Sashe 23
Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹
*27 & 28*
Nisawa nai bayan na gama tunanin tarihin abinda ya shuÉ—e a shekara É—aya da rabin data gabata.
Share hawayena nai idanuna jajir na fito daga É—akinmu, bakin rijiya naje na É—auro alwala nazo na tayar da sallar magariba,bayan na idar na zauna nan ma tunanin bayan iddata na faÉ—a.
Wanda babu kalar ƙalubalan da ban ganiba, har wankau seda nai sabida baba yayi rantsuwa a lokacin akan baze ciyar dani ba tunda na kaso aurena haka nake xama nai wankau nai gogau na sami kuɗin abinci haka al'amura sukaita faruwa wanda har akai bikin nafisa mai bina tare da ya imran daya auri maryam duk ina cikin wannan ƙuncin rayuwa seda ayiya kakata tazo da kanta taiwa baba faɗa sannan ya janye ƙudirinsa lokacinne umma taiwa matar ƙaninta magana aka saman koyarwa nan wadda ake biyana dubu bakwai a duk wata.
Da kuɗin nake taimakon anty nake taimakon ƙannena,nima naɗan sai wani abun.
Haka al'amura suka cigaba da wanzuwa a tsakanina da mahaifana wanda seda aka kai ruwa rana kafin baba ya soma amsar gaisuwata.
Gaba É—aya ni yanzu wannan rayuwar ta fita akaina bani da bazzawari bare na sami mai É—eben kewa ga shi ban san gidansu sakina ba.
Na jefa wayata masai bare muyi waya da ita haka na nisa a tunanin lokacin danaji sallamar anisa a É—akin.
Amsa mata nayi tare dajan bakina na tsuke.
"Yaya humairah"
Ta kira sunana.
"Na'am Anisa".
Gyara zamanta tai a gabana tare da cewa.
"Ɗazufa naga yaya umar dasu aslam wallahi fafur sukaƙi yarda dani wai su akaisu wajan inno".
Ban ce mata komi ba naja jikina nai saman gado.
Babu yadda anty batai dani akan na fito nasha iska naci abinciba amman naƙi haka nai kwanan kuka
Washe gari kuwa kaina ya tashi da mugun ciwo,idanuna yay jajir sallar asubahi nai na koma baccina.
"Ke humairah yau bazaki aiki ba sekin makara"
Naji muryar anty akaina.
Ban motsaba nifa wallahi in akan Æ´aÆ´ana ne sena zubar da komai na makashi kotu domin bana jin a yanzu zan iya rayuwa babu su.
Fafur naki tashi bare na shirya nai makaranta haka naita juyi agado wajan karfe goman safiya naji kamshin turarensa tare da sallamarsa da sauri na mike na nufi gaban taga ina leƙen ƴaƴana.
Waige naga islam nayi tare da turjewa waje É—aya taki shiga É—akin anty.
"Daddy ina maman?"
Tafaɗa tana turo baki irin na shagwaɓaɓɓun yara.
Shafa tulun sumar dake kansa yay tun jiya islam ta hanashi sukuni ita yakaita wajan mamah mai kuka ta jiya har dukan ƴar yay akan nacin data kafa masa amman taƙi shuru ganin haka yasa ya tattarota sukayo nan( ɗada mahaifi se Allah).
"Tana ciki muje mana"
Yafaɗa murya ƙasa-ƙasa.
Amai makon ta shiga seta saka mai kuka wanda ya janyo hankalina nayo tsakar gidan,sabida daman ni ɗayace a ɓangaren namu su anty suna ɓangaren ummah.
Kaina babu ko É—an kwali haka na zube a gabanta na ware hannuna ina kuka.
Da gudu ta shige jikina tana sakin ajiyar Zuciya.
Shafa kanta nai da hannuna ina jin wani irin nutsuwa a tare dani.
Kafin na soma kici-kicin É—agata nai É—akinmu da ita.
"Wait dakata! ina zakimin da yarinya kinga ajeta zamu wucene"
A dake na tsaya da ita a hannuna.
"Bazan bada ba ainima ina da hakki akanta dan jaraba Æ´a nason wajan mamanta ka hanata zuwa"
NafaÉ—a cikin rashin kunya.
A gabana ya tsaya yana zuban kallon banza.
"Bani ita Aisha bana son hauka"
Yana kokarin kwatar ta.
Seta saka kuka.
"Ni wallahi daddy bazani wajan mommy ba ita bata kuka akammu dukanmu take mommyn abuja".
