← Book details Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 27

Sashe 1

Zumuntar Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry
WordDocument
0Table
Data
[6/3, 4:13 pm] Takori: ****
Karfe goma na safe su Ummi suka yi shirin tafiya taren su Bashir a filin jirgi.

Tun asuba da na yi sallah fuskata babu walwala, kallon kowa kawai nake zuciyata a cunkushe da bakin ciki da bacin rai maras dalili.

Hajjah yau ko gaishe ta ban yi ba, babu wanda na yiwa magana.

Na zubawa allon talabijin ido kuri kai ka ce program din nake saurara, amma ina!

Zuciyata ba ta tare da gangar jikina, abubuwa masu ban al
ajabi da ban tsoro kawai take wassafa min masu shirin faruwa dani.

Kafin karfe goma na safe gidanmu ya cika ya batse da dan Adam, sai busa algaita ake
yan daurin aure suka fara layin shigowa gai da Hajjah suna fita,
uwa ne da abokan arziki.

Kafin Babanninmu su shigo sun sha ankon farar shadda (getzner) sai sheki suke.

Suka zube a falon Hajjah suka kwashi gaisuwa suka fita.

Ina daga uwar daki ina hango ficewarsu ta taga daya bayan daya.

Mintina talatin bayan fitarsu na ji gabana YA FADI!

A dai-dai lokacin da dakikar agogo ya nuna karfe goma sha daya na rana, a lokacin ne aka daura aurarrakin masu ban mamaki, da suka ajiye kundin tarihi da wani aure bai aje ba cikin zuri
ar Abubakar Bamalli Giwa.

Wani maroki mai zakin muryar tsiya yake fadi da murya mai karsashi da kwarzantawa cikin babatun magana
ALHAMDULILLAHI!

ALHAMDULILLAHI!!

Sai da ya fada har sau uku.

An daura auren FA
IZAH AHMAD ABUBAKAR GIWA da FA
IZU MUKHTAR ABUBAKAR GIWA.

HADIZA da MUHAMMADU BASHIR, a kan sadaki lakadan ba ajalan ba.

Allah yasa anyi a sa
a, yasa anyi sai bakin rai, Allah ya sanya alkhairi ameen.....
da sauran babatu irin na maroka.

Maimakon in kira yi sunan Allah sai na kwarara ihu da iyakacin muryata na zube a wajen a sume.

Ban kara sanin me ke faruwa a duniyar ba.
***
Jirgin Boeng 708 ya sauka a filin jirgin saman Mal.

Aminu Kano da misalin karfe daya na ranar da ta kasance Asabar, wato awanni biyu da daura auren.

Jirgi ne da ya taso daga Ukrain zuwa Nigeria bayan shafe awanni masu yawa yana keta hazo, kafin ya wulwulo kasa ya tsaya a cyprus ya sha mai sannan ya keto kasarmu mai dimbin albarka.

Sai da passengers kaf suka gama fita kafin Pilots din su fito cikin fararen uniform dinsu.

Shine na karshe a saukowa.

Fari sol!

Mai madaidaicin jiki, zai fi kyau ka ce ba shi da kauri sai fadin kirji wanda da ka kalla za ka san gym ya samar da shi.

Ma
abocin wasu ilhamomi da nasibobi da dama da ba duk maza Allah ya mallakawa ba.

Ya saya fararen idanunshi cikin gilashi mai duhu ainun samfurin
KAREN MILLEN.

Sajen da ya zagaye gefe da gefen fuskarsa baki sidik kwantacce wanda a da baya da shi bai boye tsagin mallacinsa ba.

Sai ya kara fiddo ilhama da cikar zatinsa ya fiddo cikakken Bamallen sa, kuma Bafillace.

Dan kimanin shekaru talatin da hudu, wanda ya dama, ya kutsa cikin ilmummukan zamani daban-daban.

Dogon hanci gare shi kamar ruler aka sa aka ja shi aka daidaita shi a tsakanin idanunsa.

Idanunsa dara-dara wadanda suka dan shige loko kadan farare tar masu sheki da maiko (oily eyes) wadanda duk cikin zuri
arsu maza da mata shi kadai aka ya yiwa wannan ilhamar.

