← Book details Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 42

Sashe 3

Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Daka tawa yayi da tura gate ɗin dayake ƙoƙarin yi tare da aje aslam a ƙasa sannan ya janyo islam ya turon ita gabana.
Ya kalleni yana sakin murmushin sa na rainin hankali kamar koda yaushe idan nai masa maganar yarana.
Kafin ya mayar da kallonshi gurin islam.
"My love je mama tana son ganinki"
yafaÉ—awa yarinyar haka dayake ire iren sunayen dayake gayawa yaran nasa kenan.
Wani irin daÉ—ine ya kamani jikina har rawa yake a lokacin danaji furucin nasa gareta.
Amman kafin na ɗago idanuna na dire akanta naji sautin kukan ta! tare dana gudunta tai wurin mahaifinta ta riƙeshi katamau tana kuka!.
Cikin gwarancin su na yara naji tana cewa.
"Daddy! ban canci ba daddy kaini wurin inno".
Ta ƙare faɗin haka tana wani irin kuka wanda nima ya bawa nawa kukan damar fitowa fili.
Cikin rawar jiki na karasa gabanshi ƙwarjinin shi da kamshin turaren shi suka kuma kara gudun zuciyata hannuna na ɗora a bayanta ina kuka ina magana.
"Haba islam nifa na haifeki dan Allah kijuyo na kalleki islam É—ina"
Nafaɗa ina kokarin ƙwaceta daga hannunshi still ita kuma tana kuma ƙamƙame uban nata tana shigewa jikinshi.
Cikin sauri naga ya bude gate É—in gidan inna ya tura su ciki kana ya rufo sannan ya juyo yana kallona fuskarshi babu sukuni.
"Yanzu maye amfanin sakamin yarinyata kuka da kikai ke hakan kina ganin kin kyauta min kenan?"
YafaÉ—a a zuciye har wani mayar da numfashi yake.
Ganin kamar ze doken ne yasa naja baya daga wurin shi.
"Amman dai kaima kasan ina da hakki akan yarana ko? tunda kai baka da imanin da zaka kawon su nito inada ƙafar dazan biyoka koda zaka zaneni naga wata ƙatuwa ma ka bawa su take riƙonsu amman ni uwarsu bazaka bani ba".
Nima nakai maganar a tsananin zuciye.
Murmushi ya saki kamar koda yaushe domin mawuya cin abune kaga Ɓacin ransa a fili yana da danne ɓacin rai sedai tsananin soyawa mutum aya a hannu idan ka shiga gonarshi.
Ɗago ƙwayar idanunshi yayi tare da zubamin dukkan idanun shi yana kallona dasu lokaci ɗaya naga alamun ɓacin rai tattare dashi.
Takowa yake sannu a hankali har zuwa gabana yay min tsaye akaina kamar dogari.
Ya fini tsayi nesa ba kusa ba hakan yasa naÉ—an ja baya kaÉ—an ina haÉ—e jikina wuri É—aya domin tsananin kusancina dashi yasa nakejin tsohon tsumin daya kwana biyu da lafamin na neman tasowa.
"Dan Allah ki kuma mai maita me kika faÉ—i? ke yanzu har kina da bakin faÉ—in abin da kika ce? ko kin manta abin da kikai a baya?"
Murmushi ya kuma yi.
"Gwara da kika gani da idanun ki wallahi Aisha! kona baki yaran nan bazasu barki kiyi bacci ba domin basu sanki ba, kina mahaifiyar tasu amman kika kasa basu hakki irin na uwa! ko kin manta yadda uwa keda hakki akan É—a haka shima É—an keda hakki akan uwa?"
Hanky ya fiddo daga aljihun jeans É—insa ya goge zufa sannan ya cigaba da cewa.
"Allah sarki babarsu in kinada ƙarfi kizo ki amshe su, kuma matar da kike cewa na bata su, ai ta fimin ke sau dubu ɗari tunda ita matata ce ta sunnah keko fa kokin manta kalamin ki gareni?"
YafaÉ—a yana kallona.
"Umar na tsaneka bana ƙaunar ka ka sakeni nagaji da zama dakai ka kwashe gayyar tsiyarka ka tafi dasu bana bukata"
Ya mai maita maganar yana jefamin fitinannan kallo.
