← Book details Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 42

Sashe 32

Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da ɗumbin takaicin baƙaƙen kalamansa gareni na koma gida idanuna jajir naci kuka nagodewa Allah domin ya umar yau ya cuceni kuma ya gama dani.
Da anty naci karo tana É—iban ruwa a rijiya da kallo ta bini tana nazarina nikuwa sallama kawai nai na faÉ—a É—aki tare da zama a saman gado ina cigaba da kukana ga wayar innah a hannuna.
Seda nai kusan mintuna biyar a zaune sannan anty ta shigo É—akin namu.
"Humaira"!
Naji muryarta acikin dodon kunnena.
"Na'am Anti".
NafaÉ—a cikin kukan takaicin danake yi.
"Ina kika tsaya tun la'asar daga asibitin ina kika nufa yanaga kina kuka sannan banga jakarki ba?".
Gabana ne yafaɗi sabida narasa amsar dazan bata,haka na cigaba da kukana yin duniya anty tai dani naƙi magana daga karshema masifa takamamin data gaji sannan ta ɗora da cewar bari baba ya dawo.
Tana fita na mike tsaye naje nayo alwala na dawo É—akinmu sallah nai ina idarwa na kira anisa akan ta mikawa innah wayarta.
Ana sallar isha'i na haye saman gado na kwanta sabida ban shirya amsa tambayar baba gareni ba.
Seda na kwanta sannan ƙafata tace bata san zancen ba haka tasakani agaba da zafi ina kuka ina jamai Allah ya isa da kyar bacci yay awon gaba dani.
Koda asubahi ma dakyar nai sallar asubahi ina idarwa na koma gado sanin ranar week end ne yasa nasha malamin baccina raina fess.
Wajan karfe goman safiya na tashi raina a ɓace haka zalika idanuna sunyi ja tare da kumburi, yunƙurawa nai tare da fita tsakar gida seda na ɗora ruwan wanka sannan naje ɗakin anty muka gaisa.
Daga nan nai ɗakin umma cikin ɓangarenta, alokacin ne umma ta tareni da farin cikinta akan cewar wannan bawan Allahn yacewa shugabar makaranta dan Allah yau ze xo wajena sabida nan da next week zebar kasar.
Tsananin jin kunyar umma yasa na amince mata atake kuwa ta kira mai makaranta a waya wato matar kaninta ta sanar mata da, amincewata sannan mukai sallama na fito waje.
Gaban murhun dana É—owa ruwan É—umin naje domin na duba koyay zafi
Koda na duba ruwan yayi ɗumi saukewa nai na zuba a bokitin wanka na faɗa banɗaki se lokacin na lura ashe al'adata ce take zuwa a yau ɗin sabida yadda naji ɓacin rai mai tsanani atun tashina a baccin yau.
Sosai na gyara jikina sannan nai wanka na fito abina, kicin naje na haÉ—a ruwan shayi marar suga haka zalika ban saka madara ba, na nufi É—akin anty ina kurba sabida yadda yake warwaremin hanjina.
"Humaira zauna nan daman jiranki nake bawai rabuwa nai dake ba".
Zama nai kaina aƙasa ina mai kurɓar shayin dake hannuna.
"Humaira jiya ina kika tsaya sannan kuma ina jakarki?".
Ƙasa nai da kaina bazan taɓa gaya mata abin kunyar danai ba.
"Anti suna gidan inna".
na faÉ—a kaina tsaye.
Da mamaki saman fuskarta naji tace min.
"Mai ya kaiki gidan innah bayan nasan tunda kika rabu da umar baki sake kai mata ziyara ba?".
Gumi naji ya soma ketomin abinka da rashin sabo da karya, da ƙyar na ƙaƙalo wata akaro na biyu nace mata.
"Inna yadda yatsana kemin zafi wallahi na É—auka mutuwa zanyi shiyasa dana dawo daga wajan likitan danaga can yafimin kusa na sauka wallahi nama jima agidan don harta kiramin su islam muka gaisa,To kukan da islam takeyi ne akaina yasa na manto jakar na tawo ina kuka"