Idan lissafin da yake yi dai-dai ne yau shekarunsa takwas da barin gida ba tare da ya sake ko da waiwayarta da sunan hutu ba.

A zubin halitta da kirar jiki ya fi kama da Ahmadu A.B, a halayya kacokan Abubakar Giwa ya kwaso ba wani cikin zuriyarsa ba.

Don haka, ka ce ga hakikanin halayyar FA
EEZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA, abu ne mai matukar wuya.

Za ka san halinsa ne kadai idan ka zauna da shi, zaman ba na kwanaki ko watanni ba, sai dai shekaru.

Shekarun ma sai idan kwana kake tare da shi daki daya ka kuma tashi tare da shi, halin da ake kira halin MAZAN JIYA ba na YAU ba, and difficult to be studied by sociologists and psychologists.

Idan aka ce su karanci irin pilot Fa
iz za su yi placing dinsa ne kawai (upon hypothesis) but not a dependent variable.

Daga fitowar shi daga jirgi har shigewar shi wani ofishi (pilots changing room) idanun Khadija-Ummi na kansa, tana mai yiwa Allah tasbihi da godiya mara iyaka da wannan miji da Allah ya ba ta wanda ke ninkaya cikin zuciya da mafarkinta, ba ta taba tsammanin akwai ranar zahirantar mafarkin nata ba.

A hankali ta ji danshi a kan fuskarta, wanda ba ta ko tantama hawayen farin ciki ne.

Har zuwa lokacin da ya gama shige da ficensa a (airport) din tare da abokan aikinsa, ya canza kaya zuwa kaftan na farar lallausar shadda (Hilton) da ruwan kasar hula a kansa, takalmin fata dake kafarshi shima ruwan kasar ne.

Ya janyo trolley dinsa zuwa inda ya hango fuskokin masu kama da tasa fuskar, wanda komai daren dadewa suna gilmawa cikin idanunsa, wato fuskar zuri
ar Abubakar Bamalli, wanda ya fi so da gani shi ya fara ganin, wato Aliyu Na
ibi.

Da sassarfa Aliyu ya karaso suka rungume juna shi da Fa
iz, rayuwarsu ta baya ta dinga dawo masa tar-tar kamar a majigi.

Abubuwa da yawa ba zai manta dasu ba.

Cikin taron nan kaf na mata da mazan Bamalli, manya da yara, wadanda ya sani da wadanda bai sani ba, musamman kananan yara, ya hanga ya duba bai ga Zahrar cikin taurarin ba.

Ya ga Zanirah, ya ga Ummi, Mus
ab, Junior Yahya, Shu
aib, Walida, Abdallah da wata karamar yarinya mai tsananin kama da Fa
izah (Khausar), da sauran kannensa
yan Baba Barau, Sadi, Salisu, Sani da Na
ibi.

Mutum daya ce kawai babu, wato KANWAR kuma abokiyar fadan da a yau ta juye ta rikide zuwa matarsa ta sunnah.

Ko da wacce irin fuska za ta karbi al
amarin?

Ko da wace irin fassara za ta fassara shi?

Ko da wanne irin hannu za ta karbe shi?

Abin da ya sani ya kuma kwana da da sani ne cewa, Fa
izah!

Ba ta da makiyi a duniya irin sa!!!

To amma ai shi sonta yake yi tun can din ma.

Har kuma gobe son ninkuwa yake yi irin kaunar da bai taba yiwa kowa a duniya ba, in ka dauke Mama da Baban Kaduna wato iyayensa.

This is his own style of love!

To amma da wane language (yaren) zai yiwa Fa
izah bayanin hakan har ta yarda ta fahimce shi, ta karbe shi a matsayin miji a gareta?

Ya kuma wanke wancan dattin da ya dade yana yabawa kansa a idanunta?

Don haka kallo daya za ka yiwa pilot Fa
eez ka karanto matsananciyar damuwa cikin fararen kwayar idanunsa.

Duk da yaken da yake yiwa Aliyu da sauran
uwansa.