Cak naga ya tsaya ya zuba mata ido yana kallonta kafin naga ya juya yabar tsakar gidan.
Yana gab da fita na É—aga murya.
"Allah ya isana ga duk ƙatuwar data dokarmin ƴaƴana ubangiji yabimin hakkina"
Da gudu najata mukai É—akinmu ina dariyar farin ciki.
Shima anasa ɓarin maganar islam ta kaɗashi batun yau take cemai mommy na dukansu ba amman yadda take nan nan dasu agabansa yasa ya kasa yadda da maganar islam ɗin sabida ance ba,a kama maganar yaro gefe ɗaya ga takaicin rinjayen da humaira tai mai na amsar islam wadda yaji kamar ya gaurawa islam mari sabida yadda take ƙulafucin uwarta.
Haka ya koma gidan inna aslam daman bayajin dadi yana bacci dan haka shima fita yay zuwa gidansu sakina wadda ya kasa gane kanta sam yanzu in sukazo kano bata yadda ta sauka gidan inna kamar da sedai shiya bita can gidan nasu.
A gado na ajeta na fita waje shayi na haÉ—o mana mai kauri nazo na zuba mata muka baje muna sha muna gamawa na tsefe mata kanta da kaina na wanke mata sannan na shiga É—akin anty da ita se lokacin suka san an kawon ita nanfa anisa ta amsheta ta soma yarfa mata kitso mai kyau da yamma nai mata kunshi ja wanda ya haskata.
Sosai baba yay farin cikin ganin islam a gidan haka yayta sabga mata siyayya kala kala, a daren kuma har aka rufo kofar gida baizo É—aukarta ba dan haka na cire mata kayanta muka kwanta tare washe gari ranar juma'a nafita aiki tare da ita.
Lokacin naga tashin hankali domin karfe goman safiya da rabi segashi a bakin gate É—inmu koda naje cin mutunci yahau min akan me xan fito mai da yarinya.
Sunkuyar da kaina kasa nai ina mai wasa da yatsuna haka ya gama bala'insa yaja Æ´arsa suka tafi ajiyar zuciya na mayar domin yanzu naÉ—anji dama sabida yadda islam ta É—eban kewa a daran jiya.
Sedai maganar dukan da matar ubansu ke masu ita ta tsayan a raina na kasa mantawa.
Haka na yini a makarantar sannan na dawo gida bayan an tashi lokacin naji labarin sun wuce abuja.
Hmm ashe wucewa zasuyi can É—in shiyasa yazo a burkice.
Watsar da sabgarsu nai a ranar na shiga sabgata washe gari na tashi da shirin tafiya gidan shugabar makarantarmu kamar yadda ta umarcen.
Shikuwa daman da yaran kaɗai ya tafi domin zasu koma school ne ita kuwa sakina taƙi binsa sabida fushin datake dashi tun jiya akan yace mata islam na wajan mamanta.
Wannan dalilin ne yasa ta dauki fushin dayasa har shima yay fushi ya tafi yabarta haka nan koda ta kira wayarsa bai dauka ba domin ta ɓata mai rai sabida yadda tace mai ai daman tasan munafurcin mazane amman yanasan matarsa har yau wannan maganar yasa yaji haushinta sosai.
Hankalintane ya tashi a washe garin asabar tai gidan inna domin tasakata ta basa hakuri akan laifin datai mai har yay tafiyarsa ya barta.
Shikuwa daman da biyu yay hakan na farko maganar islam na tana dukansu na biyu kuma furucinta gareshi wanda ba daban yakai zuciyarsa nesaba dase yay mata illah a daren.
Ita kanta inna, tai mamakin yadda sakina batazo gaisheta ba,amman dan rashin kunya tazo mata da wannan maganar agabanta inna ta kirasa ta hau yimai faÉ—a akanme ze tafi yabar matarsa.
Hakuri ya bata sannan yace gobe ta bata kudin mota ta tawo haka inna ta kirga kudi ta bata sukai sallama ba kunya ta kama hanyar fita.
Magana mukai akan sabon bazzawarin da shugabar makarantar mu ta sama min na taho inata tunani mai Æ´aÆ´a takwas da mata É—aya amman yana da kuÉ—i hawayene yake zubomin lallai rayuwa yau ni ake jonawa da wani duk irin soyayyar da umari ya nuna mini.
Cak na tsaya lokacin dana zo giftawa ta gidan inna ganin sakina tana fitowa daga gidan.........!
*GABA ÆŠAYA SADAUKAR WANE GA*

*29 & 30*