NafaÉ—a ina mai neman gafarar ubangijina abisa karyar danai a yanzun.
Murmushi anty tai sannan ta dubeni.
"Babu wani nan kedai kawai kice kin biya tacan domin kiji muryar yaranki, wato humaira wannan tunanin yaran ne yake hanaki cin abinci kwana biyu? mai yasa bazaki fawwalawa ALLAH komai ba?".
Ajiyar zuciya na mayar tajin daɗi sabida ada danaji tace ba waninan wallahi na ɗauka ƙaryatani zatai amman danaji tai wannan furucin senaji matukar dadi araina.
"Anty nifa ba dansu naje ba, wallahi anty da gaske nake".
Nafaɗa cikin shagwaɓa
Dariya anti tai tana tsokana akan naki daurewa da rashin Æ´aÆ´ana musamman a yanzu dana san kawata ke auren babansu.
Azuciyata nake cewa lallai anti bazaki gane yadda kishi yake ba tunda baba bai taɓa miki kishiya ba amman wallahi abin nan ya taɓani duk da bama tare daya umar amman bani ba masoyina ma nasan seya jimin takaicin wannan cin amana.
Amman a fili murmushi nai mata kana na soma rattaba mata bayanin zuwan wannan bawan Allah'n.
"To Allah ya zaɓa miki mafi alkairi amman inata addu'a akan Allah ya bayyana gaskiya ki koma ɗakinki sabida ina tausayin ki ashekarunki ace kinyi aure biyu kin soma raba ƴaƴa".
Ƙwallah ce ta tarar min a kurmin idanuna batare dana bari ta ganiba na goge na ƙaƙalo murmushin yake ina mai amsa mata da "amin".
Tashi nai na nufi É—akinmu.
To wunin ranar nayisa ne cikin kasala da faÉ—uwar gaba, kuka kam nayisa kamar babu gobe sabida jikina yana bani kila in wannan mutumin yazo tofa aurena yazo sabida xan amince masane kawai ya auren domin na nisanta kaina da Umar.
Karfe biyar da rabin yamma yazo lokacin ina cin abincin rana, Umma ce ta aiko sadiya É—iyarta akan shugabar makaranta tai mata waya cewar yana waje.
Hijabi na É—auka dogo fari tass na É—ora akan doguwar rigar dake jikina naÉ—an fesa turare kaÉ—an sannan na fita seda naje wajan anty na gaya mata sannan na fita kofar gida gabana na faÉ—uwa.
Babban mutum mai kimanin shekaru arba'in da biyar nagani tsaye ajikin wata farar honda a kofar gidanmu.
Cikin nutsuwa na karasa gabansa sabida ya haifeni ba yaro bane har kasa na tsugunna na gaisar dashi.
Cikin farin ciki yacemin.
"Tashi tashi Æ´ammata barka da yamma my beby"
Gabana ne ya faɗi wata kunya ta kamani na mike naɗan raɓe daga gefenshi.
"Beby babu wajan zama ne?".
YafaÉ—a yana washen bakinsa dayaci goro domin gaya nan jajir.
Batare danai masa magana ba na wuce gida sallaya na É—auko mai na shinfiÉ—a masa a kofar gidanmu saman dakalinmu naje na gaya masa yazo muka zauna akai.
Bayan mun kuma gaisawa nan ya soma min bayanin kansa a taƙaice.
"Da farko sunana Alhaji sa'eed ni haiffffan garin kano ne kuma ni ɗan uwan hadiza ne, yarana takwas matata ɗaya dalilin ƙarin aurena shine matata bata kula dani".
Da sauri na É—ago sabida mamakin jin kalaminsa.
ÆŠagen gira yay.
