Sashe 5
Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
da fulasta a idanunshi akayo gida da baba sarkin gida aka sallace shi zuwa makwancin shi. Su tsoho basuji labari ba se ranar bakwai sabida matsalar network da babu a kauyen. Mota kusan biyar sukai da dangi suka taho kano sosai tsoho yake kuka kamar babu gobe. Haka nan iyatu da nuratu wadda karayar umari tafi komai ɗaga mata hankali. Seda sukai sati biyu sannan tsoho yace zasu koma kauye tare da su inna tunda umari yaɗan soma taka kafarshi. Anan babanmu yasa kuka! wiwi yana cewa shikam abar masa su ze rikesu sabida yana tuna wasiyar abokinshi na cewa. "Yusufa ni rasuwa zanyi dan Allah ga umari nan ka zame mai uba, ka taimakeni kada kabar ɗannan ya koma kauye kabarshi a birni ya mori rayuwarshi ko dan ya tallafi mahaifana da mahaifiyarshi". Da ƙyar tsoho ya yarda da rokon baba haka suka tafi aka bar inna da umari a hannun Allah a kuma hannun babanmu. Umari yana warkewa babanmu yakaishi makarantar sakandire aji ɗaya bayan an masa cuku-cuku ya zana jarabawar kwaman ƴantaras tare da imran. Haka suka taso shida imran tamkar uwa ɗaya uba ɗaya komi tare baba ke musu haka nan yake fama da ɗawainiyar inna da anty wadda take ɗauke itama da juna biyu ɗan kimanin wata guda. Rayuwa na tafiya cikin amincin Allah baba yana samun rufin asirin Allah gefe ɗaya kuma yana kula da iyalanshi tare da taimakon ƙaninshi sulaiman baffa karami wanda Allah yay masa nasibi ta harkar ginin dayake domin bayan rasuwar baba muhammadu sarkin gida, se ragamar harkar gine ginen ta koma kan baffa karami komai ya xamana na fitowa daga hannunshi. Cikin wannan ƙadamin baffa karami yasai filoti anan cikin unguwar ya fidda ginin waje biyu a hankali yake ginin shi lokacin yakai kuɗin auren umma. Ƴar nan makotansu wadda take ƴar ɗakin anty domin hatta zance a ɗakin anty akeyin shi. Ahaka su umari suka shiga aji biyu a sakandire ranar da suka shiga aji biyu inna ta haihu zokuga murna wajan umar kamar ya lashe yarinyar da inna ta haifa wadda taci suna maryam. Ranar suna baffa karami shiyay hakika sabida a wannan lokacin yamafi baba samun kuɗi. Ranar da su anty suka tashi daga wannan gidan hayar suka koma gidan da baffa ya gina wanda yay ɗakuna biyu a ɓangaren shi ɗakuna uku kuma a ɓangaren babanmu na baba ɗaya na anty ɗaya na inna ɗaya se kicin da banɗaki. Ranar da suka koma da daddare aka haifoni nazo duniya. Sosai baba da baffa sukai rawar gani ranar suna na, domin haka danginmu na tofa suka cika gida ana shagali hatta su tsoho ba abarsu abaya sabida an riga an zama ƴan uwan juna. Tunda Umari ya saka idanun shi akaina ya kafa ya tsare ko anty wanka xata shiga tofa shizata barwa ni yana min wasa gaba ɗaya gidanmu humaira ake cemin amman shi kaɗai yake kirana da Aisha ko yace min nana baka ganin dariyar shi se akaina baka ganin kukan shi se bani da lafiya wanda har cutar shima yake kwanciya. Suna jss three na sakandire nai shekaru biyu a duniya sosai yake min hidima da kuɗin shi dayake bin baffa gini yake samowa komai ni alokacin nima bani da magana seta yaya domin da sunanshi na buɗi bakina. Tare muka taso da maryam kanwarshi komai namu tare, alokacin da muka shiga shekaru uku aka auro umma wadda itama ta shigo cikin su anty suka haɗe kansu su uku. Kowa da sana'ar dayakeyi. Shekaru na tafiya lokacin anty ta haifi nafisa umma ta haifi nuhu ɗanta na farko nida maryam kuma mun shiga aji ɗaya na primary. Su kuma su ya umar suna jarabarwa karshe ta sakandire alokacin kuma yasai wani filoti dake gabanmu wanda ya tara kuɗin da kansa acikin kudinshi na aikin dayake bin baffa. Sannu a hankali suka fidda fandishan lokacin sunyi candy shida ya imran suke zuwa wajan ginin tare da abokanshi na unguwa. Da kansu suka soma ginin cikin amin cin Allah seda ya umar ya ginawa inna ɗaki da kuma ɗan tsakar gida sannan shima yay nashi ɗakin ragowar filin kuma yace se nan gaba za,a cigaba da ginashi. Ranar da inna taga ginin seda tai kuka haka suka tarkata suka koma ɗan nan gaban layinmu amman kuma kusan kullum se inna tazo ko maryam koni naje. Mun shiga aji uku a primary suka sami gurbin shiga jami'a anan makaranta B.u.k, sosai ya umar ya dage yana fita makaranta yana kuma harkar bin baffa wajan gininsu, wannan dalilin yasa wahalar rayuwa tai mashi yawa ga hidimar kanwarshi gata mahaifiyar shi, gakuma tawa wadda ya mayar da ita dolen shi. Muma gidanmu yay albarka sabida anty ta haifi anisa umma ma tana da yaranta uku nuhu da sadiya da kuma hafiza, Rayuwa tana tafiya lamura na sauyawa yanxu haka na shiga aji na shida xan zana jarrabawar fita a primary. Alokacin abubuwa sun soma sauyamin domin ni sam bana son ya umar yana cemin matar shi sabida yadda kawayena kemin dariya suna cemin matar ƙato. Na taso cikin wata irin ɗabi'a ta kafiya da taurin kai sam inna kafe a abu babu wanda ya isa ya juyani gani da ɗan karen baƙi kamar bayan tukunya saɓanin su anisa da suke farare tar kamar su baba. Kullum ina zuwa makaranta baba yana wajan kayan miyarshi baffa yana wajan sana'ar ginin shi tare dasu ya umar. Haka nan su sadiya suma suna xuwa makaranta rayuwa muke cikin rufin asirin Allah domin mu ɗin bama su shi bane. Lokacin dasu ya umar suka shiga lavel 2 alokacin muka shiga jss1 gaba ɗaya alamun girma sun bayyana atare dani sabida daman tun usul ina da jikin girma duka duka banfi shekaru goma ba lokacin amman inka duben seka ce nakai sha biyar.