinsa ba, ji nake kamar ana kitsa min shi a tsakar ka, bana cikin hayyaci na.

Ya Rabi kema don Allah kiyi hakuri, kuma wallahi Momi bata san ina gidan nan ba".

Nan suka dubeni baki bude kamar sunga wadda ta warke daga cuta.

Yaya Rabi ta muskuta ta ce.

"Yanzun kin kyauta kenan da abinda ki ka yiwa Yayanki da yazo miki sallama zai yi tafiya?

Fa'izah kisan kai za kiyi?

Kisan ma na mijinki dan uwanki, rabin jikinki?

Fa'izah kina son gamawa da duniya lafiya da kike ta da hankulan rayukan iyaye da masu kaunarki akan sanin kanki?"
Na kara kwantar da kai da kaskantar da murya sai ka rantse duk duniya ba za'a samu mai kirki na ba.

"Kiyi hakuri Ya Rabi, komi ya wuce bi'izinillah.

Tsakanina da Ya Fa'iz yanzu sai gaisuwar mutunci da mutuntawa, na bashi hakurin ciwon da na ji masa tunda YA SAKENI!".

Rabi ta shiga salati tana sallallami tare da tafa hannuwa, kafin ta kai karshen salatinta take direwa ta dauko sabo.

Kafin ta fashe da kuka ta ce.

"Kin cuci kanki kin cuce mu Fa'izah, hakkin iyayenki da na Hajjah ba zai taba barinki zama lafiya ba.

Kin bata wayonki, kin fita zakka cikin A.B, kin zame mana bakin bunu bata baibaya.

Bace min da gani tun ban lallasaki ko na tattaka ki ba...".

Ko a jikina wai an tsikari kakkausa.

Sai na sa hannu biyu na mika mata takardar, Rabi ta mike tsaye kamar an fisgota ta fisgi takardar daga hannuna, na tabbata in na tsaya tabbas zata tattakanin, sai na mike tsam koma daki na murza key.

Na shige cikin bargon Abdallah tunani dubu dari da hamsin ya aureni 70% na Dr.

Nazir ne.

Mutuwar shi ta dawo min danya, inama ana mutuwa a dawo!

Ga damar da nake nema kwana da kwanaki ta samu, amma wanda nayi ta hakilon akansa mai sawa da hanawa ya yi ikonsa akansa.

Na rufe ido ina kuka, tunanin kyakkyawar soyayyar mu cikin Jami'ar Bayero da wajenta ke gifta min filla-filla.

Na yiwa Allah godiya da na zamo silar kimtsuwar Nazir Sani, ya kuma mutu akan niyyar AURE.

Babu abinda zanyi domin nuna soyayyata a gareshi bayan nema masa rahma da gafarar Ubangiji a halin yanzu.

Momi dai ban san halin da take ciki ba don bata yi magana ba, sunkuyar da kai tayi, sai Ya Rabi ke ta fadace-fadacenta wanda ko a kwala ta.

Kukan rashin Nazir nake baka da zuci, na jiyo muryar Ya Rabi na cewa.

"Shima Fa'iz ya yi karamin tunani, ba'a biyewa mace, da maza na biyewa mata da cikinmu babu wadda ba bazawara ba.

Idan hankali ya bata shi ake sawa ya nemo shi, haka nan komai aka yi shi cikin fushi, sai anyi nadamar aikata shi".

Ashe Momi na hawaye take yi, can na jiyo tata muryar tana fadin.

"Yo ai shi kenan, sai ta yi ta zama idan zaman gidan iyaye dadi ne ga baligar mace.

Duka sa'o'inta babu wanda ya ba da kunya sai Fa'izah Bakin Buni Bata Baibaya a cikin A.B.

Fa'izah bata dauko zuciyata ba sam, zuciyata mai tsafta ce da ban taba kwana da wani a cikinta ba balle in tashi da shi tsayin shekaru a cikinta.

Duk wanda yayi min ba dai-dai ba ko nice da gaskiya uzuri nake yi masa da ajizanci irin na dan Adam.

Dukkanmu masu kuskure ne da gazawa a wani bangaren, balle Fa'iz akan Fa'izah ne kawai za'a ce bashi da kirki.

Na kuma yi mishi uziri tun a wancan lokacin da rashin haxuwar jini ne kawai, ko cikin 'ya'yanka ba ma 'yan uwanka ba sai kaji wani yafi kwanta maka.

Da babanta ya ce min Fa'iz ya ce Fa'izah yake so da aure jikina ya bani akwai wani al'amari mai girma tsakanin Fa'iz da Fa'izah da babu wanda ya sani sai Allah.

