← Book details Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 42

Sashe 26

Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

"Baba inada buƙatar makaranta nima dan Allah baba ka tausayamin ka mayar dani makaranta wannan kaɗai ze saka naji sassaucin zafin dake zuciyata".
Nakai maganar ina mai fashe mai da kuka!
Dakatawa baba yayi da fitar nashi kana ya dawo gabana ya gurfana hannuna ya kamo yana mai lallashina.
"Haba Aishatu na! maye na kukan aini yanzu na zubda makaman yaƙina akanki,Bara ɗan uwanki yazo inaganin zan sama miki gurbin karatu kima daina zubda hawayenki akan wannan".
Babana ya faÉ—a min hakan cikin tattausan lafazi.
Anty ce ta, tari numfashin, baba tana mai cewa.
"Amman babansu da kawai ta fitar da mijinta tayi aure inaganin hakan zefi mata ƙima, domin yanzu haka daga gidan Haladu ƙanin umma take kuma naji umma na maganar bazzawari hajiya zata haɗata dashi ai sekaji ta bakinta kafin maganar karatun ta miƙe ko?".
Anty takai maganar tana mai kallon babammu wanda yay tsam da ransa alamun ya É—an shiga tunani ne na daban.
"To'to babu damuwa amman dai duk da haka ina son tacigaba da karatun nata yanzu ke Aisha yaya kukayi da hajiya hadizan?".
Baba ya jefamin tambayar yana kallona.
Hawayena na share domin ni tuni nama manta danaje gidan mai makarantarmu.
"Baba wai ɗan uwanta ne keson ƙarin aure matarsa ɗaya da yara takwas, amman ba gida guda ze haɗamu ba kowa da gidanshi, nan da sati ɗayama zezo mu gaisa".
Nakai maganar kaina a ƙasa.
Dafe haɓa anty tai tana mai sauraron abinda baba ze faɗi aikuwa baba se cewa yayi.
"To madallah Allah ya zartar da abinda yafi zame miki alkairi a wannan karon dama zamu baki domin ki fitar da mijin da kike so sabida haka duk wanda kika ɗauka kika kawo mana matukar muka bincika mukaga halinsa na garine zamu bakishi sabida nina fahimci a karon farko ma, Umar ba ƙinshi kikai ba tsabar zugace da hassadar waccan shaiɗaniyar ƙawar taki ya saka kikaita ƙulla masa tsiya salo-salo to yaya zamuyi da hukuncin Allah fatanmu Allah yay miki zaɓin alkairi amin".
Baba yafaÉ—a yana mai tashi tsaye ya kama hanyar fita anty tana mai masa adawo lafiya tare da amsa masa da amin.
Sosai anty ta zaunar dani tana min nasiha tare da bani manyan misalai akan yanayin rayuwa wanda nai matuƙar tsorata dasu tabbas nina shaida yarinya ce ni amman ƙaddarar auren wuri da haihuwa yasa na sami ƙarin girma ajikina da hankalina wanda ya zarta na shekaruna.
Bamu muka tashi daga rumfar anty ba seda akai kiran sallar magariba bakin rariya naje nayo alwala na shige É—akinmu na shinfiÉ—a abun sallah na som gabatar da sallar magariba ina idarwa nai bangaren umma kallo.
Anan muka shantake har Anty tagama tuwon dare ta zubo mana namu mukaci daga nan mukai sallar isha'i kowa ya kama gabansa domin ya kwanta ya hutawa ransa.
Dare mahutar bawa amman a gareni hakan ya gagara domin gaba ɗaya nakasa rintsawa idanuna ya fushe sam nakasa yin bacci se faman nanata maganganun sakina nake acikin ƙwaƙwalwata.
Wannan rayuwa wato gaba É—ayanta abar darasice ga bawa yakamata tun da sauran damarmu mu dinga gyara halai yarmu kafin mutuwa tazo ta riskemu wannan itace ranar nadama ga bawa.
Wai yanzu ace zalinci cin amana zamba cikin aminci handama da baba kere sune suka yawaita ga al'umarmu? makashin ka yana tare dakai kana tare da mutum amman shi zagon ƙasa yake maka shin mai Umar yake dashine da har sakina zataimin wannan ƙullalliyar akanshi?
Lumshe ƙananun idanuna nayi ina hasko yadda umar yake a zahiri.
Umar dogon namijine mai suffar ƙarfafan maza farine tas mai dogon hanci da manyan idanu yana da mugun haƙuri tare da kawaici da rashin magana,Amma akwai zuciya idan ranshi ya ɓaci, Lumshe idanuna na kumayi ina Mai juyawa na rungume filon dake gabana tuno tsadaddiyar soyayyarshi wadda kansa naji kamar mu kaɗaine ke rayuwa a duniyar in yana gwadamin ita, yasan salon narkar da zuciyar mace haka nan yasan laƙanin mantar dake a duniyar da kike koke wacece wajan taurin kai matukar umar ya soma rikitaki da salonsa tofa bazaki kaucewa biye masa ba.
Wani azababban fitsarine ya kamani acikin wannan dare gani Mai mugun tsoro tashin anisa na soma amman taimin shuru,ganin ya soma zubomin a pant É—ina yasa na mike da sauri tare da fita ina tsaki.
Duk tunaninshi dana yaranshi dana matarshi ya hanani sukuni har yasa na raba dare idanuna bude.
Addu'a nai kana na shiga bayi na kama ruwan na fito nai alwala na nufi hanyar ɗaki adai dai dokin kofar ɗakinmu naɗan doki bakin kofar da ƙafata wadda naɗanji zafi kaɗan amman sena maze na shige ɗaki bayan na kaɗe shinfiɗata na kwanta abina.
Yatsana ne babba na ƙafa ya cigaba da zafi kamar an watsa barkono addu'a nai a wajan na shafa a wannan karon naji dama sannan bacci ya kwasheni wanda ban farkaba seda akai asubahi koda na tashi still yatsan nawa ya ɗan kumfura haka nayo alwala nazo nai sallah bayan nai azkar na koma bacci wanda rabi azabar yatsan ce fall a jikina wadda harta zuban zazzaɓi mai zafi.
***********
Da wajan karfe bakwai ta isa tasha wanda kusan bakwai da rabi motarsu ta tashi zuwa garin na abuja,Tunda tahau motar ta kifa kanta a saman jakarta tana tunanin matakin dazata dauka akan humaira haka har suka isa garin abuja bata wani yanke tartibin abinda zata mata É—in ba.
Taxi ta tara ta shigar da kayanta sannan ta masa kwatancen inda zataje tafiyar mintuna kaɗan ta kaita unguwar tasu kuɗinshi ta bashi sannan ta saukar da kayanta tare da nufar cikin gidan ta kama kofar gate ta bude da ƙyar ta shigar da jakarta cikin falon tana uban nishin azabar gajiya data zafin ciwon kan marin jiya dayaki sakinta har yau.
Gumi ta yarfe na wahala tana mai kallonshi a fakaice kafin ta karasa saman kujerar dayake zaune da sassarfa ta isa gareshi..........

#AUTAR MANYA
*GABA ÆŠAYA SADAUKAR WANE GA*

*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹

                          *35 & 36*
Chapter 26 · 0% Book details