Sashe 21
Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Koda ya sauka a garin na abuja bai da sani akan yana yin garin dan haka seda yasha wahala kafin ya sami dai dai tuwar komi, gidan da aka bashi a matsayin ya zauna a ƙarƙashin kulawar ma'aikatarsu ya nufa wanda ya kasance flate, mai ɗakuna guda uku se kicin da bayi tare da babban falo komi yana tsare tamkar da ɗan adam aciki kasancewar gidajan daman anyi sune domin ma'aikata gyara komi yay kamar mace sannan ya ɗora ruwa yaywa su islam wanka jikin aslam da zafin zazzaɓi ga kuka dayake mai haka ya haɗa mai madara a pida ya basa sabida sabon dayay da madarar yasa ba musu ya amsa yasha. Indomie ya dafa musu shida islam sukaci seda yay sallah ya nitsu sannan ya kunna wayarshi saƙonni ne burjik ciki duka sharesu yay tare da kiran inna sosai ta rufeshi da faɗa akan dole seya dawo da humaira ɗakinta sabida butulci dan yasami aiki ze sakaeta sannan ya ɗebe mata yara dan zalunci harda mai shan mama, ta inda ta shiga ba tanan take fita ba harta gama bai ce mata komi ba haka ya bata hakuri ya katse wayar batare daya amsa ze dawo da itan ba sannan kuma bai gayawa innar ai nihin abinda ya rabasu ba domin yana ganin taci darajar ƴaƴanta baya son wani abu marar daɗi ya gifta a tsakaninsu wanda ze ɓata sunanta yasa danginsa suna ganin baƙinta kodan darajar abinda ta haifa. Tundaga lokacin ya daina doguwar magana da inna a waya sedai ya kirata su gaisa data ɗauko mai maganar humaira ze katse. Daga ɓangaren aikinsa kuwa ya mayar da hankali sosai yake fita aikin wanda baya dawowa se wajan shidan yamma. Abinda ze baka tausayi shine yadda Umar ya koma kamar macen gida shizewa yaran wanka ya wanke musu kashi ya saka musu kaya ya basu abinci seya tabbatar dasunci sun ƙoshi yake fita aiki, ya kullosu agida da karfe biyu ze ɗauki excuse yazo ya ga lafiyarsu ya kuma basu abinci sannan ya koma rayuwa yake marar daɗi bayada farin cikin daya wuce na ƴaƴansa domin yana ganin sune sanyin idanunsa yana da mahaifiya amman baya sha,awar bawa inna su sabida gudun kada humaira tazo ta ɗaukar maisu wannan dalilin yasa ya bawa yaran nasa dukkan wata kulawarsa da lokacinsa wanda yaran suka buɗi idanu dashi suka mayar shi uwa uba agaresu abinda ze baka mamaki yadda basa kuka inya fita daya dawo zasu tawo suna ɓangale mai dadashi suna dariya. Haka yacigaba da kula da yaran nasa tsayin watanni ya saba da wannan rayuwa ga kuɗi sun fara zauna mai sedai yana kokarin turawa da imran wanda ze bawa su inna da baba domin hidimar gida shikam koda wasa baya tunanin komawa kano a yanzu duk da yasan yanzu ma tai idda babu maganar kome amman kanon ta fitar mai arai duk yadda inna take masa faɗa akan yazo yaƙi tun tana mai faɗa harta zo tana mashi nasiha amman yana ce mata akwai ayyuka agabansa nawani case ne shiyasa baze zo nan kusaba. Lokacin daya cika watanni shida agarin na abuja,Inka dubi Umar da yaransa bazaka ce su bane sabida kwanciyar hankalin data bayyana a jikinsu sunyi kyau kamar larabawa sun murje haka nan yaran sunyi ƙiba sosai sun kara haske kamar su dashi sun kuma bayyana, shi kuwa ya kara cika ya ƙara xama