Nayi addu'ar Allah Ya hadasu da alherin dake tare da junansu, Ya rabasu da sharrin juna Ya kuma sanya albarka a cikin aurensu.

Amma ga abinda Fa'izah taga ya fiye mata, titsiye miji ya saketa.

Ba zan yi mata baki ba sai dai duniya kanta makaranta ce mai azuzuwa kala-kala.

Kuma na roke ki Rabi, kada ki sanya sunana cikin sha'anin nan, har gobe ni 'yar kallo ce a cikin al'amuran ku, ki bar iyayenta suyi hukuncin da ya dace da ita".

Momi ta share hawaye.

"Babu wadda ta baiwa uwarta kunya a cikin A.B sai Fa'izah don ta tabbatar muku da gaske ni bare ce a cikin ku...".

"Ki bar fadin haka Aunty Maimuna".

Rabi ta katseta cikin jin tausayi.

"Dole ince haka Rabi, shin da me zan doshi babanta da shi yau ya yarda ban san da zaman Fa'izah cikin gidana ba?

Duk muna zaune aka yi saki akan idonmu, wallahi duk mu za su dorawa laifi...".

Bata idasa maganarta ba tayi shiru saboda sallamar Baba.

Prof.

Ahmadu A.B, ya shigo da sallama, duk ya rame yayi duhu saboda tashin hankalin rashin sanin halin da nake ciki, da kuma ina na shiga.

Ya samu kujera gefen Momi na ya zauna, ya ce.

"Wash Allah!

Taimaka mini da ruwa mai sanyi Mainmunatu".

Momi ta mike tayi (kitchen) don ta kawo masa ruwan, sai a lokacin ne ya lura da autar Hajja a gefe, ya ce.

"A'ah!

Rabi yaushe a garin?

Kin zo kuma kin tadda tashin hankalin da diyarki ta saka mu ciki ko?

Fa'izah ta bani kunya, ta bada min kasa a ido.

Ban taba zaton tana da wannan halin ba na kafiya da kekasasshiyar zuciya wanda ba'a taba samun irinshi a zuri'ar A'B ba.

Sai dai ta wani bangaren na yi mata uzuri tunda ance Barewa bata yi gudu danta ya yi rarrafe ba, kuma duk abinda ka yiwa iyayenka ko bajima ko ba dade naka 'ya'yan za suyi maka (auren Momi da yayi ba tare da yardar nashi iyayen ba).

Allah Ka bamu ikon yiwa iyayen mu biyayya, ameen.

Rabi ta ce, "Ai tana nan cikin gidan dakin Abdallah, ba wani waje taje ba.

Sai dai Fa'iz din yazo ya saketa har nan".

Baba ya zabura ya mike, "What!

Shi Fa'izun ne ya yi mana haka?

Duk ta da hakarkarin da nake yi akan auren nan, tunda aka fara maganar auren nan bamu ci abinci ni da ubansa ya fada mana ba, shi ne ya biyewa shirmenta?"
Momi ta karaso da gorar ruwan 'Rogolis' da tambulan din karau a hannunta da gorar lemon (5alive) ta aje a gefe don tasan bacin ran da Baba ya samu kansa a ciki ba zai barshi ya sha ruwannan da yake son sha ba.

Bacin ran ya kashe kishirwar.

Ta ce, "Kada kaga laifinsa Baban Abdallah, ta nemi rabashi da ransa in bai saketan ba me zai yi mata ya ceci kansa?

Rotsa masa kwalba tayi aka fa?"
Baba ya mike yana salati, ya kara da.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!

Tana ina tambadaddiya ku gani in babballata itama jikinta ya gaya mata, kisan kai zata yi?

Shi kuma ya tsaya yana kallonta?"
Rabi ta tabbatar muddin na shiga hannun Baba a wannan lokacin sai tarihina yadda komi nashi yake tsima kamar ana kada mishi gangi, don haka ta tare kofar dakin Abdallah tana fadin.

"Yo Yaya in ka daki Fa'izah a yanzu aikin me aka yi?

Wacce riba za'a ci?

Baka huce ba tunda aikin gama ya gama, bakin alkalami ya bushe.

Mu duba takardar idan ya yi na Musulunci ayi kokarin gyarawa".

Ta shiga wurga ido neman inda ta cilla takardar saboda tashin hankali, kafin ta ganota a tsakanin kujerar da take zaune.

Baba da kyar ya zauna a kujerar da ya mike sai wata irin zufa yake yi, makwallatonsa na kaiwa da komowa, duk ilahirin jikinshi rawa yake.

Ya karbi takarda daga hannun Rabi ya warware, ga abinda dansa Fa'izu Abubakar ya rubuta cikin takardar.

Baban Giwa ko Baban A.B.U.
Chapter 21 · 0% Book details