"Laifi ne danna kwashe ƴaƴana! yaran da basu cika wata uku ba kika yaye su yaran da madara ce tai musu madadi da nonon uwa mai ƙara lafiya ajiki, basu da kowa seni kamar yadda nima bani da kowa sesu nine uwar su nine ubansu ninaci kashi da fitsarin su keki faɗi ɗaya daga cikin abinda kikai musu na jin ƙai a matsayinki na uwa.......haihuwa kaɗai kika sani shima cikin da kikai barazanar zubarwa bada ban Allah ya duba wahalar danai wajan samar dashi ba da tabbas yajima da faɗuwa a rariya sabida wata banzar son zuciyarki shasha kawai mai baƙar zuciyata data fuska har abada hakkina dana yarana baze barki ki kwanta lafiya ba".
Ya ƙarasa maganar cikin ɓacin rai.
"Wallahi Aisha bada ban karamcin mahaifanki ba da har abada bazaki kuma ganin yaran nan ba wallahi! da sena nesan taki dasu nisa na har abada, sedai kash niɗin cikakken ɗan halak ne wanda baya mayar da alkairi zuwa sharri tabbas mahaifan ki sunmin halaccin daya zama dole nima na kamanta, amman fa ki sani Aisha na tsaneki tsana mafi muni har abada bazan taɓa sonki ba kuma kada ki saka ran zan kuma sauraranki kamar iwar haka sabida ayyukan dake gabana sun fimin ke mahimman ci acikin rayuwata"
Yafaɗa yana mai fir fitomin da manyan idanun shi waje kana yaja ƙafafunshi da ƙarfi yabar ni a wurin ban kumajin duriyar shiba se karar turo gate ɗinshi kurum.
"Innalillahi wa'innah ilaihirraju'
Kalmar danake ta faman mai maitawa kena da ƙarfi kuma a bayyane.
Ƙarfin ambaton kalmar ne ya bani damar jan ƙafafuna da sukai min nauyi nabar kofar gidan kamar mahaukaciya haka na faɗa cikin gidanmu da kallo Anty ta bini tana min magana amman ban kulata ba har seda na dangana da ɗakinmu na kife kaina a gefen gado ina risgar kuka kamar wadda aka cemin yau baba ko anty wani ya rasu.
Cikin haka naji alamun shigowarta zama tai a gefena tana mai kallona.
"Wato ke humairah haka rayuwarki zata ƙare a kuka? kullum na fuskanci in Umar yazo sekin shiga wannan hali, toki bude kunnen ki da kyau kijini inma banzan tunani kike akan umar to kidaina sabida ayanzu ya miki nisa yakamata ki kauda hankalin ki gareshi ki fuskanci abinda yake gabanki"
Anty mahaifiyata ta faÉ—i hakan fuskarta babu sukuni.
Wani ƙululun abu ne yazo ya tokaran kirjina hannuna na saka na dafe wurin ina mai kallonta.
"Anty ni a yanzu nafi bukatar ya bani Æ´aÆ´ana ba wai soyayyar shiba tayaya anty kina kallo gani amman yaje yay aure ya bata su"
NafaÉ—a ina sakin marayan kuka!
Sakin baki anty tai tana kallona gaba É—aya tagama cika da mamaki.
"A,a to shi dutse ne daze zauna haka? tunda keda kika haifa kin nuna bakya so se Allah ya kawo mai sonsu, maganar gaskiya inma kishin umar kedamun ki kima daina sabida ayanzu yay miki nisan da bazaki taɓa samun shiba"
Kuka na saka a wannan karon mai karfi wanda yasa anty tai saurin fita tabarmin É—akin.
"Na shiga uku! ni humaira mai ke shirin faruwa dani? kodai na faÉ—a soyayyar tsohon mijina ne wanda nasan yaymin nisan da har abada bazan kamo shiba"
Koma wa nai saman gadon daɓar na kwanta ina risgar kuka!
Tsananin tunanin abinda ya shuÉ—e a baya ya fara dawomin daki-daki kamar haka.

*ASALIN LABARIN PAGE 4 INSHA ALLAH*
*ZUMA A BAKI...!*🌹
{ Painful love Story }

NA
*AUTAR MANYA*

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._

*004*

Asalin labarin.
Chapter 3 · 0% Book details