babban mutum ya kara haske ga wani uban ƙasumba mai lafiya databi fuskarsa ta kwanta luf sabida sauyin yanayi da suttura da cima tare da kwanciyar hankali. Sedai a yanzu ya koyi wani hali na rashin magana ya koyi zafin rai haka nan ya koyi wani irin miskilanci baka ganin dariyarsa inba gaban yaransa ba haka nan baka ganin maganarsa se yanawa islam wasa wadda yanzu tai wayo ta kara girma kamar ba ƴar shekaru biyu da watanni ba. Koda wasa basu san sunada uwa ba haka nan basa da magana seta daddy ko inno dayake bata waya suna gaisawa. Ranar daya fita wani case ya jima bai shigoba lokacin daya dawo gida ya tarar islam tana kuka aslam ma haka sabida sun daɗe basuga ya shigoba haka ya haɗesu yana mai zubda hawaye ya rungumesu yana basu hakuri a washe gari ya samo musu wata dattijuwa wadda ke zuwa da safe ta tafi da yamma haka rayuwar ta kasance ga Umar sam maganar mace bata gabansa bare yay tunanin aure nan kusa sabida gashin da humaira tai mai tabbas ta lasa mai ZUMA A BAKI na yaudara da halin wasu matan. Ataƙaice Umar yau gashi ya share watanni harya tafi shekara guda a garin abuja inda cikin lokacin ya samawa su islam makaranta wadda inya kaisu 7:00am baze ɗauko suba se 6:00pm hakan yafiye mai sauki domin mai haɗe da tahfiz ce dan haka seya sallami nannyn tasu. Yaran sun taso kamar tagwaye sabida sunyi saurin girman jiki irin na mahaifinsu haka nan bakinsu ya buɗe musamman islam shi aslam baida cikakkiyar lafiya sosai kamar yana da limonia ne ajikinsa shiyasa bini bini yake kaishi asibiti domin a duba mai lafiyarsa. Haka rayuwar ta kasance mai cikin farin ciki da kuma bakin ciki,suna waya da nuratu wadda take matukar son yaran nasa kamar ta mayarsu cikinta sedai ko kaɗan kalmar so bata haɗasuba sedai tsantsar zumunci dayake wanzuwa a tsakaninsu. Yau tunda ya tashi daga office ya biya ta banki yay wani uzuri sannan ya nufi hanyar gida, titin daya biyo babu kosa se ɗai ɗaikun motoci, horn yake dannawa wata budurwa dake tsaye ƙyam a saman ƙwalta sedai kamar yanayi da dutse agarin ya taka burki ne ya bugeta nan da nan ta faɗi wanwar a titin kamar gawa, cikin kiɗima ya fita ya daukota ya sakata a gidan baya dayake yana kusa da gidansa yasa ya wuce da ita nan, cikin rawar jikin son tai makon rai, ya fito da ita zuwa falonshi ya dauko ruwa a frij ya zuba mata ajikinta mayar da ajiyar zuciya tai tare da mikewa da sauri tana rintse idanunta. Kafin ta dire akansa tana jan wawiyar ajiyar zuciya. Zuba mata dara daran idanun shi yay masu rikita marar gaskiya fuskarshi babu sukuni, rabin hankalinsa kuma nakan yaransa dake school. "Ina ke miki ciwo?" Lumshe idanu tai cikin muradin soyayyarsa tace. "Babu komi se zuciyata". Lumshe idanunsa yay ya kauda kansa ga yanayin kallonta gareshi tare da tashi ya zube hannayensa a bocket ɗinsa yabar mata falon. Sakina dira tai saman kujera tana mai cewa. "My first target is successefully Alhamdulillahi" Kana ta koma ta kwanta haka yazo ya wuceta ya nufi mota yaje ya zo da yaransa. Da gudu ta miƙe tayi kan islam ta ɗagata tana "my dear your well come back ga new mommyn ki kina sona?" abin mamaki washe baki