"Yes bata san tattalin miji ba haka zalika kome na kawo mata bata godemin se rainuwa wannan dalilin yasa a yanzu na sauwake wa kaina da wahalarta komi nawa nake direshi a É—akina inci abinda raina keso,Haka zalika ga rashin kunya kala kala, hakan yasa nake kulleta a É—aki nai mata É—an banzan duka daga baya kuma ta bullomin da rashin bani hakkin kwanciyar aure shima sena daureta da igiya na haye kanta nai bidirina hankalina kwance wannan dalilin yasa nakeson na kara aure na huta".
Gumine naji yana ketomin kota ina.
Seda na yarfe sannan nace mai.
"Amman tayaya kuna zaman haka har ka kai war haka da ita batare daka mata illah ba?"
Murmushi yayi.
"Ada batamin kowani hali wallahi seda ta shiga wata makarantar matan aure tofa daga nan ta haɗu da ƙawaye na grp suka soma ɗorata a hanya, abinda ze baki mamaki yawancinsu matan manyan masu kudine wannan dalilin yasa suke gasa a junansu har hakan ta kawo tana min korafin ita kaza da kaxa yay mata kaɗan da sauransu atakaice dai yanzu komi nai mata bata gani sabida hangen na sama da ita,iya hakuri ina hakuri da ita bazan iya sakinta ba sabida darajar haihuwa amman aure zanyi domin na sami nutsuwa, kullum cikin tsurfar anko waya kaza da kaza ta fito na sai mata take".
Ajiyar zuciya nakai mai karfi kafin naji ya cigaba.
"Daga karshe ma inna kawo mata kayan abinci setaki yin girkin wai ita baxataci kalar abinci kaza ba se kaza ke danaga abin ze daman kawai sena kulle store É—ina, na soma dire mata Æ´ar awo inta ga dama tayi in bata ga dama ba ta barshi ai cikinta ne nikam ina zuwa da take away É—ina daga wje naci na koshi, sabida ita naga nasiha da bada baki baya mata se an haÉ—ata da masifa".
Wani tsoron Allah ne ya kamani daman haka mazan suke? ahaka nake fatan nai wani auren? dama haka ya umar yay hakuri dani? tabbas ba namijin daze dauki abinda naiwa ya umar koda kuwa waye, duk da zugar da sakina kemin amman nima nasan kaina ban kyautawa ya umar ba ashe haka yayta hakuri dani har haihuwa biyu, da auren sakina da jarabawar dana shiga bayan rabuwa ta da umar wallahi kaf isharace gareni haka zalika darasi ALLLAH ya nuna mini.
"Beby bakya jina?".
Naji muryarsa a kunnena.
Firgigit! na juyo na sauke ajiyar zuciya sannan nace mai.
"Amman nikam inda zaka É—auki shawarata auren dazaka daÉ—a wallahi baze kawo maka gyaraba face illah da haÉ—ari sabida daga lokacin daka fara kokarin kara aure to wallahi kawayen matarka zasu soma zugata akan tabi malamai daga nan sekaga wata barnar ta afku amman addu'a da nasiha sune zasu kawo muku gyara a tsakaninku haka nan abincin da kakeci kai É—aya a É—aki ka hanasu wallahi rashin adalci........".
Dannowar hancin wata shegiyar mota layinmune ya hanani ƙarasa maganar tawa.

*ZUMA A BAKI* _Is not for free book domin neman ƙarin bayani seki tuntubi wannan numbern 08142105218_

*Albishirin ku masu son karanta ƙayatattun labaran soyayya masu narkar da zuciya gami da ilimantarwa da faɗakarwa to gada ma ta samu ki nemi waɗannan zafafan littatan waɗanda aka baje soyayya mai tsayawa a zuƙatan makaranta cikinsu*👇🏼

*AUREN BARE*
*H A S K E*
*KOBA SO*
*DA IZZATA*
*ÆŠAN MAJALISSA*

_Nemi wannan numbern 08142105218 duk É—aya akan farashin naira 300 ne amman idan siya zaki gaba É—aya xaki biya naira 1000 É—aya ne_

*GABA ÆŠAYA SADAUKAR WANE GA*

*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹

                          *47 & 48*
Chapter 32 · 0% Book details