Yasa hannu ya karbi little Fa
izah hannun Zanirah ya dora a kafadunsa yana murmushi, kallo daya ya yiwa Ummi ya bude baki yana mamaki, ganin yadda kibarta ta zaizaye gaba daya, abin da babu wanda ya taba tsammani.

Shi da ita murmushi suka yiwa juna, wanda ga Pilot Fa
iz murmushin
uwantaka ne.

Kuma ba annuri a fuskarsa har suka shisshiga motocinsu, yana motar Aliyu ne, Aliyun na tuki shi yana gidan gaba, Ummi da Zanirah da
yarta a baya.

Sai dai tunda suka hau titin Zaria Road dodar wanda zai sada su da garin Zaria, kowa ya fahimci Pilot Fa
iz Bamalli cikin matsananciyar damuwa yake.

Ya sanya fuskarsa cikin tafukansa Allah kadai ya san me yake tunani a zuciyarsa.

Ummi ta yi tagumi a kujerar owner side da take zane.

Wane irin mutum Fa
iz ya koma?

Wane irin ango ne wannan babu wani alamar kulawa ko kwayar murmushi ga amaryarshi da aka daura musu aure yanzu-yanzun nan?

Wane irin mutum ne shi da zai bar kasar haihuwarshi shekaru har shida da wani abu ya dawo babu alamun farin ciki a fuskarshi?

Me ke damun shi?

Anya Fa
iz na farin ciki da dawowar sa cikin
uwansa?

Anya Fa
iz lafiyarshi kalau?

Anya Fa
iz na murna da auren su kamar yadda take tsammani?

Ta jerowa kanta duka wadannan tambayoyin lokaci guda, ba ta da amsar ko daya, don haka ta sunne kanta cikin cinyoyinta ta soma kuka a hankali.

Daga Aliyu, Zanirah da sauran kannensu dake cikin motar zuwa uban gayyar, babu wanda ya tambayi Ummi dalilin kukanta.

Ga Aliyu shi kam abin ne ya zo mishi wani irin banbarakwai cikin sarkakiya.

Bai san irin bayanin da zai ma kowannensu ba.

Babbar fargabarshi yadda Fa
izah za ta karbi zancen aurenta da Fa
A karo na farko ya ji haushin kansa kan munafuntarta da ya yi jiya, don me bai gaya mata gaskiya ba?

Don me ya rufe mata?

In kowa ya rufe mata shi bai dace da hakan ba.

Ita kuma Ummi tunaninta da Fa
iz aka daura mata aure amma ganin halin ko in kula da ya nuna mata ya sanyata kuka.

Shin da wane yare zai yi mata bayanin cewa da Bashir ne?

Ya ya Ummi za ta tallafi maganar bayan yana da masaniyar cewar ta tsani halayyar Basheer fiye da kowa?

Ta ya ya nitsattsiyar yarinya
yar kauyen Giwa ta cancanci tantirin dan duniya irin Yaya Basheer?

Kaico da tunanin Hajjah!

Kaico da bahagon tunanin iyayensu wurin hada irin wannan rikitacciyar auratayyar zumunci ko bata zumunci?

Su kam sun haye!

Yanzu na
yan bayansu yake ji.

A zuciyar Zanirah cewa take yi,
Ina ma ban zo garin ba kwata-kwata balle in ga wannan rikitacciyar rana......!

A dai-dai lokacin da Aliyu ya karya kan motar cikin tafkeken (gate) din ABUBAKAR BAMALLI HOUSE.....
****
WANE NE NAZIRU GALADANCHI?

Major General Sani Galadanchi shine mahaifin Dr.

Nazir.

Da na farko wurin iyayenshi, kamin haihuwar shi sun kwashe shekaru masu tsaho basu samu haihuwa ba.

Da Allah ya kawo Naziru sai hakan ya zamo musabbabin nuna mishi tsantsar gata wanda babu kwaba ko tsawatarwa a cikin sa.

Nazir ya tashi yaro dan hutu tun yana sakandire, sune samarin da ake kira
yan (high life) a lokacinsu.
Chapter 1 · 0% Book details