islam tai tana dariya haka ta kwashi yaran tai ɗaki dasu wanka tai musu ta fito ta basu abinci. Tuni sukai sabo a wunin ranar domin yaran sunada son mutane. Koda dare yay ita tai musu dinner dayace tazo ta wuce tunda ta warke kuka tasamai akan ita yar kano ce aka satota nan bata san kowa ba sosai kalaminta suka fusgi ranshi yace ze kaita tasha washe gari nan ma kuka tasamai akan bazata kai kanta gida ba sanin yadda garin namu yake yasa yace mata ta zauna na two weeks a gidan nasa inyaso kafin nan sesu wuce tare. Godiya tai mai tare da kama yaran tai ɗaki dasu sedai ya ƙeƙashe ya hanata kwana dasu haka ya kwashe yaran ya nufi nasa ɗakin dasu ita kuma ya barta a extra room guda. Haka zaman sakina ya wanxu a gidan umar itake komi sedai baya cin abincinta amman yana jin dadin yadda take kula da ƴaƴansa wanda nan da nan yaji yana ganin kimarta kamewarta yasa yaji ya gamsu da tarbiyarta domin ko kaɗan bata rabarsa da sunan iskanci. Wannan kwanakin datai yasa su islam kece mata,Mommy daga sun dawo a school suke nufar wajanta ahaka sukai kwanakin suka gama ya loda musu siyayya sukai kano anan unguwar chiranchi gidansu yake, sallama yasa akai da mahaifiyarta domin mahaifinta ya rasu kuka babarta ta saka akan ita dai tundaga makaranta bataga sakina ba ashe saceta akai babu inda basu duba ba wannan yasa suketa addu'a har aka ganta godiya tai mai sukai sallama sedai me? Fafur su islam sunƙi tafiya su se antafi da mommy sakina na kuka yaran na kuka haka ya tusasu sukai gidan inna akan ze kawosu su gaisa. Sosai inna tai murna da zuwan ɗan nata kwanansa ɗaya da zuwa gidan yasa aka fashe shi aka ƙawata shi ya koma na zamani harda su fanti sabo, kayan abinci ya siyo aka raba gida biyu aka kai gidan baba sauran innah. Kwanansa uku yay katsina koda wasa bai tunkari gidansu humaira ba seda ya xaga dangi sosai sannan ya dawo gida. Lokacin inna ta kafa mai masifar seya kai musu yaran sun gani amman fafur yaki haka ya kaiwa sakina su daya tashi dawowa suka zo gidan inna tare inna bata san sakina kawar humaira bace haka nan shima maryam ma bata san sakina ba sosai inna ta yaba da hankalin sakina. Dan haka sukaita hirarsu data tashi tafiya ya rakata hanya shi ko kaɗan baya sonta sedai ƙaunar yaransa data nuna yasa yaji ta shiga ransa ( mai ɗa wawa ) yana ganin uwar data haifesu ma ta yar dasu amman ita ta nuna tana so abinda yafi baƙanta ransa yadda yaga humaira koda wasa batazo domin ganin yaranta ba wannan abin ya ɓata ransa ya ƙara jin muguwar tsanarta. Dan haka koda ya dawo inna tace mai to ya dace ya fidda mata ko a dangi ko anan sabida xaman waje ɗaya babu mata akwai illah. Hangen wadda zata kula mai da yara yake nuratu ƴar boko ce haka nan bayajin ma ze iya auranta sabida yaga batada lokacin kanta sena aiki da karatu yaushe ma tai lokacinsa bare na yaransa tunaninsa ya tsaya akan sakina wadda taci darajar ƴaƴansa. Shawara sukai da inna wanda babu bata lokaci manya suka shiga maganar bayan dogon binciken da akai babansu humaira da baffa ne suka kai kudin aure aka saka biki sati biyu sabida yace baya bukatar komi tare zasu wuce inze koma. Zokuga